Tasirin Jinsi akan ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli

Daidaiton jinsiMuhali da dumama yanayi

Backgrounder

Matan karkara da suka shiga cikin ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli a Afrika na iya samar da fa’idoji kala-kala, da ka matakin mutum daya har zuwa katafarin al-umma. Hanyoyin magance matsaloli kamar yadda Ƙungiyar Kasa da Kasa ta Kare Halittu (IUCN) ta bayyana, na nufin jerin matakan da ake ɗauka wurin kare muhalli, da kuma kula da tabbatar da dorewar sa, har da ma farfaɗo da shi da ka cikin wani kangi. Waɗannan matakai an tsara su ne don adaidaita sahun al’umma cikin hanya mai tasiri da sauyin hali, tare da tabbatar da cewa ya amfanin ɗan adam da kuma halittu daban-daban.

Fahimtar ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli (za mu na kiran shi Nbs a cikin maudu’in nan)

Hanyoyin samun waraka daka al’amura na yau da kullum, na bawa mutane da al’umma damar shawo kan duk wani kalubale wanda ya hada da matsalar sauyin yanayi da yadda za’a dakile shi*, rashin ruwa da abinci, rage afkuwar annoba, da kuma bunƙasa zamantakewa da tattalin arziƙi. NbS suna amfani da tsarin halitta da yanayin muhalli don magance waɗannan ƙalubalen yadda ya kamata, tare da samar da fa’idoji ga muhalli da ɗan adam. Misalai sun hada da maido da dausayi don tace gurbacewar ruwa, dasa itatuwa don rage zai-zaiyar kasa da rage hayaki mai gurbata muhalli, da samar da korayen wurare na birane don inganta iska da samar da wuraren shakatawa.

Samun karbuwar NbS ya ta’allaka ne a cikin ayyukansu da yawa* — ba wai kawai suna magance ƙalubalen al’umma ba har ma suna ba da gudummawa ga kiyaye bambance-bambancen halittu da haɓaka sabis na muhalli,* ta hanyar fahimtar haɗin gwiwar tsarin ɗan adam da na halitta. 

Me ake nufi da karbuwar jinsi ga NbS?  

Tasirin jinsi ga ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli (NbS) ba wai kawai yana fifita dorewar muhalli da jin daɗin al’umma ba, har ma da cin nasarar daidaiton jinsi. Sun yarda sun kuma dau kudirin magance bukatu daban-daban, tare da ƙalubalai, burika, da ra’ayoyin daidaikun mutane a cikin kowane jinsi. Ta hanyar ƙarfafa gwiwa wurin hada kai da bayar da wakilci na muryoyin mata, maza da matasa marasa galihu, NbS yana tabatar da cewa an samu mafita da za ta samar da daidaito da kuma adalci, ta hanyar amfani da mutane masu hikima da ƙwarewa a rayuwa ta fanni daban-daban.

Matan karkara galibi suna taka muhimmiyar rawa wajen sarrafa albarkatun ƙasa kuma suna da mahimmanci musamman wajen dorewar cigaban rayuwa da haɓaka juriya acikin alumma, musamman mutanen karkara a ko ina a duniya. Ilimin su na musaman, da kwarewar su na da muhimanci wurin samar da ingantacen tasirin jinsi ga NBS.

A takaice, tasirin jinsi ga ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli, kudiri ne na tabatar da cewa duka alumma, musamman mata da rukunin mutane masu jinsi daban, sun ba da gudunmuwar su wurin kirkira, gudanarwa, da kuma tantance wadanan ayyuka. Wanan hanyar na bukatar samar da wurare inda mutane masu jinsi daban-daban zasu samu damar fadin albarkacin bakin su, a saurare su a kuma girmamasu, inda a karshe za’a samu mafita daka wadanan tattaunawa a cikin alumma masu matuakar gogewa.

Me yasa wanan maudu’in ke da muhimanci ga masu sauraro?

