Amsoshi tambayoyin da aka fi yi game da rigakafin Korona

Kiwon lafiyalafiya kasa

Backgrounder

 

Teburin abubawan da ke ciki

Sananan Bayanai 3

Wana irin rigakafin cutur Korona ne muke dasu a Afrika?. 3

Menene fa’idodin yin allurar rigakafin Korona?. 4

Ya ya rigakafin cutar Korona ke aiki?. 4

Ta yaya aka samar da rigakafin cutar Korona da sauri haka?. 5

Yaushe zanje ayi min rigakafin cutar Korona?. 5

Ko wadanda sukayi rigakafin suna samun kariya akan dukan nau’oin cutar Korona, wanda ya kunshi SARS da MERS?. 6

Shin wadanda akayi wa rigakafin suna samun kariya akan duk nau’oin Korona?. 6

Zaka iya kamuwa da cutar Korona bayan anyi ma rigakafi?. 6

Shin zan guji yin allurar don kada in sami illa daga karbar rigakafin? Shin akwai wasu illolin da ke daɗewa?. 6

Ko rigakafin cutar Korona na sa gudar jini?. 7

Toh ina mutane da suka mutu bayan anyi musu allurar rigakafin?. 7

Ko rigakafin cutar Korona na iya sa mun cutar Korona?. 7

Wana rigakafin Korona ya kamata in nema?. 7

Idan na taba yin Korona a baya, zan iya zuwa in karbi rigakafin Korona?. 8

Ko za’a iya yiwa yara da matasa rigakafin cutar Korona?. 8

Ko akwai bukatar in cigaba da sa takunkumin fuska, yin amfani da hanyoyin kariya, da daukan wasu mataken kariya bayan na karbi allurar rigakafin Korona?. 8

Shin ba komai insha magungunan antibiyotic bayan na karbi rigakafin Korona?. 9

Shin ba komai idan na sha giya bayan anyi mun allurar rigakafin Korona?. 9

Menene banbancin tsakani kariya da zaka samu bayan ka warke daka cutar Korona da kuma kariya da zaka samu daka allurar rigakafin Korona?. 9

Har zuwa tsawon wana lokaci ne wadanda aka yiwa rigakafi suke da kariya akan Korona?. 10

Ko rigakafin Korona na iya sawa a samu tabbaci a sakamakon gwajin PCR ko gwajin antigen?. 10

Ina da ciwon suga. Ta yaya Korona zata shafe ni ta daban?. 10

Ina da ciwon kansa ko kuma nayi ciwon a baya. Za’a iya min allurar rigakafin Korona cikin lafiya?. 11

Na kamu da cutar kanjamau. Ko za’a iya mun rigakafin Korona ba matsala?. 11

Na kamu da cutar kanjamau. Ko akwai wasu matakai na musamman da zan dauka dan kariya daka cutar Korona?. 11

Ko yin allurar rigakafin Gamelaya (Sputnik V) na iya sa mutum ya kamu da cutar HIV?. 11

Ina da matsalar tafiya, saboda haka yana mun wahala in fito daka gida Za’a iya mun rigakafi a gida?. 12

Ko akwai wani babanci tsakanin maza da mata akan ilar Korona?. 12

Annobar Korona tana da matukar tada hankali. Zan iya samun taimako?. 12

Kula da lafiya yayin jima’i da haihuwa da kuma rigakafin Korona. 12

Zan iya karbar rigakafin Korona idan ina da ciki?. 12

Ko rigakafin Korona zai sani rashin haihuwa ko rashin karfin gaba?. 12

Zan iya karbar allurar rigakafin Korona idan ina shayarwa?. 12

Shin yana da kyau mata masu jinin alada su karbi rigakfin Korona?. 13

Adadin allurar 13

Ko adadin alluar guda biyu zai fi bani kariya akan guda daya?. 13

Shin ba laifi idan mutum ya hada rigakafi daban-daban—misali, ka karbi guda na rigakfin kamfani daya ka karbi guda na wani kamfanin daban?. 13

Menene “allurar karfafawa” ko “harbin karfafawa” ta rigakafin Korona?. 13

Shin mutane dake matukar cikin hadarin kamuwa da Korona na bukatar Karin allurar rigakafin?. 13

Acknowledgements. 14

Sananan Bayanai
Wana irin rigakafin cutur Korona ne muke dasu a Afrika?
Akwai rigakafin cutar Korona da yawa a Afrika. A kalla har zuwa watan Afirilu na 2022, akwai rigakafin da suka hada da:

 • Bharat Biotech (Covaxin)
 • Gamelaya (Sputnik V)
 • Janssen (Johnson & Johnson)
 • Moderna
 • Oxford/AstraZeneca
 • Pfizer
 • Sinopharm
 • Sinovac

Samuwar takamaiman alluran rigakafi ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa. Duk waɗannan alluran rigakafin an gwada su sosai kafin a amince da su don amfani kuma an tabbatar da suna da aminci da inganci wajen kariya daka rashin lafiya mai tsanani, kwanciya a asibiti, da kuma mutuwa daga cutar Korona.

