Dabarun manoma domin dadaito da sauyin yanayi a kasar Nijer

Dumama YanayiMuhali da dumama yanayi

Lura ga mai watasa shiri

Save and edit this resource as a Word document

Abun lura ga mai-gabatrwa

Daidaito da sauyawar yanayi babbar kalubalace ga kasashe Afrika, wanda a cikin kasashen har da Nijar. Kamar sauran kasashe, Nijar na cigaba da samar tare da aiwatar da tsare-tsare domin cimma daidaito da sauyin yanayi. Amma kafin kasar ta samar da ingatatun manufofi, tana bukatar bayanai masu muhimanci kan yarda yanayinta zai cenza da kuma hadarin da ke tattare da shi. A halin yanzu, akwai karancin bayanai kan hanyoyin da manoma zasuyi amfani dasu wurin cinma daidaiton sauyin yanayi da zasu fuskanta.

Domin taimakawa wajen magance wannan gibi na ilimi, wata kungiya ta Jamus mai suna Cibiyar Nazarin Tasirin Yanayi ta Potsdam, ta gudanar da wani cikakken binciken kimiya kan yadda yanayin kasar Nijar zai iya canzawa cikin shekaru da dama masu zuwa. Binciken nasu ya samar da bayanai kan yadda yanayin zai iya canzawa da kuma tasirin waɗannan canje-canje ga manoma.

Haka-zalika nazarin yayi bayanin yadda ake sa ran samun cenjin sauyin yanayi a Nijar, binciken ya kuma yi nazari kan irin hanyoyin noman da za su baiwa manoman Nijar kyakkyawar damammakin samun daidaito da sauyin yanayi a nan gaba.

Wannan rubutun wata tattaunawa ce ta almara tsakanin ma’aikatan gidan rediyo biyu. Mai Gabatarwa na 2 yana gabatar da binciken kimiyya daga Cibiyar Potsdam. Mai Gabatarwa na 1 yanayin tambayoyi game da abin da binciken ya gano, kuma Mai Gabatarwa na 2 ya na ba da amsa. Masu gabatarwar su biyu sun tattauna hasashen da binciken kimiya yayi ta yadda yanayin kasar Nijar zai sauya. Haka zalika, sun bayyana hanyoyin nau’ikan noma guda hudu mafi kyau da za su taimaka wa manoman Nijar su dace da sauyin yanayi.

Zaka iya amfani da wannan rubutun a matsayin tushe don ƙirƙirar naka shirye-shiryen kan sauyin yanayi da yadda manoma a yankinka za su fi dacewa da shi. Ga wasu hanyoyin yada wannan bayanan domin masu sauraron ku su fahimta kuma su yi aiki da bayanan da suka ji:

  • Za ku iya gayyatar wani masani a bangaren sauyin yanayi / ko kuma masanin aikin gona don tattauna hasashen binciken game da sauyin yanayi da irin tasirin da za su yi kan manoman Nijar.
  • Za ku iya gayyatar kwararren masanin aikin gona don yin fashin bakin shawarwarin da binciken kimiyya ya bayar, yayi karin bayyani dalilin da ya sa yake da fa’ida sosai, sannan ya amsa tambayoyi kan yadda manoma za su fi aiwatar da ayyukan, tare da magance duk wani ƙalubale na yin hakan.

Akalla wanan tattaunawa zata dau lokaci kamar: mintina 25, har da gabatarwa da sauti.

Rubutunsa

MAI GABATARWA 1:
Ina kwanan mu, masu sauraro.

MAI GABATARWA 2:
Ina kwanan mu, jama’a. A yau zamu tattauna akan cenjin weda, wato sauyin yanayi.

MAI GABATARWA 1:
Hakane. Kuma daya daka cikin hasashen da zamuyi akan sauyin yanayi shine, a yanzu haka, kowane manomi a Afrika ya san da batun sauyin yanayi!

