Babancin-halitu

Daidaiton jinsi

Backgrounder

Gabatarwa

Ko ka taba tsayawa kayi nazari akan nau’inka rayuka masu ban mamaki daban-daban da suke duniyar nan tamu? Daga kwari mitsatsa har zuwa giwaye maka-maka, akwai dau’in halittu kala-kala, wanan dau’in shi ake kira da babancin-halittu. Amma, babancin-halittu ya wuce kyawawan abubuwa kawai – shine ainihin tushen inganticiyar duniya da jin dadin mu 

Menene banbancin halittu?

Babancin halittu, nau’i ne na kowace halitta a kowane mataki dake doron kasa, daka kwayoyin halittu, zuwa nau’in halittu zuwa muhallin halittun; daga mitsatsan ƙwayoyin halitu, zuwa manyan dabbobi, da duk abin da ke tsakanin su. Ya kunshi duk nau’oin halittu, da banbance kwayoyin halitu dake cikin su, da kuma muhali da wadanan kwayoyin halitu suke rayuwa. Fahimtar wadanan banbancin-halitu na da matukar muhimanci domin yana taimaka mana wurin dada sanin muhimancin rayuka da ke zagaye da mu da kuma irin chudanya da ya hade duk abubuwa masu rai.

Banbancin-halitti ba wai kawai ya hada da halittu tsiraru ba, ko kuma wanda suke cikin barazanar karewa, ko wanda suke cikin hatsari, amma har da ko wace halitta, da ga mutane zuwa tsirrai, dabbobi, kananen kwayoyin halittu, tsirai, da kuma dabbobi mara sa kashin baya. A Magana mafi sauki, banbancin halittu na nufin ire-iren halittu masu rai a doran kasa da kuma banbancin su.   

Matakan banbancin halittu

Halittu (kwayoyin halitta daban-daban): Wannan yana nufin nau’ikan kwayoyin halitta ko DNA da ke wanzuwa a cikin nau’ikan halittu da kuma tarin jama’u. Kwayoyin halitta kamar umarni ne da ke gaya wa halittu yadda zasu girma, su haɓaka, da kuma yin aiki. Adadin kwayoyin halitta ya bambanta tsakanin halittu daga kusan 1,000 a cikin bakteria zuwa 10,000 a wasu fungi da kuma kusan 100,000 ga babbar dabba. Misalin bambancin kwayoyin halitta shine bambancin nau’in karnuka, ko nau’in mangwaro, shinkafa, da sauransu. 

Nau’in Halittu (nau’in halittu daban-daban): Nau’i halittu na nufin wani rukuni na halittu masu rai da suke da kamanceceniya a wani yanki. Mambobin nau’i ɗaya na da siffofi iri ɗaya kuma suna iya rayuwa tare da haihuwar ‘ya’ya da za su gaje su. Misali, dukkan mutane suna cikin nau’i guda. Idan daji yana da girma, yana iya samun nau’o’in itatuwa daban-daban da yawa.

Muhalli (muhalli daban-daban): Muhalli kamar unguwa ne ko al’umma inda tsirrai, dabbobi, da ƙananan halittu ke rayuwa tare da juna sun a kuma mu’amala da abubuwan da ke kewaye da su, kamar ƙasa, ruwa, da iska. A cikin irin wannan “unguwar”, kowace halitta tana da rawar da take takawa, kuma suna dogaro da juna don su ci gaba da rayuwa. Misali, a cikin daji, bishiyoyi na bayar da iska mai kyau da mafaka, dabbobi suna cin shuke-shuke ko wasu dabbobin, yayin da ƙananan halittu ke rushe tarkace ko matattun abubuwa don tabbatar da daidaito da lafiyar muhalli..