Menene fa’idodin yin allurar rigakafin Korona?

Yin allurar rigakafin zai iya ceton rayuwar ku. Allurar rigakafin Korona suna ba da kariya mai ƙarfi daga rashin lafiya mai tsanani, kwanciya a asibiti, da kuma mutuwa sakamakon ƙwayar cutar. Yin allurar zai rage damar da za ku iya yada kwayar cutar ga wasu, wanda ke nufin cewa matsayar da kuka dauka na yin rigakafin na bada kariya daka duk wanda ya ke kusa da ku.

Ya ya rigakafin cutar Korona ke aiki?

Domin sanin yadda rigakafin cutar Korona ke aiki, yana da muhimanci mu san wadanan kalmomi guda uku: pathogen, antibody, da kuma antigen.

Pathogen wasu kananen halittu ne da suke haifar da cututuka. Kwayar halitar da take haifar da cutar Korona itama pathogen ce.

Tsarin garkuwar jikin ɗan adam yana amsa ƙwayoyin cuta ta hanyar samar da ƙwayoyin rigakafi. Kwayoyin rigakafi suna taimaka wa jikin dan adam ya gano da kuma kashe ƙwayoyin cuta.

Taka memen bangaren kwayoyin cutar da ke sa jikin dan adam ya samar da ƙwayoyin rigakafi ana kiransa antigen. Lokacin da jikin ɗan adam ya gamu da antigen a karon farko, tsarin rigakafi garkuwar jikin dan adam na samar da ƙwayoyin rigakafi waɗanda suka keɓance ga wannan antigen.

Rigakafin cutar Korona kala biyu ne. Wanda aka fi sani (kuma kamfanonin Bharat Biotech (Covaxin), Gamelaya (Sputnik V), Janssen (Johnson & Johnson), Oxford/AstraZeneca, Sinopharm, and Sinovac ke wakilta) sun kunshi rauna-nan ko kuma bari mara amfani na antigen din Korona. Idan mutum ya karbi irin wanan rigakafin, yana haifar da kariya ga jiki akan raunanan ko kuma bari mara amfani na antigen. Wanan kariya da jikin dan adam ya taso dashi na shirya jikin mutum yayi fada da cutar Korona.

Shi dayan rigakafin (da ake kira mRNA rigakafi kuma kamfanonin Pfizer da Moderna ke wakilta) basu kunshi Korona antigen ba. A maimakon haka, sun kunshi bayanai na kwayoyin halitta antigen. Sanda mutum ya karbi rigakafin mRNA, jikin mutum na amfani da wanan bayanan dan samar da kariya ga cutar Korona.

Koma wana irin rigakafin ka karba, rigakafin cutar Korona bazai saka ka kamu da cutar Korona ba. Hasali ma, zai sa dai tsarin garkuwa jikin dan adam ya fara mayar da martini kamar yana fada da ainihin kwayoyin cutar Korona. Suna yin haka ta hanyar haifar da tsarin rigakafin jikin dan adam yana kirkira kwayoyin rigakafi domin kariya daka kwayoyin cutar.

Ta yaya aka samar da rigakafin cutar Korona da sauri haka?

A da, ana daukar shekaru masu yawa kafin a samar da rigakafi a kuma raba wa mutanen gari. Amma, rigakafin cutar Korona an samar dashi a kasa da shekara guda bayan samuwar kwayar cutar. Akwai dalilai da yawa da yasa haka.

Shekaru aru-aru da ake kir-kira rigakafi, kungiyoyin bincike da hukumomin kiwon lafiya sun gano cewa samar da rigakafi na daukar lokaci sosai, domin haka ne suka kara himma da kuma saurin cinma maufarsu. Haka ma, masu bincike sun dade suna nazari akan kwayar cutar korona shekaru da yawa dan haka sun dau darasi akan cututukan korona biyu da suka shude shekaru 20 da suka wuce: SARS da MERS. Bayan an gano kwayar cutar da ke samar da Korona, masana kimiya suka hada cikaken bayani game da kwayar halitar a cikin sati biyu. Wanan ya taimaka suka gano ainihin rigakafin da zai aiki akan Korona.

Haka ma, an kula kawance a duk duniya domin magance annobar Korona. Masana kimiya da kungiyoyin a kasashe da dama sunyi musayar bayanai sun kuma tattauna akan hanyoyin da suka fi dacewa a yaki cutar.