MAI GABATARWA 2:
(Dariya) Kwarai, sun sani! Kuma suna ganin tabacin sauyin yanayin a kewaye da su. Sauyin yanayi lamari ne na yau da kulum a Nijar. Manoma suna ganin yadda ake rana mai zafi sosai da kuma dumin garin da daddare, sanan matsaikacin zafi da akeyi a shekara a Nijar ya hau zuwa 0.43 oC, ko kusan rabin digiri, daka 1988 zuwa 2006.

MAI GABATARWA 2:
To, a yau za mu yi magana ne kan yadda ake hasashen sauyin yanayi zai cenja yanayin Nijar nan da shekaru 30 masu zuwa da kuma bayan haka. Sannan kuma za mu gabatar da wasu hanyoyin noma da za su taimaka wa manoman Nijar su dace da wannan sauyin yanayi.

MAI GABATARWA 1:
Mun riga mun san cewa, kamar sauran ƙasashe na Afirka kudu da hamadar Sahara, illar sauyin yanayi zai shafi kasar Nijar. Yanayin ya riga ya canza sosai, kuma ƙasar ba ta da ikon iya jurewa ko kuma dacewa da sauyin yanayi cikin sauƙi. Nijar ta dogara sosai kan noman amfanin gona da kiwon dabbobi, wadanda suka dogara da yanayin da ya dace. Har ila yau, gurbacewar kasa da kwararowar hamada sun kasance manyan kalubale ga masu noma, don haka sauyin yanayi zai kara wa wadannan matsalolin ne kawai.

MAI GABATARWA 2:
Domin fadada bincike kan wadannan batutuwa, wata kungiyar kasar Jamus mai suna Cibiyar Nazarin Tasirin Yanayi ta Potsdam, ta gudanar da wani bincike na kimiyya da ya yi tambayoyi guda biyu: Na farko, ta yaya yanayi na Nijar zai iya canzawa cikin shekaru 30 masu zuwa da kuma bayan haka? Na biyu kuma, ta yaya manoman Nijar za su canja salon nomansu don su dace da sabon sauyin yanayin, tare da tabbatar da samun isasshen abinci da isassun kudaden shiga don tallafawa iyalansu?

MAI GABATARWA 1:
Waɗannan tambayoyi biyu ne masu mahimmanci. Ka ce masanan sun duba yadda yanayin Nijar zai canza. To, a cewar binciken, ko wane tasiri sauyin yanayi zai yi kan yanayi a Nijar nan da shekaru 30 masu zuwa?

MAI GABATARWA 2:
An yi hasashen cewa yanayi zai canza ta hanyoyi da dama: Za a sami yanayin zafi mai yawa, da matsanancin yanayin zafi, da karuwar ruwan sama na shekara-shekara da karuwan ruwan sama mai yawa, da kuma canje-canjen wurin samuwar ruwa a kasa. Sauyin yanayi zai shafi amfanin gona, zai kuma shafi wasu wuraren da aka saba noman wasu tsirarun amfanin gona.

MAI GABATARWA 1:
Toh yanzu mu fara da yanayin zafi. Ta ya yanayin zafi zai cenja a Nijar a shekaru 30 masu zuwa?

MAI GABATARWA 2:
Ana sa ran matsakaicin yanayin zafi a Nijar zai karu tsakanin digiri 1.3 zuwa 1.9 a Nijar nan da shekara 2050.

MAI GABATARWA 1:
Toh ruwan sama fah?

MAI GABATARWA 2:
Ana kuma hasashen karuwar ruwan sama na shekara-shekara—da kuma karuwar matsanaicin alamura da suka shafi yanayi a duk sassan kasar.

MAI GABATARWA 1:
Me kake nufi “matsanaicin alamura yanayi”?

MAI GABATARWA 2:
Matsanaicin alamura wasu abubuwa ne da ba’a zaton su, ba’a kuma saba dasu ba, suna zuwa da tsanani, ko kuma yanayi mara lokaci. A Nijar, wannan zai hada da ruwan sama mai yawa wanda zai iya haifar da ambaliya. An yi hasashen cewa ruwan sama mai karfin gaske zai karu a dukkan sassan Nijar nan da zuwa shekarar 2050. Amma, kamar kowane hasashe, abin da zai faru a zahiri zai dogara ne kan irin matakan da za’a dauka a fadin duniya nan gaba kadan don rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli. wadanda ke kawo sauyin yanayi.