  • Saukin kamuwa da ilolin sauyin yanayi* da juriya akan sauyin yanayi: Kasashen Afirka da yawa na kan gaba wurin fuskantar sauyin yanayi, suna fama da fari, ambaliyar ruwa, da kuma cenji faduwa ruwan sama. Tasirin jinsi ga Nbs na ba da hanyoyi mafi inganci wurin sabawa da wadanan cenje-cenjen, a lokaci guda kuma ya na tabbatar da cewa wadanan dabarun da aka dauka masu kyau ne kuma zasu magance bukatun alumma, da duka jinsi gaba ki daya. 
  • Harkar noma da rayuwar yau da kullum: A yankin nahiyar sahara Afrika, kaso mafi yawa na alumma ta sun dogara da noma da albarkatun kasa wurin rayuwar yau da kullum. Mata, musaman, na taka muhimiyar rawa a wadanan bangarorin, amma sau da yawa ana barin su a baya wurin samun albarkatun kasa, muhiman labarai, da kuma wurin daukar hukunci. Tattauna tasirin jinsi ga Nbs a kafafen rediyo zai taimaka wurin haskaka muhimancin shigo da mata wurin tattaunawa da yanke hukunci akan alamura masu daurewa da ya shafi rayuwar su, wanda zai samar da ingantatun unguwanni da kuma habaka rayuwawar yau da kullum din alumma.  
  • Ba da tallafi da daidaito: Daidaiton jinsi abu ne mai tasiri a wurin mutanen yankin sahara Afirka. Tasirin jinsi Nbs ba wai kawai kalubalen muhalli yake kokarin gyarawa ba, ya na samar da hanyoyi na tallafawa mata da kuma habaka daidaiton jinsi ta jadada muhimancin rawar da mata suke takawa da ilimin da suke dashi wurin kula da muhalli da juriya kan cenje-cenje sauyin yanayi.
  • Ilimi da wayar da kai: Rediyo hanya ce mai karfi ta ilimantar wa da wayar da kan mutanen da suke karkara da kauyuka, inda samun sauran kafafen yada labarai ke da wuya. Tattauna tasisirn jinsi na Nbs na sanar da masu sauraro da ilimantar da su kan sababin hanyoyi samun saukin magance kalubalen muhalli da suke tabbatar da adalci, tasiri ga jinsi da kuma karbuwa a gurin kowa.
  • Samun hadin kan alumma unguwanni: Neman hadin kan alumma domin tattaunawa akan tasirin jinsi na Nbs na sawa mutane su ji cewa su na da ta cewa a yarda za’a kula da tafiyar da sababin hanyoyin kula da muhalli. Ya na karfafa gwiwar mutane da suke zaune a unguwanni, wanda suka hada da mata su ba da gudunmuwar su, da ra’ayoyin su, da kuma shawarwarin samun mafita.

Muhiman bayanai game da hadinkai da tasirin Jinsi akan ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsalolin rayuwa

Ta hanyar tabbatar da mata sun shiga matakai daban-daban na shirin Nbs musamman a lokutan da ake matakin tsarawa da aiwatarwa —daka gano matsalolin zuwa tsarawa zuwa aiwatarwa—ayyukan za su zamo masu inganci da amincewar kowa. Wadanan sassa na gaba za suyi duba ne akan matakai daki-daki na aiki da za su kara wa shirin inganci ta hanyar saka mata a ciki da basu damar jagoranci. 

  1. Gano ainihin matsala

Samun hadin gwiwar mutane daka rukuni daban-daban, ciki har da mata da sauran kungiyoyi mara sa galihu, tun da ka farkon shirin don tabatar da anyi la’akari da ra’ayoyinsu, iliminsu, kwarewar su da kuma gogewar su. Saboda mata tun asali su na da tattali a cikin alumma, zasu iya ba da shawarwari masu amfani a alamuran da ba kowa ne ke iya gani ba da sauri, kamar ingancin ruwan sha ko kuma raguwar wasu tsirai da suke da amfani a wurin ciyar da iyali ko samar da magani.

