Tallan Rediyo akan masara

Noma

Lura ga mai watasa shiri

Abun lura ga masu gabatarwa

Masara tana daya daka cikin manyan amfanin gona a wasu sassan Najeriya, inda aka kiyasta hekta miliyan 6.85 da ake shuka masara a shekarar 2019, a cewar hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya.

A wanan shirin rediyon, zaka kara koyon abubuwa iri-iri da suka danganci ayukan noman masara, wadanda suka hada da:

  • Zaban wurin noma
  • Auna girman fili
  • Amfanin cire ciyayi
  • Gano takin zamani na kwarai
  • Noman masara na dabara a sauyin-yanayi, kashi na 1
  • Noman masara na dabara a sauyin-yanayi, kashi na 2
  • Magance kwari ta hanyar gargajiya
  • Muhimancin busarwa

Wadanan shirin sun banbanta a tsayin lokuta, wasu suna kaiwa daka dakika 45-60 sanan za’a iya sasu dayawa yayin shirye-shiryen noman masara da kuma ayukan bayan girbi. Zakuma a iya sasu a wasu lokutan da manoma suka bada hankalinsu suna sauraro, musamman a muhimman lokuta na cikin kalandar noman masara.

Rubutunsa

Talla #1:
Zaban wurin noma

MAI BAYANI:
Manoma! Domin samun amfanin gona mai kyau, ku zabi gona mafi kyau. Ga kyakyawan abubuwa uku na fili noman masara.

Na farko, filin ya zama a shimfide yake.

Na biyu, kasar wurin ta zama tana zukewa tare da rike ruwa mai yawa ba tare da ta jike ba. Kasa mai laushi itace mafi kyau dan shuka.

Na uku, kasar ta zama tana da kwayoyin sinadirai da yawa. Kasa mai kalar baki-baki ko mai dan-duhu sun fi samun kwayoyin halitu masu amfani ga noma.

Idan kasar ka na da abubuwa ukun nan—wato kasar ta zamo a shimfide sumul, tana rike ruwa da yawa ba tare da ta jike ba, sanan tana cike da kwayoyin halitu—toh ka dau hanya mai kyau ta samun amfanin gonan noman masara mai albarka!


 

Talla #2:
Auna girman fili

MANOMI 1:
Wai a duniyan nan mai kake da ma’aunin tef— da igiya, da turaku…. duk wadan abubuwan?

MANOMI 2:
Auna gona ta.

MANOMI 1:
Amma me yasa? Ka riga ka san kana da hekta uku!

MANOMI 2:
Eh, amma in na auna gona ta dai-dai da dai-dai zai taimaka mun wurin adana kudi.

MANOMI 1:
Yanzu na ma fi rikicewa. Ta yaya amfani da ma’aunin tef zai taimaka maka wurin adana kudi?

MANOMI 2:
Abu mai sauki. Idan na san ainihin girman gona ta, zan iya lissafa daidai takin da sauran abubuwan da zan siya. Don haka kullum ina da isashe sanan bazan yi asarar komai ba.

Sanan kasan me kuma?

MANOMI 1:
Fada mun.

MANOMI 2:
Idan na auna fili na, zan iya kimanta nawa zan samu in nayi girbin masara ta. Wanan zai nuna mun ko masara ta zata bani riba ko faduwa a shekarar. Idan faduwa ne, zan iya shuka wani abun da zai fi bani riba. Saboda haka auna fili na yana taimaka mun wurin adana kudi.


 

Talla #3:
Amfanin cire ciyawa

MAI BAYANI:
Me yasa manomi zai cire ciyayin masara?

Ga kyawawan dalilai hudu da yasa:

Na farko, cire ciyawa nasa masara tayi amfani da takin da manomin ya zuba, a maimakon ciyayi suna amfani da shi.

Na biyu, ciyayi na iya tara kwari da saura kwayoyin halittu masu sa cuta.

Na uku, ciyayi na rage albarkar amfanin gona ta sace sinadirai, ruwa, hasken rana da wuri.

Na hudu, idan an gama cire ciyayi, mutatun ciyayin na kara wa kasar wurin sinadirai.

Saboda haka ka cire ciyayin ka da wuri kamar sati biyu ko uku bayan shuka. Sanan ka sake yin na biyu sati biyar ko shida bayan shuka.

Zakayi murna sosai in kayi haka!


 

Talla #4:
Gano takin zamani na ainihi

MAI BAYANI:
Manomi! Ka bi a hankali! Akwai takin zamani na bogi a kasuwa!

Ga hanyoyi biyu masu sauki na gano taki na ainihin gaske.

Na farko, hukumomin noma kamar ma’aikatar noma da ADPs, ke bada shawara akan takin zamani na ainihi. Saboda haka, kana tuntubar malaman gona na kananen hukumomin ku kafin siya.

Na biyu, takin zamani na ainihi na da tabbaci da hatimin SON, Cibiyar tantancewa ta Nijeriya da FEPSAN, Kungiyar masu samar da takin zamani ta Nijeriya.

Idan hukumomin noma basu ba da shawara akan taki ba, kuma SON da FEPSAN basu ba da tabbaci da hatimin su ba, KAR KA SIYA!


 

Talla #5:
Noman masara mai dabara na sauyin-yanayi, kashi na 1

MANOMI 1:
(Karaya) Ina ruwan sama ne? Oh, wanan sauyin yanayi zai mun illa.

MANOMI 2:
Kar ka karaya, dan-uwa. Akwai abubuwan da zaka iya yi. Ka zama mai dabara a harkar sauyin yanayi.