MAI GABATARWA 1:
Toh. Kace ana sa rai matsakaicin yanayin zafi zai karu da ga digiri 1.3 zuwa 1.9 nan da shekarar 2050. Ko wanan zai haifar da banbanci mai girma? Dan ba kowa bane zai gane idan yanayin zafi ya karu da digiri daya ko biyu. Shin zai kawo cenjin noma ga manoma?

MAI GABATARWA 2:
Hakika, digiri 1.3 zuwa 1.9 zai kawo cenji sosai. Wannan karin adadin zafi zai iya, alal misali, rage yawan amfanin gona, kodayake ba duk amfanin gona zai shafa ba. Hasali ma, a jamhuriyar Nijar, albarkatun gona na wasu kayan gona na iya karuwa, a kalla har zuwa shekarar 2050.

MAI GABATARWA 1:
Toh, da alama zuwa 2050, za’a samu karuwar yanayin zafi, za mu sami ƙarin ranaku da dare masu matsanancin zafi, kuma za a sami karuwar ruwan sama. Ta yaya wannan karin ruwan sama zai shafi manoma?

MAI GABATARWA 2:
Manoma a Nijar sun dogara sosai kan ruwan sama da ruwan da ke kasa. Ana sa ran adadin kogin zai karu a fadin kasar, ciki har da kogin Neja da kuma kwarin Dallo Bosso. An yi hasashen cewa kogin Neja zai karu a duk shekara, musamman a watan Oktoba da Nuwamba. Shi kuma kwarin Dallo Bosso, ana hasashen kwararar kogin zai karu a cikin watan Agusta da Satumba.

Masana kimiyya daga Cibiyar Potsdam sun yi hasashen cewa, saboda wadannan sauye-sauye, wasu yankunan kasar za su fi dacewa da noman dawa, kuma amfanin dawa zai karu har zuwa shekara ta 2050 da kuma bayan haka.

A halin yanzu, wasu bangarori kalilan ne a Nijar suka dace da noman masara. Ana hasashen hakan zai ci gaba da kasancewa, duk da cewa a yankunan kudancin kasar kamar Zinder da Maradi, ana hasashen noman masara zai karu har zuwa shekarar 2050, sannan ya kuma ragu.

Ana hasashen samuwar gero zai fadada zuwa arewa, wanda hakan zai sa yankin Tahoua ya fi dacewa da noman gero.

A ƙarshe, kusan kashi 10% na ƙasar sun dace da noman wake. Ba a tsammanin wannan zai canza, amma za a sami bambancin yankuna daban-daban. Misali, dacewa zai ragu a yankin Zinder kuma ya karu a yankunan Tahoua da Tillabery.

MAI GABATARWA 1:
Na yi farin ciki ba duka labaran ne mara sa dadi ba ga manoman Nijar.

Ka yi nuni da cewa, binciken kimiyya ya yi nazari kan irin ayyuka da manoman Nijar za su yi amfani da su wajen daidaito da wadannan sauyin yanayi. Wadanne ayyuka ne masana kimiyya suka nuna a matsayin mafi amfani don daidaitawa da sauyin yanayi?

MAI GABATARWA 2:
Akwai ayyukan noma da yawa waɗanda kan iya taimakawa manoma su dace da canjin yanayi. Amma masanan sun gano wasu ayyuka guda hudu da suka fi dacewa ga manoman Nijar su samu albarkatun noma na musamman.

Waɗannan su ne: noman gandun daji, musamman ma idan manoma sun gudanar da aikin sake shuke-shuken bishiyu, harkar kula da yalwar ƙasar noma, ban ruwa don noman kaka, da ingantaccen tsarin kula da abinci da ciyar da dabbobi. Ya kamata na ƙara wani batu guda daya: Lokacin da manoma suka yi amfani da haɗakar waɗannan dabarun, za su iya samun nasara sosai.