A duniya baki daya, talafin kudin rigakafin Korona sun zo daka wurare daban-daban, harda kungiyoyi na masu zaman kansu, gwamnatoci, mutane, da kuma kamfanonin magunguna.

A baya, a na daukar shekaru da yawa kafin ayi gwajin rigakafi a asibitoci. Shirya gwaji, samo masu agaji yan sakai, sanan kamala matakai daban-daban guda uku na gwajin asibiti da ake bukata domin tabatar da aminci da ingancin rigakafin shine mafi tsayi wurin samar da rigakafin. Amma akan rigakafin Korona, an gudanar da matakan gwaji daban-daban a lokuta da suke shafe juna, kuma hukumomin da suke bada amincewar su ga rigakafi sun yi nazarin bayanan gwaji akai-akai kuma sun yanke shawarar cewa alluran suna da aminci da inganci.

Haka zalika, an ba kamfanoni da yawa kudade da suka ba su damar fara kera magungunan kafin a amince da su gaba daya. Ga waɗancan allurar rigakafin da aka amince da su daga baya, wannan ya taimaka ta hanyar rage lokacin da aka ɗauka don samar da allurar da kuma kai su ga jama’a watanni kafin lokacin da ake tsammani.

Yana da mahimmanci a lura cewa allurar Korona ta wuce gwaje-gwajen kimiyya da yawa, godiya ga dubun dubatar mutanen da suka gwada su. Alurar rigakafin Korona da aka amince ayi amfani da su sun cika ka’idojin da hukumomin kiwon lafiya na gwamnati suka gindaya a cikin kasashen duniya.

Ayyukan kimiyya da ka’idoji akan allurar har yanzu ba su tsaya ba. Duk wanda ya karɓi allurar rigakafin zai iya bayar da labarin yadda abun ya kaya, da yadda yaji da ya karba ta haka ya ba da gudummawa ga kyakkyawar fahimtar yadda rigakafin ke aiki.

Yaushe zanje ayi min rigakafin cutar Korona?

Ya dace kuje kuyi rigakafin Korona da zarar kun samu dama. Ka’idoji game da lokutan yin rigakafin ya ban-banta kasahe zuwa kasashe. Domin karin bayani, ka tuntubi ma’aikatan lafiya na unguwa ku.

Ko wadanda sukayi rigakafin suna samun kariya akan dukan nau’oin cutar Korona, wanda ya kunshi SARS da MERS?

Shi rigakafin cutar Korona an tsara shine domin ya kara wa dan adam kariya daka cutar Korona kadai, banda sauran cututkan corona da suka hada da SARS da MERS.

Korona nau’i guda ne na cutukan corona. Cututukan corona wani rukuni ne na kwayoyin cuta masu alaka wanda ke samar da cututuka a tsintsaye da dabbobi da ya hada da mutane. Misalan cututka da kwayar cutar Korona ke samar wa sun hada da mura, (wanda kuma wasu nau’ikan ƙwayoyin cuta ne ke haifar da su), da ƙwayoyin cuta da ke da illa ga lafiyar ɗan adam kamar waɗanda ke haifar da SARS, MERS, da Korona.

Shin wadanda akayi wa rigakafin suna samun kariya akan duk nau’oin Korona?

Duk ƙwayoyin cuta suna canzawa ko yaushe ta hanyar da ake kira maye gurbi, kuma sabbin nau’oin cutar suna fitowa akai-akai. Kadan daga cikin nau’oin Korona, kamar su delta da omicron, sun fi saurin kamuwa akan cutar ta asali. Sauran nau’oin na iya haifar da mummunan tasirin akan lafiyar mutum fiye da asalin kwayar cutar Korona.

Tun daga watan Afirilu na 2022, duk allurar rigakafin da aka amince da amfani da su suna da tasiri sosai wajen hana rashin lafiya mai tsanani, kwanciyar asibiti, da mutuwa daga duk nau’oin Korona—wanda suka hada da delta da omicron.

Alurar rigakafin Korona ba su da tasiri wajen hana watsa nau’in delta musamman nau’in omicron. Amma idan kun kamu da cutar bayan an yi muku alurar riga kafi, alamomi cutar na iya zuwa da sauki akan wadanda ba a yi wa allurar ba, sanan yiyuwar kwantar da kai a asibiti ko kuma mutuwa ta dalilin cutar kadan ce.

Zaka iya kamuwa da cutar Korona bayan anyi ma rigakafi?

Yin alurar rigakafin Korona daka amince aka tabatar dashi na ba da babban matakin kariya daga rashin lafiya mai tsanani, kwanciyar asibiti, da mutuwa. Alurar rigakafi na rage yuwuwar kamuwa da kuma watsa cutar Korona ga wasu.

Zai iya yiyuwa wanda akayiwa rigakafin ya kamu da rashin lafiyar Korona ya kuma ba wa wasu mutane cutar. Wanan haka yake musamman game da nau’in omicron mai saurin kamuwa.

