Shirin Rediyo: Noman dankalin turawa da aikace-aikacen sa bayan girbi

Matslolin da ake fuskanta bayan anyi girbi

Theme pack

Shiri 1: Ingantacen wurin Ajiya

Ingantacen wurin ajiya zai taimaki shukar ka sosai! Wurin ajiya mai kyau yana da wurin shan iska, babu kuma kwari-da cututuka. Wurin ajiya mai kyau yana taimakawa manoma su ajiye amfanin gona tsawon lokaci mai yawa har yakare su daka cunkoson kasuwa da kuma faduwar farashi bayan girbi. A maimakon haka, zasu ajiye su siyar daka bayan bacin farashin yayi sama.

Ka saurari wanan Shiri da Hausa a: https://soundcloud.com/farmradio/irish-potato-radio-spots-1-effective-storage-areas

Shiri 2: Amfanin tantancewa

Tantancewa yana raba dankali masu kyau da wanda suka rube, masu cutuka, ko kuma masu digon baki, da sauran marasa kyau. Ka cire wanda suka rube ko suke dauke da cututuka nesa daka wurin ajiya ka kona.

Shiri 3: Samun sabin kasuwa

Manoma a ko da yaushe na neman kasuwa su sayar da dankalin su. Amma ta ya zaka samu masu sabin siya? Ga abubuwa biyar da zakai amfani dasu ka samu sabin masu siya: Na farko, kayi magana da sauran manoma kasan was uke siyarwa. Na biyu, kayi magana da-ko ka shiga taron ko kungiya hadaka. Na uku, kayi magana da kungiyoyi-kungiyar masu siya’, kungiyar kasuwani, da kungiyoyi masu zaman kansu, kungiyar masu siya dai-dai, kungiyar masu gidan abinci, da dai sauransu. Na hudu, kana kayan ka kasuwani da aka sani. Na biyar, kayi binciken sabin kasuwani ta kiran waya ko tura sakon salula. Ko kasan wata hanya mai kyau da zaka samu sabin kasuwa? Dan Allah ka fada mana!

Shiri 4: Kada ka jima dankalin ka ciwo!

Dankali mai ciwo na nufin faduwa babba! Ka tara dankalin ka mra ciwo a hankali cikin 50-kg buhu domin sifiri a babbar mota. Ka cika buhu saboda dankalin bazai na yawo bas una gogar juna akan titi mara kyau. Ka tabbatar da an loda a mota a hankalin dan gudun ciwo. Dankali masu ciwo na iya saurin kamuwa da cututuka, wanda zai iya yada cututuka zuwa sauran dankalin, ya janyo asara sosai.

Shiri 5: Muhimmancin cire ciyayi

Menene Ciyawa? Ciyawa shuka ce da take girma inda ba’a santa. Ciyayi na dakile girman shuka tana kuma rage albarka gona ta hanyar fadan da shuka akan ruwa, sinadiran kasa da wuri. Suna kuma cinyewa manomi kudi da lokaci. Cire ciyayi na nufin tsige ciyayi dan rage jayaya da shuka da kuma bunkusa albarka gona.

Shiri 6: Amfanin ajiye rekod

Wata rana, na ziyarci wani manomi dashi da matarsa. Gidan su da kewayensa a tsaftace tsaf. Suna da aladu, da kaji masu kyau da kuma lambu.

Muna cikin hira, sai suke fada mun wasu manoma sunfi su samun kudi. Sai suka tambaye ni mai yasa. Kafin na basu amsa, sai nayi musu wasu tambayoyi akan gonar su.

Na tambaye su nawa suke kashe wa wurin cire ciyayi da kuma girbin shukar su. Na tambaye su ya girman albarka amfanin gonarsu ta bara, nawa suka siyar, da kuma yawan kudin da suka samu siyarwa.

Na tambaye su yaushe aladen su zata haifi kananen aladu.

Basu iya bani amsar wanan tambayoyin nan ba. Saboda basu sani ba.

Na ziyarci wani manomin daban a ranar da yamma. A wurin su, komai daban. Sun iya bani amsa tambayoyi na. Idan basu tabbatar ba, sai su kalli inda suka rubuta a kalanda ko bango, ko kuma a kwati da ya kunshi takadu da suka boye a gidansu.

Wanan iyalin na samun kudi sosai fiye da wancen iyali. Hasali ma, wanan iyalin sun fada mun cewa amfanin da ayukan noma na kwarai ya taimaka musu saboda komai samun kudi da yawa a noma.

Sunce noma ne san’ar s, haka kuma kamar yadda mutane dake cikin gari suke sana’a suke ajiye rekod, haka suma suke ajiye wa.

Yanzu…wana manomin a cikin su kake so ka zama?

Shiri 7: Yadda zakai shuka da kuma inda zakai shuka.