MAI GABATARWA 1:
Kana nufin, alal misali, hada noman gandun daji da kuma ban ruwa? Ko inganta kayan abincin dabbobi da kuma kula da yalwar kasar noma?

MAI GABATARWA 2:
Kwarai kuwa.

MAI GABATARWA 1:
Yawwa. Toh bari mu fara da noman gandun daji da kuma farfado da bishiyu. Amma da farko, me kuke nufi da “noma gandun daji”?

MAI GABATARWA 2:
Noman gandun daji ya ƙunshi mu’amala a cikin filin noma tsakanin amfanin gona da bishiyoyi. A Nijar, ana yin aikin noman gandun daji ne ta hanyar Farmer Managed Natural Regeneration ko FMNR. FMNR wani nau’i ne na aikin noma wanda maimakon dasa bishiyoyi a cikin gonaki, manoma na duba wasu bishiyoyin daji da ciyayi waɗanda tuni suke girma a cikin gonaki tare da kiyaye su sosai don su ci gaba da girma.

Tare da FMNR, ana iya kare bishiyoyi a wuraren da manoma ke noman amfanin gona na shekara, da kuma inda suke kiwo da kuma ciyar da dabbobi. Bishiyoyi suna samar da kayayyaki da yawa waɗanda manoma za su amfana kuma za su iya amfani da su ko kuma su sayar da su a kasuwannin unguwa, ciki har da ‘ya’yan itatuwa, goro, katako, da itacen wuta. Bishiyoyi kuma suna rage radadin zafi musamman ga shuke-shuke da dabbobi da basa san zafi sosai. Suna kuma aiki wurin kawar da gugin iska, kuma suna taimakawa wajen rage zaizayar ƙasa daga iska da ambaliya.

Idan manoman suka rungumi aikin noman gandun daji a Nijar, sakamakon hasashen shi ne, dawa, gero, da wake za su karu, musamman a wuraren da ba’a yi amfani da taki ba.

MAI GABATARWA 1:
Ko akwai kalubale wajen fara aikin noma gandun daji musamman FMNR a Nijar?

MAI GABATARWA 2:
To, yana da mahimmanci ace bishiyoyi ba sa rufe amfanin gona da yawa. Haka kuma, ana iya samun jayaya a wurin amfani da fili tsakanin noma da kuma sauran amfanin gona, kamar kiwo. Manoma za su iya guje wa waɗannan matsalolin ta hanyar kyakkyawan shiri da kuma yin aiki tare da makiyaya don kafa hanyoyin kiwon dabbobi.

Wani kalubalen kuma shi ne, akwai tazarar shekaru da dama tsakanin lokacin da manoman suka fara aiwatar da aikin noman gandun daji da kuma lokacin da suke samun kudade da ka noman. Wasu manoma na ganin wahalar tsawon jiran.

Amma yin FMNR ba shi da tsada saboda ba ya buƙatar wani abu da za’a nema daka waje. Agroforestry yana da arha kuma yana da sauƙin kafawa, yana da fa’idoji da yawa, kuma yana ta samun karbuwa da cigaba a shekaru da yawa a Nijar, don haka akwai sha’awar da babban yuwuwar faɗaɗa shi a duk faɗin ƙasar.

MAI GABATARWA 1:
Toh mung ode sosai. Na biyu daga cikin ayyuka hudu da suka fi dacewa shine Hanyoyin kula da kasar noma (Integrated Soil Fertility Management), ko ISFM. Toh mene ne ma ainihin ISFM?

MAI GABATARWA 2:
ISFM wani tsari ne na ayyukan noma wanda aka ƙera don inganta kyawun ƙasa da kuma dakatar da lalacew da raguwar sinadirai dake kasa. Ya ƙunshi nau’ikan ayyuka daban-daban, tare da sanin yadda ake daidaita waɗannan nau’ikan ayyuka zuwa yanayin da ya dace a al’adan ce, har zuwa matakin ƙirƙira, yayin kiyayewa ko haɓaka albarkatun gona.