  1. Tsarawa

Idan mata su ka shiga tsara ayyukan Nbs, ya na kara yiyuwar cewa sakamakon aikin zai magance da samar da mafita ga kalubale da yawa da suke adabar alumma, wanda su ka hada da zamantakewa, tattalin arziki, da harkar gyaran muhalli. Shigar mata na tabatatar da cewa sakamakon da za’a samu karbabe na ga kowa a cikin alumma. Misali, ayyukan da suka shafi aikin karfi kamar dasa bishiyu ko kuma gine-gine, mata su zama suna cikin tsare-tsaren aikin tun farko don a yi la’akari da karfi da kuma rauni na maza da mata su duka. Wanan ya hada da lura da ayyukan yau da kullum da suke, da gyare-gyaren gida, da sauran ayyuka da ya shafe su, da kuma tabatar da akwai kayan aiki da hanyoyi da za su dace da kowa.

  1. Aiwatarwa

Kamar yada ayyukan Nbs suke matsawa da ka matakin kirkira zuwa matakin aiwatarwa, tabatar da daidaiton jinsi a bangaren jagoranci da suaran mukamai na taimakawa wurin samar da adalci a sakamakon da za’a samu, wanda ya hada da aikin yi, tattalin arziki, faidojin muhalli da banbancin halittu, da tallafi. Tabatar da wanan matsaya zai samar da sauya yadda ake daukan mata a gargajiyance, ta basu horo a bangarorin da maza suka mamaye, kamar aikin fasaha na daji da kuma injiniyoyi a wurin ayyukan gyaran ruwa da dam-dam. 

  1. Saido da kula

Idan ayyukan Nbs za su zama masu tasiri akan jinsi, dole mata su taka muhimiyar rawa wurin saido da kula da aikin. Wanan ba kawai bin didigin cigaban shirin akan manufofin muhali da aka sa ba, har da tabatar da cewa shirin ya cigaba da cimma manufofin zamantakewa tsakanin alumma da aka saka. Mata za su na kawo ra’ayoyin alumma ba akan muhalli kawai ba, har kan yadda ayyukan ke tasiri a rayuwar yau da kullum ta alumma, su bayar da shawarar gyare-gyare, da kuma taimakawa wajen auna sakamakon da ya shafi daidaiton jinsi da tallafawa mara sa karfi.

  1. Auna nasara da faduwa

Fassara nasara ko gazawa ta mahangar tasirin jinsi ya hada da kallon abun fiye da ma’auni na gargajiya kamar irgga yawan bishiyoyi da aka dasa ko girman gona da aka gyara. Hakanan ya hada da bin diddigin inganta matakan samun kudin shiga na mata, rage lokacin da ake kashewa kan ayyukan gida da kulawa da iyali ba a biya, da kara shigar mata cikin mukamai da suke da ikon yanke hukunci a gida da sauran matakan karamar hukuma. 

Kimanta nasara ko gazawa wata dama ce ta ayyana darussan da aka koya, da tattauna darusan da sauran mutanen unguwanni da makwabta. Yana da mahimmanci a sa mata akan duk wata dama da ta bullo, dan basu lokaci suyi nazarin yadda zasu shawo kanta.

  1. Jin ra’ayoyin mutane da daidaitawa

Ayyukan NbS da shirye-shirye su ya dace su sami tsari don tabbatar da cigaban samun ra’ayoyin jama’a da daidaitawa shirin, wanan zai basu damar daidaita shirin da kyau da kawar da duk wani kalubale da zai taso. Wannan matakai za su tabbatar da cewa waɗannan ayyuka sun dore, har ma su shiga cikin manufofin tsare-tsaren da aiwatrwa na karamar hukuma, yanki, da ƙasa baki daya. Cigaba da shigar da mata yana da mahimmanci a nan, saboda yana iya haifar da gyare-gyaren ayyuka da zasu dace da buƙatun duka alumma da muhallin su.