Amma idan kun kamu da cutar bayan an yi muku alurar riga kafi, alamomi cutar na iya zuwa da sauki akan wadanda ba a yi wa allurar ba, sanan yiyuwar kwantar da kai a asibiti ko kuma mutuwa ta dalilin cutar kadan ce akan wadanda ba’a yiwa ba.

Shin zan guji yin allurar don kada in sami illa daga karbar rigakafin? Shin akwai wasu illolin da ke daɗewa?

A’a, kada ku guje wa yin allurar rigakafi don guje wa illa. Kuma a’a, illar rigakafin ba sa daɗewa.

Yin alurar rigakafin Korona daka amince aka tabatar dashi na ba da babban matakin kariya daga rashin lafiya mai tsanani, kwanciyar asibiti, da mutuwa. Wanan kariya ta hada da duka nau’in cutar, harda wace tafi saurin yaduwa wato nau’in delta da omicron.

Ilolin da akan iya samu yawanci suna faruwa a cikin ƴan kwanakin farko na samun maganin Korona. Tun lokacin da aka fara shirin rigakafin farko a cikin Disamba 2020, kusan biliyan 11 na allurorin rigakafin Korona akayi a duniya ba tare da wani illa na dogon lokaci ba.

Illolin allurar rigakafi kusan ko yaushe suna da sauƙi kuma yawanci sun haɗa da alamomi kamar haka: ciwon hannu, zazzabi mara tsanani, gajiya, ciwon kai, da ciwon jiki ko ciwon gwiwa. Waɗannan alamomi na nuna cewa jikin ku yana gina kariya daga Korona. Duk da haka, wasu mutane ba sa fuskantar illa bayan alurar rigakafi, kuma suna da matakan kariya iri ɗaya.

Haɗarin kamuwa da Korona ya fi girma kuma ya fi haɗari akan illolin da zak smau daga karɓar ingantaccen rigakafin.

Ko rigakafin cutar Korona na sa gudar jini?

An sami wasu rahotanni guda uku zuwa 30 bayan allurar rigakafin AstraZeneca da Janssen (Johnson & Johnson). Waɗannan lamuran suna da tsanani amma ba kasafai ake samu ba.

A zahiri, bincike ya nuna cewa kuna iya samun gudan jini daga kamuwa da Korona fiye da yadda zaka samu daka kowace irin alurar rigakafin Korona.

Toh ina mutane da suka mutu bayan anyi musu allurar rigakafin?

An gwada allurar rigakafin Korona don aminci, kuma suna da tasiri wajen hana rashin lafiya mai tsanani, asibiti, da mutuwa. Rahotanni na munanan abubuwan da suka faru bayan alurar rigakafi ba su da yawa. Kawai saboda wani ya sami wani abu mara kyau bayan an yi masa alurar rigakafi baya nufin cewa maganin ya haifar da matsalar ba. Maimakon haka, matsalar na iya tasowa daga yanayin lafiyar mutum tun farko.
Ko rigakafin cutar Korona na iya sa mun cutar Korona?

Ba rigakafi daya da take dauke da kwayar cutar Korona. Dan haka, babu yanda rigakafin Korona zai sa maka cutar Korona.

Wana rigakafin Korona ya kamata in nema?

Dukkanin allurar rigakafin Korona da aka amince da su suna da matukar tasiri wajen hana rashin lafiya mai tsanani, kwanciya a asibiti, da mutuwa daga Korona. Hukumomin kiwon lafiya suna shawartar mutane da su karbi maganin da aka fara ba su kuma a yi musu rigakafin da wuri-wuri.

Kar kayi jinkirin karbar rigakafin sai dai in likita ne ya baka shawarar hakan, domin jinkiri na kara saka a cikin hadarin kamuwa da cutar Korona.

Yin rigakafi zai ceci rayuwar ka. Rigakafin Korona mafi kyau shine wanda zaka samu da wuri.

Idan na taba yin Korona a baya, zan iya zuwa in karbi rigakafin Korona?

Eh, ana bawa mutane shawara da suka taba kamuwa da Korona a baya da su karbi cikaken adadin rigakafin—cikaken lambar allurar da ya dace. Mutane da suka kamu da Korona suka warke suna samun wani garkuwa akan Korona, amma zaiyi wuya a san iya kwanakin da zakai da wanan kariyar.

Alurar rigakafi shine hanya mafi aminci kuma mafi inganci don rigakafin rashin lafiya mai tsanani, kwanciyar asibiti, da mutuwa ta dalilin Korona.

Don haka ne Hukumar Lafiya ta dinkin Duniya da sauran hukumomin lafiya ke ba mutane shawarar da su yi cikakken rigakafi da zarar sun samu dama.