Yana da matukar mahimmanci ana lura da ruwa da ƙasar gona a Nijar saboda dalilai da yawa. A jamhuriyar Nijar noma ya dogara ne da gonaki kalilan ko kuma gonaki da suka fara bushewa saboda karin yawan mutane da kuma wuyar samun filaye da suke da sinadirai na yin noma. Zaizayar kasa ta dalilan ruwa da iska, raguwar sinadiran kasa, karin samun kasa mai gishiri duk hanyoyi ne da suke kashe kasar shuka. Kuma rashin damshin ƙasa yana rage samar da amfanin gona a wurare da yawa.

A takaice, fa’idojin ayyukan ISFM, zamu iya cewa an tsara su ne don cimma manufofi guda huɗu: 1) don haɓaka taran ruwan sama da rage guduwar sa bayan ya sauka, 2) don rage zaizayar kasa ta dalilin ruwa da iska, 3) don sarrafa ƙarancin albarkatun ƙasa, da 4) don amfani da takin zamani.

MAI GABATARWA 1:
Zaka iya bamu misalin ISFM da ake amfani dasu a Nijar?

MAI GABATARWA 2:
Kwarai kuwa. Jerin ayyukan ISFM da ake a Nijar sun hada da tassa, wanda aka fi sani da zaï, raba-wata, duwatsu, tsirarun ciyawa, da kuma huda.

MAI GABATARWA 1:
Mungode. Ko zaka fara da yi mana bayanin mai tassa da raba-wata ke nufi?

MAI GABATARWA 2:
Tassa wata hanya ce ta gargajiya da ake tara ruwa inda manoma ke yin hakar shuka da fadin sa bai wuce 20-30 cm ba da zurfin daka 20-25 cm, wanda tazarar tsakani ramukan ba ya wuce mita daya. Shi kuma rabin-wata ramuka ne dake yi masu kama da tsayuwar wata wanda fadin bay a wuce mita biyu, zurfin su kuma ya kai 15-20 cm, tazarar da ke tsakanin su kuma zata kai mita takwas.

Duka wadanan ramukan shuka na gargajiya suna tara ruwa ne, suna kara danshin kasa ta yanda manoma zasuyi shuka a cikin ramukan. Manoma su na kara kara na gero, kashin shanu, ko kuma taki a cikin ramukan. Ta dalilin haka, suna taimakawa wajen farfado da mataciyar kasa, ba ta kara danshin kasar ba kawai, har da kara mata sinadirai. Wanan yana karawa manoma su samu albarkatun gona a inda akayi shuka a tassa da rabun-wata. A Nijar, gero shine amfanin gona da aka fi shukawa a ramukan tassa da rabun-wata, duk da dai wasu manoma suna hada gero da dawa.

MAI GABATARWA 1:
Yawwa. Toh ko zaka yi mana bayanin me ake nufi da tara duwatsu sanan ta yaya zasu taimakawa manoma Nijar su samu daidato da sauyin yanayi?

MAI GABATARWA 2:
Taran duwatsu shima ana kiran sa da layin duwatsu, kuma mafi yawan lokaci ana hada shine da tassa a inda aka samu lankwaya a gangare don kara yawan ruwan da ke kutsawa cikin kasa, yana kuma rage zaizayewa kasa ta tassa. Tarun duwatsu ya hada da jera duwatsu kusa da juna. Manoma suna farawa da cire kasar wurin da takai 10-15 cm a kan layin inda za’a gina taron duwatsun. Tsawon ya kai tsayin 20-30 cm tazarar da ke tsakanin duwatsu ya na kai 20-50 cm, ya danganta da gangaren kasar wurin.

Tarun duwatsu na aiki sosai a inda akayi shuke-shuke a tsakanin su, kamar ciyayi, hayi, ko bishiyu da kuma inda aka sa takin gargajiya a wurin. Yin amfani da tarun duwatsu a irin wanan yanayin na rage zafin kasa kuma yana kare kasa daka guguwa iska. Shuka ciyayi tsakanin duwatsu na kara sa ruwa ya ratsa cikin kasa.