  1. Horarwa da karin ilimi

Tallafawa mata ta hanyar ilimi da horarwa wurin kula da muhalli, jagoranci, da ƙwarewar fasaha yana taimakawa wajen tabbatar da cewa an riƙe ilimi a cikin al’umma kuma an ba da shi ga yaya da jikoki masu zuwa. Wannan yana da mahimmanci don dorewar fa’idojin NbS har shekaru masu yawa da hade kan alumma su zama masu juriya.

A takaice, shigar da matan karkara cikin NbS ba wai yana inganta sakamakon aikin ba kawai, har ma daidaiton jinsi yake ingantawa, ya tabbatar da cewa hanyoyin magance muhalli suna haɓaka adalci a zamantakewa da jin daɗin al’umma. Wannan hanya tana da mahimmanci don tabbatar da cewa ci gaba mai dorewa ya amfanar da dukkan al’umma.

 

Aiwatar da ayyuka masu tasiri akan jinsi ta hanyoyi daban-daban

Aikin noma da shuka bishiyu: Lokacin aiwatar da ayyukan noma da shuka bishiyu, yana da mahimmanci a yi la’akari da yadda ake gudanar da ko wana aiki a matsayi daban-daban. Misali, mata na iya sa hannu da farko wajen girbin ‘ya’yan itatuwa da su gyada, yayin da su kuma maza za su mai da hankali wurin mai da manyan bishiyu zuwa katako. NbS mai tasiri ga jinsi na iya ba da horo da kayan aiki na musamman ga mata don su karo ilimi da ƙwarewa wurin girbi mai dorewa, da ko ya musu tallace-tallace, don tabbatar da cewa ayyukan da suke yi su ma mai fa’ida ne da dorewa kamar na maza.

Da wo da shuke-shuken bishiyu a daji: Ayyukan dasa bishiyu a daji ta hanyar NbS zai tabbatar da cewa nau’in bishiyun da aka zaɓa dan dasawa sun yi daidai da bishiyun da mata da maza su ke so duka. Misali, mata za su iya fin son a shuka nau’ikan bishiyu masu ‘ya’yan itatuwa, gyada, ko ganyen magani waɗanda galibi suke amfani da su, yayin da maza za su fifita nau’ikan bishiyun da za su iya yin katako da su. Jin ra’ayin maza da mata a lokacin da ake tsarawa da daukar hukuncin abun da za’a shuka ba wai zai tabbatar da samar da ire-iren bishiyu kala-kala (haɓaka bambancin halittu) ba ne kawai, har ma taimakawa wurin kara haɓaka tattalin arziki da gyara wurin zama dan jin dadin kowa da kowa.

Dawo da daji na bishiyun kan ruwa: Ayyukan NbS mai tasiri akan jinsi don maido da bishiyun kan ruwa zai haɗa da tuntuɓar maza da mata daga al’ummomin yankin yayin da ake matakin tasara manufofin shirin. Mata, waɗanda a al’adance za su iya tattara kifi a jikin bishiyun gefen ruwa, da maza, waɗanda a al’adance za su iya kamun kifi a cikin kogin da ke kusa, za su sami fahimta daban-daban game da lafiyar muhallin da kuma yadda maido da shi zai inganta rayuwarsu. Tsarin NbS da ke da alaƙa da jinsi zai tabbatar da cewa ra’ayoyin mata da na maza sun shiga cikin tsara manufofin shirin, wanda zai haifar da sakamako masu fa’ida da daidaito ga al’umma baki ɗaya. Mata da maza kuma za su iya shiga ayyukan sa ido da tantancewa, bisa la’akari da ayyukansu daban-daban a cikin kokarin da wo da bishiyun daji.

Tsare-tsaren gudanar da ruwa don amfani: A yawancin yankunan karkara, mata ne ke da alhakin debo ruwa da sarafa yadda za’ai amfani dashi. NbS mai tasiri akan jinsi wanda aka mayar da hankali kan dawowa da gyara magudanan ruwa ko dausayi za’a sa mata a ciki tun da ka lokacin tsarawa don tabbatar da cewa an samu hanyar shiga da a debo ruwa, sanan inganicn ruwa ya dace da bukatun gida. Haka zalika, za a ilimantar da maza da mata game da amfani da ruwa ta hanya mai ɗorewa tare da shigar da su cikin harkokin gudanar da ruwa, tare da taimakawa wajen inganta juriyar al’umma gaba ɗaya ga matsalolin da suka shafi ruwa.