Ma’anar wasu kalmomin halittu

    1. Kare halittu: Aikin karewa da kula da bam halittu don tabbatar da lafiyarsu da dorewarsu na dogon lokaci, domin tabbatar da daidaito da lafiyar duniyar mu. Biodiversity conservation: 
    2. Asarar halittu: Raguwa ko asarar nau’o’in halittu a wani yanki.
    3. Matsayin kariya (na halitta): Alamomin yadda nau’in halitta ke cikin haɗari ko tsira. Misali: Mai rauni, haɗarin gushewa, ko wadanda suke gushe gaba ɗaya. 
    4. Kimiyyar mu’amala da muhalli: reshen ilimi da ke nazarin halittu tare da alakar su da muhalli da suke rayuwa a ciki.
    5. Ayyukan muhalli: Fa’idodin da ɗan Adam ke samu daga muhalli. Misali: Ruwa mai tsafta, iska mai kyau, yaduwar furanni na amfanin gona.
    6. Halittun da ke cikin haɗarin shuɗewa: Nau’o’in halittu da ke cikin haɗarin shuɗewa saboda cenjin yanayin muhalli ta dalilin ayyukan ɗan Adam ko sauyin yanayi. Misali: Damisa da karkanda.
    7. Matsuguni: wurin zama halittu na ainihi.
    8. Halittun da suka mamaye wuri: Tsirrai ko dabbobi da aka shigo da su wani sabon wuri, kuma suna cutar da halittun da suka fi dacewa da yankin. 
    9. Kamun kifi fiye da kima: Kama kifaye da yawa fiye da yadda za su iya sake haihuwa da yawa.
    10. karamar halitta (Macroorganism): ƙaramar halitta da da ido zai iya gani ba tare da na’ura ba.
    11. Mitsitisyar hallita: Halitta mitsitsiya da ba za a iya ganinta da ido ba, musamman kamar kwayoyin bakteria
    12. Hanyoyi aiki masu daurewa: Yin amfani da albarkatun kasa ba tare da cutar da muhalli ba. Misali, kamun kifi a bisa ka’ida dan gudun karar da su gaba daya.
    13. Farauta: Farautar dabbobi ba bisa ka’ida ba. Misali: Kashe giwaye saboda cire musu kaho.
    14. Sababun birane: Faɗaɗa birane har wurin namomin daji. Misali: Ginin sabbin unguwanni da ke rushe matsugunin dabbobi ko halittu.

Muhimman bayanai game da bambancin halittu

Ire-iren muhallin halittu

Halittu dake rayuwa a muhalli da ke ban ƙasa: Waɗannan su ne halittu da muhallin su ke kan ƙasa.

  • Muhallin daji na da girma kuma yana ɗauke da nau’o’in bishiyu, dabbobi, furai, da bakteriya da ke mu’amala da juna. Akwai nau’o’in tsirrai da dabbobi daban-daban a dazuka, ciki har da bishiyu, itatuwan kuka, ganyan magunguna da ƙwayoyin halitta ƙanana. Dazuka Afirka na da matuƙar halittu dabn-daban. Misalai: Dajin Congo Afirka ta Tsakiya, Dajin Atewa (Afirka ta Yamma), da Dajin Kakamega (Afirka ta Gabas). 
  • Muhallin ciyayi shi kuma wanan ciyawa ce ta mamaye wurin, sanan bashi da cunkoso kamar daji. Dajin Savana na Afrika na daya daka cikin muhallin ciyayi. Misali: Serengeti (Tanzaniya) 
  • Muhalin Hamada shi kuma wanan busashen muhali ne mai dauke da dai-dai kun tsirai. Misali shine Hamadar Sahara dake Afrika ta Arewa. Wadannan wurare na fama da ƙarancin ruwa kuma suna da nau’o’in halittu da suka saba da irin wannan bushewar yanayi. 
  • Muhali mai duwatsu shi a wurare masu tsawo yake, sanan yana da furai da tsirai da suka saba da sanyi mai tsananin gaske. Duwatsun Rwenzori (kasar Uganda) da kuma Duwatsun Drakensberg da ke (South Africa).

Halittu da ke rayuwa a muhallin ruwa (Ruwan kogi, da ruwa na bakin teku): Waɗannan su ne suka hada muhallin cikin ruwa, ruwa mai dandado (tafkuna, koguna, dausayi) da kuma na teku (kamar gabar teku, da reef na coral).

  • Muhallin ruwa mai ɗanɗano: Misali, Tafkin Victoria a Afirka ta Gabas yana da kifaye, tsirrai, da sauran halittu da suka saba da ruwa marar gishiri. 
  • Muhallin teku: Misali, gabar mangroves a Ghana tana ɗauke da nau’o’in halittu na ruwa iri-iri.

Muhallin da mutane suka kirkira: Irin wadanan wuraren da mutane su ka kir-kira kamar gonaki, lambuna da kuma wurin kiwaon kifi. 

  • Filayen noma da gonaki su ne muhallin da dan adam ya gina domin samar da abinci da kayan amfanin gona. 