Ana iya barin tarun duwatsu ya kai shekaru 20. Bayan wani lokaci, kasa na taruwa a jikin su.

MAI GABATARWA 1:
Toh irin wadanan ayyukan suna aiki kuwa? Suna kara yawan amfanin gona?

MAI GABATARWA 2:
Tabbas. Cibiyar Potsdam ta yi hasashen cewa amfani da tassa na iya inganta yawan dawa da kashi 1500 cikin dari, musamman a kudancin Nijar. Wannan shine dalilin da ya sa suka ce yana daya daka cikin dabarun da suke da tasiri wurin daidaito da sauyin yanayi. Ga wani misali: A cikin aikin shekaru takwas a Tahoua, kusan kadada 6,000 na ƙasa mai wace ta lalace aka maido da ita mai kyau ta hanyar ISFM.

ISFM na taimaka wa manoma su kasance masu juriya ga fari da kuma ƙarancin abinci. Wannan yana da matukar muhimmanci a Nijar, inda karuwar yawan mutane ke kawo kalubale akan gonakin da suka rage masu amfani.

MAI GABATARWA 1:
Shin waɗannan gine-ginen suna buƙatar aiki mai yawa don ginawa da kulawa?

MAI GABATARWA 2:
Yana ɗaukar ƙasa da rabin yini a kowace hectare don tsara duwatsu da kuma samun horo akan su sau ɗaya a shekara. Kuma suna buƙatar kulawa kawai kowace shekara ta biyu. An dauki kwanaki shida a cikin shekarar farko na tattara tsakuwa da duwatsun a gina su, da kwana biyu a cikin shekaru masu zuwa. Dole ne a sake gina ramukan tassa kowace shekara. Gaba daya aikin shirya kasar da tona ramukan tassa, manoma na bukatar kwana biyar zuwa shida a kowace kadada kowace shekara. Don haka idan manoma sun gina ramukan tassa akan kadada biyu, zai dauki kwanaki 10-12 a shekara.

MAI GABATARWA 1:
Toh shin irin wanan lokaci da aiki da ake batawa wurin yin wanan aikin, kana gani zai kawo wa manoma kudi?

MAI GABATARWA 2:
Yin amfani da ayyukan ISFM irin wannan ba’a kashe kuɗi mai yawa. Idan ka haɗa aiki da lokaci da aka bata, kuɗin da suka samu daga karuwar yawan amfanin gona yana nufin manoma sun fara ganin riba a cikin shekara ta biyu.

MAI GABATARWA 1:
Yawwa. Yanzu muyi maganar da aiki na uku da suka fi dacewa da kayi magana: ban ruwan rani.

MAI GABATARWA 2:
A lokacin ban ruwan noman rani ko kuma damuna, manoma kan bar filayensu su huta na tsawon makwanni biyu a ƙarshen damina sannan su shuka amfanin gona da ake shukawa da rani kamar albasa, tumatir, da barkono. Ana ban ruwa ne da ruwa da ke fitowa daga rijiyoyi, tafkuna, da rijiyoyin burtsatse. Wannan dabarar tana taimaka wa manoma su guje wa ƙarancin abinci tare da bambanta abincinsu a wannan ɓangaren na shekara.

Ana iya amfani da tsarin ban ruwa mai arha wanda ba ya buƙatar kulawa mai yawa a duk inda aka samu ruwa.

MAI GABATARWA 1:
Shin akwai kalubale wurin ban ruwan noman rani?

MAI GABATARWA 2:
Samun ruwa abu ne mai wahala, saboda yana da muhimanci a guji amfani da shi fiye da kima, a bangare daya don rage janyewa ruwan kasa. Yana da matukar muhimanci a samar da ingantatun hanyoyi na magance rikice-rikice tsakanin masu amfani da ruwan ƙasa da na sama.

Har ila yau, yana iya ɗaukar shekaru 20-25 kafin manoma su dawo da jarin da suka saka a fannin ban ruwa noman rani.