 

Misalan Ayyuka masu tasiri akan jinsi 

Da wo da shuke-shuken bishiyu a daji a kasar Nepal

Matsalar da aka magance: Hana sare bishiyu da rashin shigar mata wajen yanke hukunci.

Hanyar da aka bi aka samu mafita: A kasar Nepal, wani aikin dawo da martabar dajika na hadin gwiwa da alummar yankin guda sukai, wanda Ƙungiyar kare halittu ta Duniya ta dauki nauyi, ta tabbata an bawa mata damar yanke hukunci a matakai daban-daban. Wannan ya hada da ba su horo kan kula da lambu da dabarun dasa bishiyu kala-kala.

Sakamako: Wannan yunƙurin ba wai kawai ya inganta dawo da martabar daji ba, har ma ya tallafawa mata ta hanyar ba su ikon daukar hukunci akan alamura da ya shafe su da alumma, da kuma sarrafa duk wani kayan albarkatu da aka samu, wanda yayi silar magance matsalolin muhalli da daidaiton jinsi.

Domin ƙarin bayani game da mahimmancin shigar mata a cikin sake fasalin gandun daji, duba labarin daga Ƙungiyar Ƙasa ta Duniya don Kare Halitta (IUCN): 

https://www.iucn.org/news/forests/202108/hanyoyin-taimkawa-matankarkara-kare-daji 

Tsare-tsaren gudanar da ruwa a kasar Jordan 

Matsalar da aka magance: Rashin daidaito wurin raban ruwa da rashin shigar mata wurin gudanar da ruwa 

Hanyar da aka bi aka samu mafita: A cikin kasar Jordan, wani aiki da Majalisar Dinkin Duniya bangaren mata ta dauki nauyi, ya mai da hankali kan ayyukan samar da ruwa da zai dore. Wannan ya haɗa da kafa ƙungiyoyi masu amfani da ruwa inda aka ƙarfafa mata su shiga a matsayin mambobi da shuwagabanni.

Sakamako: Shigar da mata ya tabbatar da in aka zo raba ruwa zuwa gidaje an yi la’akari da bukatun mutanen gidan, ciki har da mata, ta haka aka tabatar da adalci da dorewa samar da ruwa. 

Domin karin bayani akan hanyoyin taimakawa matan karkara su kare dajika da gudunmuwar da suke bayarwa wurin tsare daji, a duba wanan link na UN bangaren mata: https://wrd.unwomen.org/sites/default/files/2021-11/UNMata-matankarkarajordan-Brief-WEB.pdf 

Mata jaruman bishiyu a kasar Uganda 

Matsakar da aka magance: Zaizayar kasa, sare bishiyu, da rashin daidaiton jinsi a harkar kula da kasa.

Hanyar da aka bi aka samu mafita: Aikin Kungiyar Tallafawa Mata domin samun Dorewar kula da Kasa (WESLAM) dake a garuruwa Bugiri da Mayuge da su ke yankin gabas a kasar Uganda sun lashi kudirin kawo karshen lalacewar kasa da sare bishiyu ta hanyar noma mai dorewa da shuka sababin bishiyu. Wanda kungiyar Swedish Postcode Lottery ta dauki nauyi, WESLAM ta magance raguwar dajika da yawa, wanda ya janyo lalacewar kasa da karin talauci a garuruwan, wanda talaucin ya fi shafar mata. 

Sakamako: Aikin ya tallafawa mata ta hanyar shigar da su ayyuka masu dorewa kamar kiwon zuma da noman musharum, wanda hanyoyi ne na samun kudin shiga da rage dogaro kan abubuwan da suke taimakawa wurin sare bishiyun daji. Ta hanyar tsarin kula da gandun daji na hadin gwiwa, manoma na gargajiya na samun damar yin amfani da gandun daji, wanda zai inganta rayuwarsu ta yau da kullum da wuraren zaman su. 