Domin bawa shukar ka ta dankalin turawa dama sosai, ka tuna da abubuwa guda uku nan:
1) Kayi shuka inda ruwa ya stane kamar kasa mai duwatsu ko kasa mai laushi.
2) Ka shuka dankalin ka gonar da a cikin shekara daya ko biyu da suka wuce ba a shuka tumatir, ko attaruhu, ko yalo, ko dankalin ba.
3) Kayi huda mai zirfi da takai 30 na sentimeter.

Saurari Shiri din da yaran Hausa a: https://soundcloud.com/farmradio/spot-7-where-and-how-to-plant

Shiri 8: Ka shuka irin ka da yafi ko wane kyau

Domin samun sakamako mai kyau, ka shuka dankalin da fadin su ya kai 25-60 na milimita, suna tsiray 4-6, da kuma nauyi da ya kai gram 40-60ko kuma girman kwan kaza.

Shiri 9: Neman abun shiga

Domin samun albarka da kuma kudin shiga, ka nemo irin ka da kuma yadda zaka kare shukar ka daka majiya mai karfi. Wanan ya hada da wurin diloli na kwarai da kuma Cibiyar Bincike ta kayan gona masu jijiya ta kasa. Zaka iya samo iri da kuma kare kayan gonar ka daka wurin manoma daka wurin manoma da aka aminta da kwazan su. Amfani da ingantatun hanyoyi zai kare ka daka fadawa kan siyan gurbatace, ko na karya, ko kuma karancin inganci.

Shiri 10: Share gona kafin shuka

A lokacin da ka zabi gona da kake so kayi shukar dankali, ya kamata ka share ta. Wanan ya hada da abubuwa biyar: Na farko, ka tatara ragowa shara a wuri daya ka kona dan gudun kasha kasar wurin da wuta. Wanan zai kasha duk wasu kwari dake kawo cututuka a shuke-shuken dake kusa. Haka kuma, ka cire duk wasu duwatsu da wasu makamashi.
Na biyu, ka share gona da hannu ko kuma da maganin ciyayi.
Na uku, kayi huda, idan ya samu, ayi da injinan gona.
Na hudu, buda, idan ya samu, ayi da injinan gona.
Na karshe, kayi tuddai.

Shiri 11: Hanyoyin ban ruwa

Akwai hanyoyin ban ruwa guda uku. Na daya, ban ruwa mai diga shine wanda ake jera tiyo a kasan kunyar shuka a layi. Ana yiwa tiyo din kananonin huda da zai ringa fida ruwa kadan-kadan da kuma a jere. Na biyu, bazawa shine wanda yak e harba ruwa sama, ta inda yake fadowa kan shukar. Na uku shine turo ruwa daka maajiyar ruwa a kyale shi yana gudana akan tuddan.

Shiri 12: Kayi shuka a tsare!

Manoma. Kada ku shuka dankali gaba daya a lokaci daya! Wanan zai kawo cunkoso a kasuwa, ya rage farashin siyarwa, har ya janyo rubewa da kuma asara. A maimakon haka, ka tsagaita shukar ka ta hanyar shuka a lokuta daban daban. Zaka samu farashi mai kyau za kuma ka rage asara.

Shiri 13: Kula da cutar digo

Cutar digo-digo ta dankali na daya daka cikin cututuka dake adabar dankali yana iya kuma kase shukar gaba daya, musamman idan akwai ruwan sama, akwai dumin gari sosai, da kuma karancin zafin rana. Domin kariya daka wanan cutar, ya zamanto a ko da yaushe kana juya shukar dankali da su masara, waken suya da sauran shukoki masu kariya daka cutar duk lokacin da suka samu, kana kuma kula da kamuwar cutar duk bayan kwana biyu bacin shukar ta fito. Cutar na nuna farin gari aka ganyaye.

Shiri 14: Kula da cutar skab

Skab itama cut ace dake adaba dankali. Domin samun kariya daka skab, kana juya shukar dankali da wasu shukokin kamar masara da waken suya, amfani da iri mai kyau, wanda bay a dauke da cuta, ka guji shuka a gona da pH yayi kasa, ka guji jima shuka ciwo wurin cire ciyayi, ko hargitsa kasa, ko girbi. Ka saka ido a kafin girbi da kuma lokacin da ake girbi.

Shiri 15: Cire Ciyayin farko

Ka cire ciyayi lokacin da dankali yake sati 2-3 bayan shuka, ganye ya fara fitowa daka kasa. Me yasa cire ciyayi ke da muhimmanci? Saboda yana rage jayaya da ciyayin suke da shukar ka wurin ruwa, sinadira da kuma fili, yayi da yake samar da albarka sosai.

Shiri 16: Ka kare kanka daka maganin kwari

Maganin kwari anyi sune dan suk kasha kwari, zasu iya cutar dakai kaima idan baka yi a hankali ba. Maganin kwari na shiga jiki ta hanyoyi uku: ana iya shakar su ta fata ko ido, ko baki, ko kuma shakar su ta numfashi su shiga huhun ka. Saboda yana da muhimanci ka saka kayan kariya, kasa tabarau da kuma abun rufe fuska da zai rufe ma hanci da baki.