MAI GABATARWA 1:
Tab, wanan babban kalubale ne. Toh ka ce ingantacciyar hanyar kula da kiwon dabbobi da ciyarwa ita ce hanya ta hudu da za ta taimaka wa manoman Nijar su daidaita da sauyin yanayi. Wadanne irin cigaban ciyarwa da sarrafa kayan abinci kuke magana akai?

MAI GABATARWA 2:
Akwai nasara da aka samu a wasu yan nau’ikan shirin, daya da ka ciki kuwa shine sabon nau’in abinci. Misali, gwajin wani sabon nau’in dawa mai suna Fadda ya kara yawan abincin a yankuna daban-daban na Nijar da kashi 10-80 cikin dari, inda aka fi samu yawan wanan a arewacin kasar, yayin da amfanin gona ya kusan ninkawa a Agadez.

Wata hanyar ita ce noman alfalfa. Alfalfa na iya ba da abinci a lokacin rani idan aka yi ban ruwa, don haka ya fi wa makiyaya kyau fiye da yawan neman abinci a lokacin rani. Masu sana’a kuma za su iya sayar da rarar alfalfa don samun kuɗin shiga, ko ma su yi amfani da alfalfa wajen ciyar da dabobin rumfuna, sannan su sayar da dabbobin da ke ciki.

Amma alfalfa na da sauran fa’idodi masu yawa. Musamman idan aka shuka da yawa, yana ƙara bawa kasa kariya ta samar da ciyayi, wanda ke taimakawa wurin sake gyara ƙasa mara kyau.

Wani karin amfanin na ta shine, yawanci mata da matasa sun fi maza wajen tallafa wa iyalansu da kuma samun riba ta hanyar samar da abincin dabobi da sarrafa shi fiye da maza. Don haka noman alfalfa, misali ta hanyar samar da bankunan kiwo, na iya samar da ayyukan yi ga mata da matasa.

Idan aka kwatanta da sauran abincin dabobi, alfalfa abinci ne mara tsada mai dauke da furotin da kuma sauran sinadiran gina jiki. Shanu na tauna shi cikin sauki, kuma yana da yawan albarka, kuma yana jure fari saboda jijiyoyin sa sun kafu a kasa sosai. Alfalfa kuma yana gyara nitirogin, ya mai da shi mai amfani a wurin da ake jujjuya noma.

MAI GABATARWA 1:
Noman alfalfa da kuma sabbin nau’ikan abincin dabbobi kamar alama ce ta samun nasara daidaito da sauyin yanayi. Menene kalubalen fadada noman alfalfa?

MAI GABATARWA 2:
Alfalfa yana da sauƙin girma, amma yana buƙatar ban ruwa. Saboda haka ana buƙatar samun wuraren ban ruwa ko filayen ban ruwa don samar da alfalfa. Amma, ko da manoma sun sami damar shiga filayen ban ruwa, da yawa ba za su iya karbar hayar su ba—ko gina tsarin ban ruwa a gonar su. Hakanan, kamar yadda aka ambata a sama, yana da mahimmanci a guje wa rikice-rikice yadda ake amfani da ruwa saboda wahalar sa. Wannan yana nufin, alal misali, dole ne a tsara aikin noman abincin dabobi cikin tsanaki don kar a samu akasi da noman abincin rani.

Wani kalubalen kuma shi ne, tattarawa da sifirin abincin dabobi na da tsada a Nijar. Amma, an samu wani sabon mashin na hannu mai saukin kudi da ake amfani dashi wurin tattarawa sanan ayi siffirin sa. Ana cigaba da duba hanyoyin samun kayan aiki masu sauki don adana kayan abinci dabobi wanda zai taimaka sosai a wanan bangare.

Fadada noman alfalfa kuma na iya haifar da karuwar yawan dabbobi, wanda hakan zai kara haifar da hayaki mai gurbata muhalli da ke dagula sauyin yanayi.

A karshe, mata da matasa ba su da iko akan harkar da ta shafi kiwo da noman abinci dabobi. Mata yawanci suna samun damar malakar gona ne kawai ta hanyar aure. Idan ba su suka mallaki gonar da suke noma ba, toh an cire su daga jerin masu yanke hukunci. Bawa mata hakkinsu da kare yancin su na daukar mataki akan alamura da suka shafi gonaki zai sa su ci moriyar kiwo, da kuma yadda zai taimaka musu su dace da canjin yanayi.