Domin karin bayani akan ayyukan WESLAM da fa’idojin su, a ziyarci shafin yanar gizo na: https://viagroforestry.org/projects/weslam/ 

Kalubale 

Matan karkara na fuskantar ƙalubale da yawa wanda za su iya hana su yin aiki yadda ya kamata a lokacin nazari da aiwatar da aiyukan samun nasara wurin amfani da alamuran yau da kullum. Waɗannan kalubalen su kan samo asali ne daga halayar zamantakewa, al’adu, da rashin daidato wurin shigar mata a dama da su sa mu kuma riba. Magance waɗannan ƙalubalen yana da mahimmanci don tabbatar da cewa NbS na da tasiri ga jinsi kuma suna da fa’ida ga al’umma baki ɗaya. Ga wasu manyan matsalolin da matan karkara ke fuskanta:

  1. Karancin damar samun albarkatu: Galibi Maza sunfi matan karkara damar samun muhimman albarkatu kamar filaye, ruwa, kuɗi, da ilimin na fasaha. Wannan na iya tauye ikonsu na shiga da kuma cin gajiyar shirin NbS a fannoni kamar aikin noma ko noma mai dorewa, wanda galibi ke buƙatar mallakar filaye da ikon saka hannun jari a sabbin fasahohi.
  2. Aladu da halayen zamantakewa da aka gada: A cikin al’ummomi da yawa, matsayin jinsi na gargajiya yana hana mata shiga cikin tsarin yanke hukunci a cikin gidansu da cikin al’ummominsu, tare da ba da alhakin duk ayyukan gida ga mata. Waɗannan ayyukan gida na hana mata shiga tarurrukan al’umma, ya hana su ba da gudummawa ga tsare-tsare, ko ɗaukar matsayin jagoranci a NbS.
  3. Rashin ilimi da horan aiki: Matan karkara galibin su damar da suke samu na su yi karatu ko koyan sana’oi ba ta da yawa. Wanan ya ke rage fahimtar su game da ayyukan Nbs, ya ke kuma rage kwarewar su wurin aiwatar da aikin yanda ya kamata
  4. Rashin Kudi: Mata su na dogaro da wasu domin samun kudin kashewa, don haka lokacin da suke samu suyi aikin Nbs kadan ne. Domin galibin mata su ne ke kula da yara da sauran aikace-aikacen gida, sau da yawa suna dogaro ga mazajensu domin samun kudin kashewa. Idan ba su samu yancin kan su na samun kudi da kansu ba, zai yi wahala su shiga cikin ayyukan da zasu dau dogon lokaci waɗanda ba za su samar da kudin kashewa ba nan take.
  5. Rashin samun wakilci da shiga a dama dasu: Ko da mata sun shiga cikin shirye-shiryen NbS, yawanci a na ajiye su a matakin aikace-aikace a maimakon a su a cikin masu tsarawa da shugabanci. Wannan rashin wakilcin su a cikin tsare-tsare, gudanarwa, da daukar mataki a cikin shirin yana nufin cewa bukatun mata da shawarwarin su ba sa shiga cikin ayyukan..
  6. Rashin samun shiga kasuwa: Matan da ke yankunan karkara da yawan su na fuskantar cikas wurin cin gajiyar kasuwanni. Wannan na iya faruwa ne saboda rashin abun hawa da sufuri, ko aladun gargajiya da ya ke hana mata fita ko kuma rashin kudi. Ba tare da samun kasuwa ba, yana da wahala mata su sayar da kayayyaki daga ayyukan NbS ko samun kayan da suka dace.
  7. Rashin samun abokan tafiya masu taimako: Sau da yawa mata kan rasa abokai da za su ba su taimako, horarwa, da nuna musu hanyoyi samun damamaki a ayyukan da su ka shafi muhalli. Wannan na dakile su wurin zama shugabanni da ƙirƙira ayyuka a cikin NbS.
  8. Rashin samun muhiman bayanai: Rashin raraba bayanai bisa jinsi ya sa da wahala a gane takamemen irin raunin da alumma ke fama da shi da kuma irin bukatun su. Wanan ya sa ake shan wahla wurin kirkira ayyukan Nbs da zasu amfani kowa da kowa. 
  9. Haɗuwar siffofi daban-daban da ke shafar mutum: Yana da mahimmanci a gane cewa mutane na fuskantar kalubale da yake chakudawa a lokaci guda kuma yake karfafa musu fahimtar daidaiton jinsi, launin fata, ƙabila, shekaru, kwarewa, yare, kalar sha’awar mutum, matsayin mutum a cikin alumma, tattalin arziki mutum da sauran abubuwa. Wadanda ke da nakasa ko kuma yan gudun hijira ba a saka su a cikin masu ba da umarni ko yanke hukunci, don haka matan da ke da waɗannan rauninka, ciki har da waɗanda suka fito daga ƙananan kabilu, na da wuya su shiga cikin tsarin NbS.