Me yasa halittu daban-daban ke da muhimmanci?

Fa’idojin da ke tattare da bambancin tsirrai, dabbobi, albarkatun ruwa da ƙananan halittu suna da yawa. Wasu daga cikin fa’idodin sun haɗa da:

  • Tattalin arziƙi (Tushen samun kuɗi ga mazauna ƙauyuka da birane, da kuma samun kuɗaɗen shiga daga fitar da kaya ƙasashen waje).
  • Rayuwa da zamantakewa (hanyar samun abinci, magunguna don kula da lafiya da warkar da cututtuka)
  • Addini da al’ada (silar samun nutsuwa wurin bauta)
  • Kyan gani da nishadi
  • Muhalli na halitta (kare wuraren tara ruwa, hana iska mai karfi ko guguwa, farfaɗo da daji, da kula da kasar noma da gyara ta.)
  • Muhalli na zamantakewa (taimakawa wajen daidaita iskar carbon a sararin samaniya, da rage gurɓataciya iska da ruwa.)

Ba tare da halittu daban-dabam ba, babu rayuwa. Kowace halitta ko ƙaramar halitta a cikin muhalli na taka muhimmiyar rawa kuma tana da matuƙar amfani ta hanyoyi daban-daban. Bambancin halittu yana da mahimmanci a fannoni da dama kamar yadda aka bayyana a ƙasa:

Taimakawa wurin ci gaba da rayuwa: Dukkan halittu – ciki har da mutane – suna da alaƙa da juna a matakai daban-daban na bambancin halittu. Bambancin halittu yana tallafawa ayyukan muhalli da suke da matuƙar muhimmanci ga rayuwarmu, kamar samar da abinci, daidaita yanayi, da cigaba da samar da sinadarai masu amfani. Misali, muhallin da ke da bambancin halittu kamar dazuka suna rage zafi da sauya yanayi da kuma samar da ruwa mai tsafta.

Lafiyar ƙasar noma: Fungai da bakteriya da ke cikin ƙasa suna balla tarkacen halittu, don samar da sinadarai da tsirrai ke bukata su girma. Wannan yana taimakawa wajen kiyaye ƙasar noma da bunkasa samar da abinci.

Samar da magunguna: Yawancin sinadarai na magani suna fitowa ne daga tsirrai da dabbobi, kuma suna da matuƙar amfani wajen warkar da cututtuka da kuma inganta lafiya. Kare halittu daban-daban yana ba mu damar gano sabbin hanyoyin magani. Misalai:

Motsa jiki da lafiyar kwalkwalwa: banbantakar halittu na taimakawa mutane da ke zaune a birane samun juriya fiye da na kauye ta hanyar rage damuwa da inganta lafiyar kwalkwalwa. Wuraren shakatuwa masu dauke da korayen ciyayi da dazuka a cikin birane na kara bawa mutane dmar samun hutu. A wasu lokuta, likitoci na ba wa mutum shawarar yin zagaye ko zama a wuraren shakatawa dan magance wasu cututtuka kamar damuwa da faduwar gaba. Nishadi da motsa jiki ma na da muhimmanci wajen kula da lafiyar jiki da kwakwalwa. 

Yawon buɗe ido: Wannan yana daga cikin hanyoyin samar da tattalin arziƙi. Bambantar halittu yana ƙarfafa yawon shakatawa, inda baƙi na san ziyarar wuraren da ba a lalata ba, wanda ke kawo kuɗaɗen shiga ga al’umma da kuma inganta wayar da kai game da muhalli. Yawon buɗe ido da da albarkatun halittu mabanbanta ke dauke shi na samar da ayyukan yi da tallafa wa tattalin arziƙin yankuna. Misalai sun hada da ziyarar kebatatun dazuka namun daji da ke Afrika:

  • Maasai Mara, a kasar Kenya: Shahararren wuri ne saboda yawan dabbobin da ke ciki, musamman lokutan “babbar hijra” da gwanki suke yi duk shekara.
  • Kruger National Park, dake Afrika ta Kudu: Ana zuwa ziyara don ganin manyan dabbobi da akai wa lakabi “manya biyar” (zaki, damisa, giwa, kada, da saniyar daji)
  • Kakum National Park, Ghana: Ya shahara saboda gadar sama, wadda ake hawa ta musamman don kallon girman bishiyu da namomin daji. 
  • Mole National Park, Ghana: ta shahara saboda yawan giwaye da sauran namomin daji, wanda ke kawo matafiya yawon bude ido. 
  • Cape Three Points Forest Reserve, Ghana: Wanan yana janyo masu san kallon tsuntsaye da son binciken gefen teku. 
  • Bwindi Impenetrable Forest, Uganda: Wanan wurin gida ne ga manyan birurika masu hawa duwatsu, wanda yake kawo baki masu son kallon su. 
  1. Kare al’adun gargajiya da na bauta da kuma kyautatuwar rayuwa: Al’adu da yawa a Afirka, ciki har da kabilu daban-daban na kasar Ghana, sun kula alaƙa ta musamman tsakanin halittu mabanbanta da al’adun gargajiya da kuma addini. Mutane da dama na samun amfani na  al’ada da nishaɗi daga halittu mabanbanta. Wasu dabbobi da tsirrai suna da matsayi mai girma a cikin waɗannan kabilu. A misali, ana kallon wasu dabbobi da bishiyu da wani mastayi a al’adance  a gurin wasu kabilu a kasar Ghana. Wuraren shan iska na samr da wurin yin ibada da shakatawa. Misali, akwai dazuka da aka cemfa su a kusan kowace ƙasa a Afirka. Kare bambancin halittu yana da matuƙar muhimmanci wajen adana waɗannan al’adu. 
  2. Ingantacen ruwa da iska: Bambancin halittu, musamman tsirrai, na taimakawa wajen tsaftace iska ta hanyar shakar gurbataciyar iska sai su fitar da kyayawar iskar oxygen. Haka nan kuma, akwai halittu daban-daban da ke taimakawa wajen tace ruwan sama, da hanyar tace gurɓatacen ruwa, su inganta shi ya fito a tsaftatacen ruwa. Iskar oxygen da tsirrai ke fitarwa na taimakawa wajen tabatar da ci gaban rayuwa. Kamar yadda karin magana ke cewa, “Idan bishiya ta ƙarshe ta mutu, mutum na ƙarshe ma zai mutu.”

  3. Ka’idojin tafiyar da sauyin Yanayi: Tsarin halittu mabanbanta na taimakawa wajen daidaita yanayi ta hanyar rage zafin rana da matsanancin yanayi. Dazuka da rafuka suna taka rawa sosai wajen wannan daidaiton.

  4. Kirkire-kirkire da ilimi: Nazarin nau’o’in halittu daban-daban na iya haifar da sababbin bincike na kimiyya da kirkire-kirkire da za su amfanar da fannoni da dama kamar noma, lafiya da masana’antu.

  5. Tsaftace muhalli: Halittu masu cin tarkace kamar fungi da dabbobin da ke cin matattun halittu na taimakawa wajen rage datti da sake maida tarkace zuwa sinadaran gina ƙasa. Waɗannan halittu suna rage yawan tarkace da kuma hana yaduwar cututtuka, sun a tsaftace muhalli. A yayin da suke yawo, su na watsar da iri wanda ke taimakawa wurin ci gaban tsirrai da lafiyar muhalli gaba ɗaya.

  6. Kayan abinci masu gina jiki da dorewar samun abinci: Halittu mabanbanta na tabbatar da samun nau’o’in abinci daban-daban da ke da matuƙar amfani ga lafiyar ɗan adam. Abincin mutane shine tsirrai da dabbobi. Halittu mabanbanta na tabbatar da akwai ire-iren amfanin gona da dabbobi daban-daban, waɗanda ke da matuƙar muhimmanci don samun abinci mai gina jiki. Haka kuma, nau’o’i halittu daban-daban na taimakawa wajen ƙara ƙarfin noma ta samar da iri masu juriya ga cututtuka da kwari. Idan ba mu kare waɗannan tsirrai da dabbobi ba, mun tabatar da cigaba da rayuwar su, nan gaba babu abin da za mu ci. 

Barazana ga Halittu Mabanbanta

Akwai abubuwa da dama da ke barazana ga halittu mababanta. Za mu rarraba su zuwa manyan rukuni guda huɗu: 

  1. Rasa Muhlli ko rusa shi: Ana sare dazuka saboda dalilai mas yawa, ta dalilin haka ake rusa wa dabobi wurin zaman su. Alal misali:
  • Sare itatuwa ba tare da dasa sabbi ba na daya daga cikin manyan dalilan rusa muhalli da rarabewar dazuka. 
  • Mayar da wuraren zaman namun daji zuwa gonaki – wannan abu ne da ke yawaita a Afirka.
  • Fadada birane da gina ababen more rayuwa.