Amma duk da waɗannan ƙalubalen, noman sabbin nau’in abincin dabobo da kuma noman alfalfa na da babban tasiri na haɓaka ƙarfin manoma don dacewa da canjin yanayi. Kuma, kamar ayyukan ISFM, manoma ba dole ba ne su jira dogon lokaci don cin moriya aikin su. Manoma za su iya fara samun fa’ida ta kuɗi a cikin shekara ta biyu bayan noman amfanin gona irin su alfalfa.

MAI GABATARWA 1:
Toh mung ode sosai. Ka ba mu abubuwa da zamuyi tunani sosai akai. Idan zan iya yin bayani a takaice, da farko ka yi magana kan yadda akai hasashen yanayi zai canza a Nijar nan da shekaru 30 masu zuwa, har zuwa 2050, da kuma bayan haka. Ka ce yanayin zafi zai karu, za’a samun karuwar ruwan sama, za’a samu karuwar alamura na zafi da ruwan sama. Sannan kuma ka yi magana game da abin da manoma za su iya yi don dacewa da waɗannan canje-canje na yanayin zafi da ruwan sama. Ka ce akwai nau’o’i iri hudu da ke nuna mafi girman da zasu taimaka wa manoman Nijar su dace da sauyin yanayi: noman gandun daji, musamman ma idan manoma suka bi hanyar gargajiya dan dawo da albarkartun gona, ISFM, noman rani da kuma noman abincin dabobi na zamani.

MAI GABATARWA 2:
Eh, waɗannan su ne ƙarshen binciken masana kimiyya daga Cibiyar Nazarin Tasirin Yanayi na Potsdam. Waɗannan su ne sauye-sauyen da ake sa ran za su shafi yanayi da kuma ayyukan da manoma shawara su yi.

Amma tabbas, yana da kyau a koyaushe manoma su yi magana da ƙwararru da suke unguwanin su ko yankin su idan suna son kare bishiyoyi a gonakinsu ko amfani da ramukan tassa-ko ban ruwan noman rani, ko kuma noma sabbin abincin dabobi. Madaidaicin shawarwarin da ke aiki mafi kyau ga kowane manomi zai dogara ne akan inda suke zaune da ainihin halin da suke ciki.

Duk da haka, ko a ina kake, waɗannan shawarwari ne da ya kamata manoma su yi la’akari da su da gaske—kuma su yi la’akari da su nan ba da jimawa ba.

MAI GABATARWA 1:
Mungode sosai da wanan. Zamu dawo wani makon da wani sabon [sunan shirin]. Zamu sake tattaunawa a wani makon.

MAI GABATARWA 2:
Sai anjima mu, mu hadu a wani makon.

 

Acknowledgements

Gudunmuwa daka: Vijay Cuddeford, Manajin edita, Farm Radio International.

Bita daka: Carla Cronauer, Mai bincike a Cibiyar Nazarin Tasirin Yanayi ta Potsdam

 

 

Information sources

Tushen bayanan

Röhrig, F., Gloy, N., von Loeben, S., Arumugam, P., Aschenbrenner, P., Baek, H., Cartsburg, M., Chemura, A., Ibrahim Fodi, B., Habtemariam, L., Kaufmann, J., Koch, H., Liersch, S., Lüttringhaus, S., Murken, L., Ostberg, S., Schauberger, B., Shukla, R., Tomalka, J., Wesch, S., Wortmann, M. & Gornott, C., (2022). Binciken illar sauyin yanayi domin tantancewa da auna dabarun da suka dace da harkar noma a Nijar. Wanda ya shirya wanan bayanan shine Cibiyar Nazarin Tasirin Yanayi ta Potsdam da hadin gwiwar Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit (GIZ) GmbH a madadin ma’aikatar tattalin arizki da cigaba ta Jamus (BMZ), 154 pp. https://agrica.de/downloads/?country=16&format=27