 

Amfanin hada kai da mata ’yan ƙauye wajen shiga cikin hanyoyin kula da muhalli masu tasiri akan jinsi na Nbs a Afirka

  • Samar da kuɗaɗen shiga: Hanyoyin kula da muhalli galibi suna haɗawa da noma mai dorewa, dasa itatuwan gona, da sauran ayyukan samun abin dogaro da kai mai dorewa. Ta hanyar shiga irin waɗannan shirye-shirye, mata ’yan ƙauye na iya samun kuɗi don kansu da iyalansu
  • Samun isashen abinci: Ayyukan NbS kamar aikin gona mai dorewa ko ilimin noman na iya samar da wadataccen abinci mai sinadirai masu inganci ta hanyar haɓaka nau’ukan amfanin gona masu juriya da dama. Matan karkara suna taka muhimmiyar rawa a cikin waɗannan ayyukan, don haka suna ba da gudummawa ga inganta noman abinci na gida da kuma ingancin abincin iyali 
  • Kiyaye muhalli: Galibin matan karkara su ne ke kula da albarkatun kasa a cikin al’ummominsu. Shigar su cikin ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli (NbS) na iya haifar da ingantaccen kiyayewa da sarrafa albarkatun ƙasa, ciki har da ƙasa, ruwa, da bambancin halittu.
  • Rage tasirin canjin yanayi da kuma daidaituwa da shi: Ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli galibi ana tsara su ne don su kara juriya kan sauyin yanayi. Ta hanyar yin noma na zamani da adana albarkatun kasa, matan karkara kan iya taimakawa yankin su wurin rage tasirin sauyin yanayi da saurin sabo da cenjin yanayi zai kawo.
  • Ingancin rayuwar alumma: Ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli yawanci suna da tasiri mai kyau akan jin daɗin al’umma gaba ɗaya. Misali, samun wuraren shakatawa a cikin birane, kula da ruwa mai ɗorewa, kiyaye gandun daji, da ingantacciyar iska suna ba da gudummawa ga ingantacciyar lafiyar jiki da ta hankali. Ta hanyar shiga cikin irin waɗannan shirye-shiryen, mata za su iya ba da gudummawa ga cikakkiyar lafiya da jin daɗin al’ummominsu.
  • Tallafi da daidaton jinsi:  A yawancin al’ummomi, matan karkara sun daɗe suna fuskantar ƙalubale wurin samun damar amfani da albarkatu da matsayin daukar hukunci akan abubuwa da ya shafi alumma. Shiga cikin ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli zai iya tallafawa mata ya sama musu damammaki kara koyan sana’oi, samun matakin jagoranci, da kuma shiga cikin masu daukar mataki a cikin alumma. 
  • Kiyaye bambancin halittu daban-daban: Ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli suna kara jadada muhimancin banbancin halittu. Ta hanyar shigarsu cikin ayyukan noma mai ɗorewa da kiyaye muhalli, mata za su iya taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye bambancin halittu
  • Kiyaye al’adu: Da yawan ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli sun sa mo tushe ne daka al’adu da ilimin gargajiya. A matsayin su na masu kula da ilimin al’adu, matan karkara za su iya ba da gudummawar su don kiyayewa da haɓaka al’adun gargajiya waɗanda ke tasiri ga muhalli.
  • Zamantakewa mai inganci: Shiga ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli na kara dakon zumunci a cikin alumma yayin da mutane suka taru suna aiki tare da cimma wata manufa. Ta hanyar hadin kai da hadin gwiwa tsakanin alumma, matan karkara za su ba da gudunmuwa wurin gina zamantakewa mai inganci da juriya.
  • Ilimi da horarwa kwarewa: Shiga ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli na bukatar ilimi da kwarewa. Ta hanyar samun ilimi da ƙwarewa a cikin ayyuka masu ɗorewa, matan karkara za su iya zama wakilan canji a cikin al’ummominsu, watsa bayanai masu mahimmanci ga sauran jama’a, da kuma ga yaya da jikoki masu zuwa. 