Za a iya yi muku allurar da zaran ba ku da wasu alamomin kamuwa da Korona.

Ko za’a iya yiwa yara da matasa rigakafin cutar Korona?

Ana ci gaba da gwajin rigakafin Korona ga yara da matasa. Har zuwa yanzu, kasashe da yawa suna ba da rigakafin Korona ga yara da matasa, duk da dai mafi ƙarancin shekarun rigakafin ya bambanta tsakanin ƙasashe.

Yaran da ba sa fama da wata mumunan rashin lafiya yawanci ba sa kamuwa da tsananin rashin lafiya in sun kamu da Korona kamar manya, don haka babban makasudin yi wa yara rigakafin shine a rage yaɗuwa ta.

Amma rigakafin Korona da alama ba su da tasiri wajen rage yaduwa nau’in omicron. Don haka, yin allurar rigakafi na da kyau, amma hanya mafi kyau don kare yara ita ce kowa ya ci gaba da sanya takunkumin fuska da ke rufe hanci, baki, da haba; kiyaye aƙalla tazarar mita ɗaya daga wasu; yin tari da atishawa acikin gwiwar hannu; da kuma wanke hannaye akai-akai da ruwa da sabulu.

Ya kamata iyaye da masu kulawa da yara su bi ƙa’idodin da ƙasa ta gindaya game da yaran da ke zaune a gida basa makaranta saboda rashin lafiya. Hakanan yakamata su bi ƙa’idodin ƙasa game da yiwa ‘ya’yansu gwajin Korona a lokacin da suka fara nuna alamomin cutar da kuma inda akwai wurin gwaje-gwaje.

Ko akwai bukatar in cigaba da sa takunkumin fuska, yin amfani da hanyoyin kariya, da daukan wasu mataken kariya bayan na karbi allurar rigakafin Korona?

Eh, zaku cigaba. Alurar rigakafin Korona suna ba da kariya mai kyau daga tsananin rashin lafiya, kwanciyar asibiti, da mutuwa. Hakanan suna rage kamuwa da yaduwa kwayar cutar, duk da dai ba su da tasiri wajen hana watsa nau’in omicron. Saboda wannan dalilai, kuma saboda mutane da yawa ba su riga sun yi cikakken alurar rigakafi ba, yana da mahimmanci a ci gaba da amfani da wasu hanyoyin kare kai da sauran su.

Domin kare kai da sauran mutane, wadanda suka karbi rigakafi zasu cigaba da:

 • Sanya takunkumin fuska da zai rufe musu baki, hanci da haba,
 • Su bar akalla mita daya daka sauran mutane,
 • Suna yin tari da atishawa a cikin gwiwar hannu, kuma
 • Wanke hanaye a ko da yaushe da ruwa da sabulu.

Wadanan matakan na da muhimanci sosai a rufafen guri mai tarun mutane da kuma karancin hanyoyin shan iska.

Takunkumin fuska na asibiti mai inganci, sun fi tasiri fiye da takunkumin yadi da za a wanke a sake amfani da shi wajen kariya daga kamuwa da cuta da hana ci gaba da yaduwar Korona. Dole ne takunkumin fuska ya yi daidai da kumatu da hanci da kuma kan haba don kariya daga kamuwa da cuta da kuma hana yada cutar ga wasu.

Idan baka da damar samun takunkumin fuska irin na asibiti, ka cigaba da amfani da na yadi da zai rufe ma hanci, baki da haba. Sanya yadi yafi muhimanci akan rashin sa komai.

Ana bun shawarwari da ka’idojin daga jami’an lafiya na unguwa.

Domin Karin bayani akan matakan kariya, ka karanta Muhiman bayanai akan Korona dan masu gabatarwa a: http://scripts.farmradio.fm/radio-resource-packs/covid-19-resources/key-information-covid-19-broadcasters/

Shin ba komai insha magungunan antibiyotic bayan na karbi rigakafin Korona?

Idan ƙwararren malamin lafiya ya rubuta maka maganin antbiyotic kafin ko bayan alurar rigakafi, ya kamata ka ɗauki cikakken kwas da ya baka. Idan kana da zazzabi, bai kamata ka yi allurar rigakafin Korona ba har sai ka ji sauki.

Shin ba komai idan na sha giya bayan anyi mun allurar rigakafin Korona?

Babu wata shaida cewa ci ko shan wani abu, hade da giya, kafin ko bayan yin rigakafin zai shafi aminci ko ingancin rigakafin Korona. Koyaya, shan giya na iya dagula ƙananan illolin da za ku iya fuskanta bayan allurar rigakafi, kamar ciwon kai da gajiya. Don haka, masana kiwon lafiya sun ba da shawarar cewa a guji shan giya har sai duk wani illar da ke tattare da rigakafin ya wuce.