MANOMI 1:
Amma ta ina zan fara? Zaka iya fada mun abubuwa uku kacal da zan iya yi?

MANOMI 2:
Abu mai sauki!

Na farko, kar ka taba kona gonar ka. A maimakon haka, ka bar ragowar amfanin gona a gonarka. Suna ajiye danshi a kasa sanan suna rubewa bayan wani lokaci su karawa kasar ka yalwa.

Na biyu, kayi amfani da kayan aiki masu sauki. Idan lokcain shuka yayi, kayi amfani da manjagara da kuma amalanke. Manyan mashinan aikin gona zasu iya tsuke kasar wurin. Sanan ma dai, manyan mashina suna hargitsa kasar sama ne kawai.

Abu na karshe, gwargwadon iko, kana amfanin da takin gargajiya, sanan kana binne takin zamani a cikin kasa a ko da yaushe.

Kana da gaskiya, dan’uwa, sauyin yanayi na da wahala. Amma zamu iya yin abubuwa da yawa ta hanyar noman dabara na sauyin-yanayi!


 

Talla #6:
Noman masara mai dabara na sauyin-yanayi, kashi na 2

MAI BAYANI:
Ana cikin wani lokaci mai wuya na zama manomi. Hasashen yanayi yana zama abu mai wuya, ruwan sama ya zama ba tabbas, yanayin damina ya zama kadan, ga fari, kwari da cututuka ta ko ina. Amma ga abubuwa kadan da manomi mai noman dabara na sauyin-yanayi zai iya yi ya ci nasara.

Na farko, ka bada hankali sosai akan lokutan shuka sanan kana sauraran hasashen yanayi da akeyi, wanda ya hada da kowace rana, da na sati, da kuma na shekara.

Na biyu, ka shuka irin masara ma jure-fari da ke girma a cikin kwana 100 bayan shuka ya zama ya kuma dace da yankin da kake.

Da ka karshe, ka shuka wake mai dauke da sinadirin Nitirogin ko sauran dangin wanke a lokacin da masara ka ta fara yaya. Ta haka, waken zai bar wa masara sinadirin nitirogin domin amfanin shukar masara da za kayi nan gaba.

Akwai hanyoyi da yawa na shawo kan sauyin yanayi. Wadanan kadan ne kawai daka ciki.


 

Talla #7:
Kula da kwari na gargajiya

MAI BAYANI:
Kwari da yawa na san cin masara, wanda suka hada da tsutsa, tsutsotsin kara, beraye, da kuma tsuntsaye.

Feshin maganin kwari daya daka cikin hanyoyin maganin kwari ne. Amma mene ne hanyoyin maganin kwari na gargajiya. Yana yin aiki kuwa?

Ga hanyoyi hudu mara sa tsada, masu saukin yi, na magance kwari na gargajiya da zai taimaka maka.

Na farko, dan magance kwari da cututuka, ka tambayi malaman gona akan iri da suke da juriya akan wasu kwari da cututuka.

Na biyu, idan ganye ya fara nuna alamar cin kwari ko cuta, misali, cenja kala, ka cire shukar daka cikin gonar ka kona ko kuma ka binne ta.

Na uku, kana koran fari da tsintsaye da na’ura mai ihu ko mutum-mutumi.

Na hudu, zaka iya amfani da ruwan bishiyar dogon-yaro da aka matse dan maganin kwari.

Beraye na kwadayin wasu abinci kebabu, kamar hatsi da ya’yan itatutuwa, da gyada da kuma shara. Ka tabbatar da gonar ka a tsaftace take sanan ba inda beraye zasu buya.

Ka tuna cewa, hanyoyin gargajiya irin wadanan sunfi tasiri idan aka samu barkewar cututuka. Saboda haka kana lura da gonar ka dan gano matsaloli da wuri.


 

Talla #8:
Amfanin busarwa

MAI BAYANI:
Me yasa yake da amfani ana busarda masara kafin ajiya? Ga dalilai guda uku masu kyau.

Na farko, danshi na kawo saurin shigar cinkosan cututuka, wanda yake haifar da ribewa, gurbacewa da kuma lalacewar shuka.

Na biyu, cinkoso na haifar da afulotoxin, wanda yake sanya cutar daji ko mutuwa.

Na uku, danshi mai yawa na kara samar da kwari irinsu dodon gona.

Saboda haka, domin samun masara mai ingancin gaske, wanda babu cuta, ko kwayoyin afulotoxin da kwari, toh ka busar da masara ka zuwa kaso 12-13% na danshi kafin ajiya.


 

Acknowledgements

Godiya

Gudunmuwa daka: Doug Ward, Ciyaman din FRI da ya wuce, an kuma yi bitan sa a cikin shekarun da suka wuce da gudunmuwa daka ma’aikatan FRI, da masu gabatar da shirin manoma a yankin sahara Afirka.

Gudunmuwa daka: Vijay Cuddeford, managing editor, Farm Radio International

Mai bita: Stephen Babajide, Malamin gona sana mai bada shawara akan sadarwa, Green Innovation Centre for the Agriculture & Food Sector, Nijeriya, da kuma Mohammed Ubale, Mai bada shawara akan tsarin masara, Green Innovation Project Kaduna, Nijeriya.

Wanan aikin an fasara shi daga tallafin da Ma’aikatar Tarayya ta Hadin Gwiwa Tattalin arziki da Cigaba ta kasar Jamus ta cikin Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit GmbH (GIZ) da kuma abokiya hulda ta “Green Innovation Center for the Agriculture and Food Sector” a Nijeriya.