Rabewar dazuka wata hanya ce ta rusa muhalli namun daji. Ka ayyana daji mai girma da bunkasa ana sasare bishiyun ciki ana raraba shi tsila-tsila. Hakan yana faruwa yayin da ake yin tituna, gonaki, ko gina garuruwa da suka ratsa ta cikin daji. Wannan yana haifar da matsaloli babba ga dabbobi. Dabbobi na rasa yankunan da suke rayuwa, kuma hakan na sa su cikin wahala wurin neman abinci da mafaka. Sau da yawa suna shiga cikin unguwannin mutane, kuma hakan na iya kaiwa ga mutuwar su ko kuma kashe mutane. 

Amfani da abu fiye da kima: Yawan kamun kifi da farautar dabbobi na barazana ga rayuwar namun daji. (misali, farautar giwaye a Afirika). Wanan ya hada da:

Yawan kamun kifi a tekun.

Farauta da kashe dabbobin da ke gab da karewa kamar giwa, damisa, zakuna, barewa da karkanda, da sauran su, musamman a Afirka.

Cinikin dabbobi da itatuwa ta haramtacciyar hanya.

Gurbata muhalii da cenjin yanayi: Hayaki sakamakon amfani da gas, sinadirai da ake zubar wa da ka masana’antu na taimakawa wurin gurbata iskar da muke shaka, da ruwa da kuma kasar noma. Wadanan sun hada da: 

  • Gurbata teku da robobi: Robobi da ke yawo a saman ruwa na ɗauke da sinadarai masu cutarwa da ke da illa ga dabbbobi har yayi sanadiyar kashe su a cikin ruwa. 
  • Gurbataciya iska daga masana’antu da ababen hawa a birane: Hayakin da yake fita yana lalata ƙwayoyin halittu abubuwa masu rai, dabbobi da muhallinsu. 
  • Gurbatacen ruwa da ka noma da hakar ma’adinai: Sinadarai masu guba da ake amfani da su a wurin noma da hakar ma’adinai na bin hanya ya shiga ruwa ya lalata halittun da ke ciki.
  • Dumamar yanayi na rusa tsarin sauyin yanayi: Misali, narkewar kankarar dake cen Aktic na cutar da beya da ke rayuwa a cikin kankara, wanda ya dogara da kankarar wurin nemo abinci da haihuwar yaya. Yayin da kankara ke narkewa, tilas beyan ya yi doguwar tafiya a cikin ruwa wajen nemo abinci da mafaka, wanda ke janyo gajiya da rashin karfin jiki da zai basu damar haihuwa. 
  • Yawaitar faruwar iftila’i kamar ambaliyar ruwa da gobarar daji alamu ne na sauyin yanayi. Sauyin yanayi na haifar da karuwar gobara a Afirka, musamman a ƙasashen Afirka ta Kudu, Namibiya, da Botswana. Wadannan gobara na lalata muhallai da rushe tsarin halittu.

Nau’in halittu masu yaduwa: Tsirrai da dabbobi da aka kawo daga wasu yankin na iya fin ƙarfin nau’o’in halittun da ke yankin, su tilasta musu barin muhallin da suka same su a ciki. Wannan yana kama da kawo ɗan dambe wurin taro. Misalai: 

  • Shudin macijin bishiya (Boiga irregularis) da ke cutar da tsintsayen Guam: Wannan maciji an kawo shi a rashin sani zuwa tsibirin Guam ana kyautata zaton bayan yaƙin duniya na biyu, a cikin jirgin kaya. A yanzu haka ya raba yawancin tsuntsayen da ke Guam da ka gidajen su, kuma ya hallaka wasu nau’in tsuntsaye gaba ɗayan su, wa sun su kuma ya jefa su cikin barazana karar da su gaba daya.
  • Yaduwar tsirran ruwa masu mamaye muhalli kamar tsiren Awoloda da kyamia  Wadannan tsirran ruwa daga Kudancin Amurka aka kawo su zuwa kasar Ghana da wasu ƙasashen Afirka. Suna iya mamaye kogi da tabkuna, su hana ruwa gudu yadda ya kamata, har ya janyo rashin wasu nau’in halittun da yake gidan su ne nan. 