Shiri 17: Amfani da taki akan dankali

Idan dankali ya fara girma, kayi amfani da takin zamani na NPK 15-15-15. Kayi wanan sati hudu bayan shuka da kuma bayan cire ciyayi na farko. Ka tuna takin zamani na da tsada. Saboda ka auna takin, dan kasan daidai yawan wanda zakai amfani dashi.

Shiri 18: Cire ciyayi na biyu

Ka sake cire ciyayi na biyu sati 5-6 bayan shuka, kafin gayen ya rufe. Kayi a hankali saboda kar ka lalata dankali dake girma.

Shiri 19: Girbi a yanayi da ake rana sosai

Kayi kokari ka guji ruwa ko danshi a lokacin da kake girbin dankali. Duk lokacin da ya samu, kayi girbi a lokacin da ake rana kuma gari da sanyi bayan shukar ta mutu gayen ya bushe. Ka shanya dankali ya bushe na awa biyu, sanan ka raraba kafin ajiya.

Shiri 20: Lalata rubabun dankali

Bayan girbi, ka guji gurbata dankali masu kyau ta hanyar tara sauran rubabun dankali a wuri daya nesa da gona ka kona su.

Saurari wanan sautin da Hausa a: https://soundcloud.com/farmradio/spot-20-destroying-rotten-tubers

Shiri 21: Cire Ciyayi

Ka cire ciyayi sati 2-3 bayan shuka lokacin da tsirai suka fara fitowa daka kasa. Ka sake cire ciyayi na biyu sati 5-6 bayan shuka, kafin gayen ya rufe. Kayi a hankali saboda kar ka jima dankali masu tasowa ciwo.

Shiri 22: Dalilai da zai sa manoma su tantance, jerawa da kuma kunshe dankalin su

Me yasa manoma suke tantance dankali bayan girbi? Saboda a cire mara sa kyau da masu dauke da cututuka.
Me yasa suke jera matsayinsu? Suna jera su a bias tsayin su da ingancin su. Wanan yana raba dankalin da zaa kai kasuwa da wanda za;a ci.

Me yasa manoman dankali ke masa kunshi na musamman? Yin amfani da pakiti da ya dace, mai daukan ido, iska na shiga sosai, kuma an sa masa suna, manoma na dada samun kudin shiga.

Shiri 23: Amfanin hada kai guda ayi talla

Ka duba yiyuwar hada kai domin tallan dankali a cikin rukuni guda? Akwai fa’ida sosai, amma ga guda biyu: Saboda babu yan tsakiya, manoma zasu cikaken kudin da yashigo wurin saida dankali. Haka kuma, idan manoma sun siyar a tare, zasu iya hada kai a saukake, su hana cunkoson kasuwa, su koyi harkar noma da ya dace daka wurin juna. Kano so ka samu Karin bayani? Kayi Magana da manoma da ke siyar da kaya a tare!

Saurari wanan shirin a Hausa a: https://soundcloud.com/farmradio/spot-23-benefits-of-collective-marketing

Shiri 24: Hanyoyin sifiri da suka dace

Sifirin dankali da ajiya sa hanyoyi ne da ake asara bayan girbi sosai. Amma idan kayi da kyau, zai saka a agaba da sauran! Da zara, an gama girbi, a hankali kayi pakitin dankali a 50m kg buhu, ka tabatar kar ka ji musu ciwo. Sanan kayi sifirin zuwa wurin ajiya a cikin babbar mota mai diban kaya. Idan ka bi wanan shawara, zaka samu riba sosai.

Shiri 25: Tazara tsakanin shuka da ya dace

Wadanan sune tazara da ake bada shawara a bayar tsakanin dankalin turawa: Ana so ayi shuka mai zurfi kimanin sentimita 8 zuwa 15, a kuma bar tazara tsakin shukoki kimanin sentimita 30. Domin shuka mai idanu 6 ko 7, a bar tazara sentimita 40. Idan karamar shuka ce mai idanu 2 ko 3, a bar tazara sentimita 20.

Shiri 26: Juya shuka ya zama dole!

Domin gudun taruwa kwari da cututuka, ka na juya shukar dankali da masara da waken suya. Ka kyale gonar babu dankali kamar shekara uku. Kana shuka dankali a gonar a shekara ta hudu.

Saurari wanan shirin a Hausa a: https://soundcloud.com/farmradio/spot-26-crop-rotation-is-a-must

Acknowledgements

Yabo
Gudunmuwa daka: Vijay Cuddeford, Manja tantance ayyuka, Farm Radio International, daka cikin bayanan da aka tattauna a taron tsara shirye-shirye na aikin FRI’s GREGI (GIZ Radio Enabling Green Innovation) a Nijeriya.

Wanan aikin an dauki gudanar dashi ne daka gudumuwar kudi da “Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit GmbH” (GIZ) ya bayar, wanda suke gudanar da cibiyar “Green Innovation” tare da hadin gwiwar AFC Agriculture and Finance Consultants.