Menene banbancin tsakani kariya da zaka samu bayan ka warke daka cutar Korona da kuma kariya da zaka samu daka allurar rigakafin Korona?

Kariyar da mutane ke samu bayan farfadowa daga Korona na iya zama mai karfi ko mai rauni. Karfi da tsawon lokacin rigakafi bayan murmurewa ya bambanta daga mutum zuwa mutum, domin haka samun tabacin dadewar kariya na da wahala akan na alluraryana mai da shi ƙasa da tsinkaya fiye da rigakafin da aka samu daga allurar.

Korona cuta ce mai barazana ga rayuwa tare da illoli kala-kala na dogon lokaci, kuma an yiwa biliyoyin mutane allurar rigakafin cutar Korona da aka amince da su. Don haka ya fi aminci a yi alurar riga kafi fiye da haɗarin samun Korona.

Kayi allurar rigakafi da zarar ka samu dama sanan kayi duk abun da ya kamata don kare kanka da sauran mutane.

Har zuwa tsawon wana lokaci ne wadanda aka yiwa rigakafi suke da kariya akan Korona?

Binciken kwana nan ya nuna cewa yawancin mutanen da aka yi wa allurar suna da kariya mai ƙarfi daga rashin lafiya mai tsanani, kwanciyar asibiti, da mutuwa daga Korona na tsakanin watanni uku zuwa takwas bayan samun cikakkiyar rigakafin, ya danganta da wane maganin da suka samu.

Hakanan yana da mahimmanci a lura cewa kashi na farko na maganin allurar rigakafi na cikin biyu yana ba da ƙarancin kariya fiye da karɓar alluran guda biyu.

Ko rigakafin Korona na iya sawa a samu tabbaci a sakamakon gwajin PCR ko gwajin antigen?

A’a, maganin Korona ba zai haifar da kyakkyawan sakamako akan ɗayan waɗannan gwaje-gwajen ba. Saboda shi gwajin yana duba samuwar ainihin ƙwayoyin cutar Korona a jikin mutum ne, ba wai ko mutum ya samu garkuwa akan cutar Korona ba.

Ina da ciwon suga. Ta yaya Korona zata shafe ni ta daban?

Nazarin kwanan nan sun nuna cewa mutanen da ke da ciwon sukari sun fi nuna alamomi mafi tsanani na ciwon Korona kuma suna iya mutuwa saboda Korona fiye da waɗanda ba su da ciwon sukari. Dalilin haka shine, saboda ciwon sukari yana lalata tsarin garkuwar jiki, haka kuma saboda yawancin masu ciwon suga na fama da wasu matsalolin lafiya kamar hawan jini da kiba. Waɗannan abubawan na sa garkuwar jikin dan adam ya sha wahala yaƙar Korona.

Don haka, yana da mahimmanci ga masu ciwon sukari su rage haɗarin kamuwa da Korona ta hanyar yin allurar rigakafi da ci gaba da yin taka tsuntsun.

Baya ga yin allurar rigakafin Korona, mutanen da ke da ciwon sukari ya kamata su ci gaba da:

 • Sanya takunkumin fuska da zai rufe musu baki, hanci da haba,
 • Su bar akalla mita daya daka sauran mutane,
 • Suna yin tari da atishawa a cikin gwiwar hannu, kuma
 • Wanke hanaye a ko da yaushe da ruwa da sabulu.

Waɗannan matakan suna da mahimmanci musamman a cikin rufafen wuri, da yake da cunkoson mutane, ko wuraren da ba su kofofin shan iska.

In ba haka ba, mutanen da ke fama da ciwon sukari ya kamata su ci gaba da sarrafa abincinsu da salon rayuwarsu kamar yadda suka tattauna da likito cin su ko hukumomin lafiya na gida. Wannan ya haɗa da amfani da insulin na yau da kullun da sauran magungunan da aka rubuta kamar yadda ake buƙata.

Ina da ciwon kansa ko kuma nayi ciwon a baya. Za’a iya min allurar rigakafin Korona cikin lafiya?

Wasu mutanen da ke da ciwon kansa ko tarihin ciwon na iya yin allurar lafiya cikin aminci. Tambayar ko wanda ke da tarihin ciwon kasa za a iya yi masa allurar rigakafi ya dogara ne akan wace irin rigakafi ce da kuma irin shi ciwon kansa, ko mutum din na karbar magungunan ciwon kansa, da kuma tasirin garkuwa jikinsa.

Idan kana da ciwon kansa ko kuma tarihin ciwon a baya, kuyi magana da likitan ku ko wani mai ba da lafiya na gida kafin samun kowane nau’in rigakafin, gami da rigakafin Korona.

Na kamu da cutar kanjamau. Ko za’a iya mun rigakafin Korona ba matsala?