Balewar cututuka: Balewar cututtuka na iya rage yawan wasu nau’o’in halittu sosai. Idan cuta ta kashe dabbobi masu yawa daga nau’i guda, sauran halittu da su ka dogara da su don abinci ko mafaka za su fuskanci barazana, kuma hakan yana iya shafar dukan sauran halittun da suke zaune a wuri daya. Misalai:

  • Bayyanar cututtukan da ke wucewa daga dabbobi zuwa dan adam: Cutar HIV da Ebola sun kashe mutane da dabbobi da yawa. 
  • Yaduwar ƙwayoyin cuta da ke cutar da halittu: Wasu cututtuka na shafar wasu nau’in dabbobi da tsirrai kai tsaye, da haka s uke rage yawansu a duniya. Misali, ƙwayar chytrid fungus ta yadu a duniya sosai, ta kashe wasu nau’in kwadi da yawa, ta dagula muhalin da suke ciki. 

Yadda za a Kare Halittu Mabanbanta (Tare da Misalai):

A matakai daban-daban – na duniya, da yanki da na kuma na ƙasa – ya kamata a ƙara ƙaimi wajen kare halittu mabanbanta, musamman irin wadda Afirka ke da ita. Muhimman matakan kare muhalli na da matuƙar amfani wajen hana lalacewar halittu. Amma har gidaje da al’umma za su iya taka rawar gani.

  • Ƙirƙirar wuraren kariya: A kafa wuraren kiwo da kula da namun daji. A kasar Ghana, akwai Kakum National Park don kare dazuka da muhalli. Al’umma ma za su iya kare dazuka a yankinsu ta hanyar samar da dokokin shiga da amfani da kayan daji.
  • Gudanar da dazuka cikin hanyar da za ta dore: Gudanar da dazuka tare da hadun gwiwa da alumma wata hanya ce mai kyau ta kare daji da hana sare bishiyu dan jin dadi kawai. Wannan zai iya haɗawa da amfani da daji wurin kiwon zuma, wanda zai samar da amfanin mai dorewa, ba tare da sare itatuwa ba daga dajin.
  • Yaki da farauta ba bisa ka’ida ba: A ƙarfafa sintirin hana farauta da kisan dabbobi kamar giwaye da rhino. Misali, a kasar Botswana, an samu nasarar rage kisan giwaye ta hanyar shirin “Operation Pangolin” wanda ya haɗa da amfani da jiragen sama na sintiri, karnuku, tare da haɗin gwiwa al’umma.
  • Rage amfani da leda/robobi: A dakile yawan gurbacewar muhalli da robobi ke haifarwa. A kasar Rwanda, dokar hana amfani da leda mai amfanin daya tun daga 2008 ta kasance nasara sosai, inda ta rage yawan shara da illa ga dabbobi da tsarin halitta.
  • Tallafa wa noma mai ɗorewa: A karfafa amfani da hanyoyin noma da ba sa cutar da muhalli, irin su amfani da takin gargajiya don inganta lafiyar ƙasa. Dogaro da sinadarai sosai na lalata ƙasa da hallaka ƙwayoyin halitta kamar fungi da bakteriya. A Yammacin Afirka, manoma da dama musamman a kasashen Senegal da Burkina Faso, na amfani da hanyar zaï – hanyar gargajiya ta tona ƙananan rami da cike su da tarkacen shuka domin ajiye ruwa da ƙara ɗimbin amfanin gona

Farfado da filaye da suka lalace: A dasa itatuwa da gyara wuraren da mutane su ka lalata don ƙirƙirar sabbin muhalli. Misali, shirin “Katuwar Koriyar Katanga” a yankin Sahel na Afirka babban yunƙuri ne na dakile hamada da mayar da ƙasa mai amfani ta hanyar dasa itatuwa da kula da gonaki. Manoma ma na iya amfani da hanyar sake haifar da itatuwan daji da kansu a gonakinsu. 

Karfafa yawon bude ido: A inganta yawon bude ido da zai amfanar da al’umma da ke zaman a yankin da kare muhalli. Misali, yawon safari a Maasai Mara, a kasar Kenya. Dadin dadawa, a kasar Namibia, mutanen gari ne suke gudanar da wuraren da aka killace, kamar kilatacen wuri da ke “Skeleton Coast”, y ana basu damar amfana da kudaden shiga da ka yawan bude ido, a lokaci guda kuma suna kare namomin daji da muhalin su.