Acknowledgements

Gudunmuwa da ka: Stephanie Coucopoulos, Mai tsara shirye-shirye, Farm Radio International.

Tantancewa da ka: Sareme Gebre, kwarariya kan ayyukan da suka shafi muhalli don magance matsaloli, Farm Radio International, da kuma Michele Sona Koundouno, Kwarare a harkar daidaiton jinsi, Farm Radio International.

Information sources

Wuraren da aka samo bayanai

Angula, M. N. et al, 2021. Gidauniyar Karfafa Tasirin Jinsi na sauyin yanayi- Tsarin Daidaitawa na Al’umma a Namibia 13(18). https://doi.org/10.3390/su131810162

IUCN, 2021. Daji na bukatar mata dan dawo da martabar sa. https://www.iucn.org/news/forests/202103/forest-landscape-restoration-needs-women

IUCN, 2021. Hanyoyin taimakon matan karkara dan kare dajika. https://www.iucn.org/news/forests/202108/strategies-help-rural-women-protect-forests

IUCN, 2020. Ma’auni na Duniya na Ayyukan da Suka Shafi Muhalli: Tsarin da ke da sauƙin amfani don tabbatarwa, tsarawa, da faɗaɗa ayyuka of NbS. (1st ed.). Downloadable at: https://portals.iucn.org/library/node/49070

Majalisar dinkin duniya, 2011. Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta bayyana cewa “mata a yankunan karkara suna da damar zama “muhimman jigo” wajen yakar yunwa. Women could feed millions more people if given access to means of production – UN | UN News

Salcedo-La Viña, C., Trivedi, A., and Grace, K., 2023. Ƙarfafa Matan Karkara a Matsayin Manyan Jigogi a Ayyukan da Suka Shafi Muhalli. Takardar Nazari ta World Resources Institute, Yuni 2023 https://files.wri.org/d8/s3fs-public/2023-07/enabling-rural-women-key-actors-nature-based-solutions.pdf

UNEP-WCMC, 2020. Ƙarfafa Mata da ‘Yan Mata ‘Yan Karkara a Matsayin Mafita ga Dorewar Muhalli da wadataccen Abinci.. https://www.unep-wcmc.org/en/news/empowering-rural-women-and-girls-as-a-solution-to-environmental-sustainability-and-food-security

Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP), 2022. Ayyukan da Suka Shafi Muhalli: Damammaki da Kalubale don Faɗaɗa Ayyuka.. https://wedocs.unep.org/handle/20.500.11822/40783

N Women, 2021. Mata ‘Yan Karkara da Canjin Yanayi a Jordan. Akwai a https://wrd.unwomen.org/sites/default/files/2021-11/UNWomen-RuralWOmenJordan-Brief-WEB.pdf

Vi Agroforestry, undated. WESLAM. https://viagroforestry.org/projects/weslam/