Yawancin binciken da akai da suka auna aminci da ingancin rigakafin Korona sun haɗa da ƙaramin adadin mutanen da ke dauke da HIV. Waɗannan binciken sun nuna cewa allurar rigakafin Korona da Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da su ba su da wata matsala ga mutanen da ke ɗauke da HIV.

Babu allurar rigakafi daya da aka amince don amfani da su ke ɗauke da kwayar cutar da ke haifar da Korona. Don haka, alluran rigakafin suna da aminci ga mutanen da ke fama da cutar rangwamamen garkuwar jiki, kamar mutanen da ke dauke da HIV.

Alurar rigakafin Korona ba su da wata matsala da magungunan rigakafin cutar kanjamau. Mutanen da ke dauke da kwayar cutar HIV ya kamata su ci gaba da shan magungunan rigakafin cutar bayan an yi musu alluran rigakafi da kuma bin shawarwarin kwararrun malaman kiwon lafiya.

Na kamu da cutar kanjamau. Ko akwai wasu matakai na musamman da zan dauka dan kariya daka cutar Korona?

Gaskia ne masu dauke da HIV sun fi zama cikin hadarin kamuwa da rashin lafiya mai tsanani daka cutar Korona. Dan haka, yana da muhimanci masu dauke da cutar HIV, kamar duk sauran mutane, su cigaba da kula da wadanan kaidojin kare kai:

 • Sanya takunkumin fuska da zai rufe musu baki, hanci da haba,
 • Su bar akalla mita daya daka sauran mutane,
 • Suna yin tari da atishawa a cikin gwiwar hannu, kuma
 • Wanke hanaye a ko da yaushe da ruwa da sabulu.

A lokacin annobar Korona, mutane masu dauke da HIV su cigaba da shan magungunan su kamar yadda maaikatan lafiya suka shawurta.

Ko yin allurar rigakafin Gamelaya (Sputnik V) na iya sa mutum ya kamu da cutar HIV?

Aah. Ba yanda za’ai mutum ya kamu da cutar HIV daka rigakafin cutar Korona.

Amma, har izuwa watan Afirilu na 2022, kasar Afirika ta Kudu basu amince da rigakafin Gamelaya (Sputnik V) dan amfani, saboda wasu bincike sun bayana cewa zai iya kara hadarin daukar cutar HIV. Masana kimiya na cigaba da bincike akan wanan.

Ina da matsalar tafiya, saboda haka yana mun wahala in fito daka gida Za’a iya mun rigakafi a gida?

Ko wace kasa tana da nata tsarin na yada mutane za’ai musu rigakafi. Domin Karin bayani akan yadda ake rigakfi a yankin ku, ka tuntubi maaikatan lafiya na kusa da kai.

Ko akwai wani babanci tsakanin maza da mata akan ilar Korona?

Masana kimiya basu gano wani banbanci ba tsakanin maza da mata da suka kamu cutar Korona. Amma yana da muhimanci a lura cewa cutar Korona tana da matukar illa akan lafiyar maza da mata, yara maza da yara mata. Kowa yana cikin hadarin kamuwa da ita, ko kamuwa da rashin lafiya mai tsanani, ko kwanciya a asibiti ko kuma mutuwa daka cutar.

Annobar Korona tana da matukar tada hankali. Zan iya samun taimako?

Annobar Korona ta kasance lokaci mai matukar damuwa da tashin hankali. Idan kanajin damuwa, ko dimuwa, ko takura, ko kuma dai ba dai-dai ba, ka nemi maaikatan lafiya na kusa da kai da sanin wani irin taimako zaka samu. Taimakon lafiya na kwakwalwa ya banbanta a ciki da wajen kasashe.

Kula da lafiya yayin jima’i da haihuwa da kuma rigakafin Korona

Zan iya karbar rigakafin Korona idan ina da ciki?

Eh, zaka iya karbar rigakafin Korona ko kina da ciki. Masana kimiya suna cigaba da bincike akan lafiya mata masu ciki da ingancin rigakafin Korona akan su, ammahar yanzu basu gano komai da zai nuna matsala ba.

Yana muhimanci masu ciki su karbi rigakafi saboda, a lokacin da suke dauke da ciki, suna cikin hadarin kamuwa da rashin lafiya mai tsanani daka cutar Korona. Suna kuma cikin hadarin haihuwar yaro lokaci bai kai ba ko kuma samun matsala a yayin haihuwa a dalilin kamuwa da cutar Korona yayin da suke dauke da ciki. Yin rigakafi Korona hanya ce mafi sauki da aka tabatar mata masu ciki zai rage muss hadarorin kamuwa da cutar.

Ko rigakafin Korona zai sani rashin haihuwa ko rashin karfin gaba?