Ilimantar da al’umma: Wayar da kan mutane game da muhimmancin halittu mabanbanta ta hanyar gudanar da shirye-shiryen ilimi a makarantu, unguwanni da kuma kauyuka. Misali, shirin “zagaye gari” a kasar Kenya na amfani da hanyoyin koyarwa masu jan hankali don ilmantar da yara da al’umma game da kare halittu mabanbanta. 

Tallafawa ilimin gargajiya: Haɗe ilimin gargajiya da na zamani, musamman mutanen da ke zaune daidai da yanayi na tsawon shekaru. Misali, mutanen Maasai a kasar Kenya suna da dogon tarihi na rayuwa tare da dabbobi. Hanyoyinsu na kiwo da amfani da tsirrai na magani suna inganta dangantaka mai kyau da muhalli. 

Ba da muhimanci akan makamashi mai sabuntawa: A rage dogaro da amfani da irinsu man fetur, wanda ke ƙara dumamar yanayi. Misali, a Afirka ta Kudu, ana aiwatar da manyan ayyukan hasken rana don rage amfani da kwal da hana illar sauyin yanayi ga halittu.

Dakile yaduwar halittu masu mamaye wuri: Daukar matakai don hana yaduwar tsirrai masu mamaye wuri dan kare tsirai masu amfani da ke wurin. Misali, a kasar Ethiopia, ana amfani da hanyar samar da abubuwa masu rai dan dakile yaduwar ciyayi da ba’a so, kamar kawo kwari da suke cin ciyayi dan su rage yaduwar ciyayi da kuma kare tsiran da suke wurin. 

Tsaftace gurɓatattun wurare: Daukar matakai don rage gurbacewar iska da ruwa daga masana’antu da kuma aikin gona. Misali, Shirin tsaftacen kogi Ebonyi” a Najeriya shiri ne da al’umma suka jagoranta don cire shara da robobi daga kogin Ebonyi, wanda hakan ya kara ingancin ruwan don amfanin mutane da dabbobi.

Tallafawa kamun kifi mai ɗorewa: A kafa dokoki da ƙayyade yawan kamun kifi don hana kamu fiye da kima da kare rayuwar dabbobin ruwa. Misali: A kasar Senegal, an samar da “kilace wurin dabbobin ruwa” da kuma iyake adadin kifin da za’a iya kamawa don kare yawan kifin da muhalli. A Ghana kuma, ana dakatar da kamun kifi a wani lokaci na shekara don ba kifaye damar hayayyafa da hana su karewa. 

Adana ruwa: A ƙarfafa amfani da ruwa cikin hikima a aikin gona da rayuwar yau da kullum don adana ruwa. 

Karfafa bincike: A ƙarfafa bincike kan kare bambancin halittu da hanyoyin kiyaye su, don samar da ingantattun dabaru don kare halittu na musamman da muhalli a Afirka.

Gina hanyoyi don amfanin dabbobi: A samar da hanyoyin da dabbobi za su bi a saukake  tsakanin yankuna da aka raba. Misali, Babban wurin da aka kebe na Kruger da ke Afirka ta Kudu yana haɗa wuraren da aka tanada don dabbobi.

Karawa alumma karfin gwiwa wurin adana muhalli: A bai wa al’umma dama da ƙarfi gwiwa su kula da albarkatunsu yadda ya kamata. Wannan na ƙarfafa riƙon amana da alhakin kula da muhalli. (Misali, shirye-shiryen adanai a Namibia).

Ƙarfafa amfani da kayayyaki masu dorewa: Rage illa da muke yi wa muhalli ta hanyar amfani da kayayyakin da zaka iya juya kayi amfani dasu sama da daya dan rage tara shara ko bola, wannan ya na da tasiri akan yadda ake gudanar da kasuwanci a duniya ya kuma shafi halittu mabanbanta a Afirka. 