Aah, rigakafin Korona baya kawo rashin lafiya ko rashin karfin gaba. Babu wani shaida da yake nuna cewa Korona na kawo rashin lafiya ka rashin karfin gaba ga mata ko maza.

Zan iya karbar allurar rigakafin Korona idan ina shayarwa?

Eh, zaki iya karbar rigakafin Korona ko kina shayarwa. Babu daya daka cikin rigakafin da aka amince ayi amfani dashi ke dauke da kwayar cutar Korona. Wanan yana nufin ba wani hadarin mata masu shayarwa su bawa yayan su cutar Korona ta hanyar shayarwa. Hasali ma, akwai yiyiwa jarirarn su karu da kariya iyayen su ke dauke da ita cikin rigakfin. Wanan zai taimaka wurin bada kariya ga jarirai daga Korona.

Shin yana da kyau mata masu jinin alada su karbi rigakfin Korona?

Eh, babu wata mastala mata masu jinin alada su karbi rigakafin cutar Korona. Idan mace tana jin alada a ranar da zata karbi allurar rigakafin, taje ta karba babu wani abu.

Jinin alada ba dalili bane na jinkirta karbar rigakafin Korona.

Adadin allurar

Ko adadin alluar guda biyu zai fi bani kariya akan guda daya?

Yawancin rigakfin Korona na bukata adadin allura guda biyu a tsakanin wasu satutuka, duk da dai rigakafin Janssen (Johnson & Johnson) na bukatar guda daya ne kawai.

Karbar adadin allurar guda daya na bada karancin kariya akan kamuwa da cutar da kuma rashin lafiya mai tsanani.

Mutanen da suka yi cikakken alurar rigakafi daga Korona zasu iya yin rashin lafiya sakamakon Korona har ma su yada ta ga wasu. Amma yin allurar rigakafin yana rage haɗarin faruwan haka.

Mutanen da suka sami cikakken tsarin rigakafin ba su da cikakkiyar kariya har sai makonni 2-4 bayan rigakafin su na ƙarshe. A wannan lokacin, jikinsu yana ƙirƙirar ƙwayoyin rigakafin da ake buƙata don yaƙar Korona.

Shin ba laifi idan mutum ya hada rigakafi daban-daban—misali, ka karbi guda na rigakfin kamfani daya ka karbi guda na wani kamfanin daban?

Masana kimiya na nazari akan wanan lamarin ko yana da inganci hada rigakafin Korona na kamfani daban-daban. Sharuda akan wanan tambayar ya banbanta kasashe zuwa kasashe. Kana bin shawarwarin maaikatan lafiya don Karin bayani a ko da yaushe.

Menene “allurar karfafawa” ko “harbin karfafawa” ta rigakafin Korona?

Cikakken tsarin rigakafin cutar Korona yana nufin samun adadin alluran rigakafin da ake buƙata don samun cikakkiyar kariya daga ƙwayar cuta. Ga mafi yawan alluran rigakafi, kamar AstraZeneca da Moderna, cikakken tsarin rigakafin allurai biyu ne. Ga sauran alluran rigakafi, kamar rigakafin Janssen (Johnson & Johnson), cikakken tsarin rigakafin kashi ɗaya ne kawai.

“Allurar karfafawa” ko “harbin karfafawa” rigakafi ne na Korona wanda ya wuce cikaken adadin alluran. Saboda kariyar da rigakafin Korona ke bayarwa ba ya dauwama, wasu kasashen suna bawa yan kasar su daman karbar harbin karfafawa domin ya taimaka ya kara musu kariya akan kwayar cutar.

Shin mutane dake matukar cikin hadarin kamuwa da Korona na bukatar Karin allurar rigakafin?

Mutane da suke cikin hadarin Korona, hade da wanda suke da raunanan garkuwan jiki, basa iya samun kariya cikakiya bayan sun karbi iya adadin allurar rigakafin. Saboda haka, zasu iya neman karin allurar dan kara samun kariya.

Wanan karin yana da banbanci da allurar karfafawa. Ana kalon shi a matsayin cikon adadin rigakafin ga mutanen da baza iya gina cikakiyar kariya ba bayan anyi musu guda daya ko biyu. Karin allurar na taimaka musu su gina cikakiyar kariya akan cutar Korona.

Acknowledgements

Contributed by: Vijay Cuddeford, Managing Editor, Farm Radio International and Hannah Tellier, Resources Coordinator, Farm Radio International

This resource was supported with the aid of a grant from the German Federal Ministry of Economic Cooperation and Development through Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit GmbH (GIZ) and its project “Green Innovation Center for the Agriculture and Food Sector” in Nigeria.

This resource was updated and translated thanks to funding by the Government of Canada through Global Affairs Canada as part of the Life-saving Public Health and Vaccine Communication at Scale in sub-Saharan Africa (or VACS) project.