Ƙoƙari na musamman don ƙara yawan halittu masu haɗarin karewa a ban kasa Misali:

    • Bakake da fararen Karkanda: A kasar Kenya, masu sintiri dauke da makamai na kare karkanda daga sharrin mafarauta. A Afirka ta Kudu, ana cire wa Karkanda ƙahunhuna su don kare su da ka farauta. ​(Mujallar gandun daji)​​ (Kimiyya a kullun).
    • Kusu-kusu: A kasashen Vietnam da China, ana ceton kusu-kusu da suka fada matsala, a kula da su har sai sun warke sannan a maida su cikin daji. Hakanan Hukuma ta yi doka don hukunta masu fataucin su. ​(Mujallar gandun daji)​​ (Kimiyya a kullun).
    • Damisa: An kafa wuraren kariya a kasashen Rasha da China don kare damisa. An kuma ƙara tsaurara matakan hana farautar su. (Gidan tarihi na America)​​ (Kimiyya a kullun).
  • Ranar kore a ksasr Ghana wanda ta kama 1 ga watan Yuni na kowace shekara domin dasa itatuwa, ciki har da nau’o’in da ke fuskantar bacewa. Hakanan, ana rufe teku da koguna na ɗan lokaci don kare kifaye a lokacin haihuwar su.

Wasu dokokin kasa da kasa, da na Yankuna da kuma Na Gida don Kare Halittu mabanbanta

Dokokin Kasa da kasa

Dokokin Yanki 

Acknowledgements

Godiya

Gundumuwa daka: Linda Dede Nyanya Godji Incoom, yar jarida ma zaman kanta ta re da AgriGhana (http://agrighanaonline.com/), a kasar Ghana.

Tantancewa da ka: Sareme Gebre, Masani da ke aiki a cibiyar samar da waraka, Farm Radio International

Tattaunawa da: Emmanual Nii Attram Taye, mai bincike, a cibiyar adana halittu daban-daban, a jami’ar Ghana, Legon.

 

Information sources

Manazarta:

  1. Gidan Tarihi na Amurka. Menene banbancin halittu? https://www.amnh.org/research/center-for-biodiversity-conservation/what-is-biodiversity
  2. Benton, Tim and Wallace, John. 2023. Barazana ga banbancin halittu. Chatham House. https://www.chathamhouse.org/2023/04/threats-biodiversity
  3. Biodiversity. https://www.britannica.com/science/biodiversity
  4. Corlett, R. T. 2020. Kare Makomar Mu ta hanyar Kare Halittu. Itatuwa kala-kala. Vol. 42, ta 4.. Itatuwa kala-kala. Vol. 42m ta 4.
  5. Davies, Glyn. 2002. Halittun Daji na Afirka: Binciken Dabbobi masu kashin baya. Earthwatch Institute.
  6. Fritts, T. H., & Rodda, G. H. 1998. Rawar Da Halittu masu mamaye wuri suke takawa wajen lalata tsarin muhalli: Misalin Guam. Annual Review of Ecology and Systematics, 29(1), 113-140.
  7. Tsarin Dabaru da Ayyuka na Kare Halittu a Ghana. Nuwamba 2016. Ma’aikatar Muhalli, Kimiyya, Fasaha da kirkire-kirkire.
  8. Global Biodiversity Forum report. 1997. World Resources Institute. IUCN The World Conservation Union.
  9. Gundun kalmomi na halittu mabanbanta. Ethiopian Biodiversity Institute (EBI). (n.d.). https://ebi.gov.et/biodiversity/education/glossary-of-biodiversity-terms/
  10. Cibiyar Kuɗi ta Duniya don Kula da Dabbobi. 2024. Kalmomin halittu daban-daban da ma’anoninsu. https://www.ifaw.org/international/journal/biodiversity-terms-definitions
  11. Owusu, E.K.A et al. 2020. Shuke-shuken Ruwa na Waje a Ghana: Bita kan Matsayinsu na Yanzu da Hanyoyin Sarrafawa. Jaridar Kimiyyar Muhalli da Lafiya, Sashe na B
  12. Smithsonian National Museum of Natural History. Menene halittu mabanbanta?  https://naturalhistory.si.edu/education/teaching-resources/life-science/what-biodiversity
  13. Swanson, Timothy. 1997. Daukar Mataki na Duniya don Bambancin Halittu: Tsarin Duniya na aiwatar da yarjejeniyar bambancin halittu. Routledge.”
  14. United Nations. 1992. Yarjejeniyar Bambancin Halittu, Mataki na 2
  15. Wilson, John W and Primack, Richard B. 2019. Ilmin Kariya na Halittu a Nahiyar Afirka ta Kudu da Sahara. Masu Wallafa: Open Book.”
  16. 2021. Gargadi: Inda ake asarar halittu ke faruwa a duniya. World Wildlife Fund. https://www.worldwildlife.org/magazine/issues/summer-2021/articles/a-warning-sign-where-biodiversity-loss-is-happening-around-the-world