Unguwanin gandun daji na samun kudin shiga a yayin da suke kare mahalin su

Lura ga mai watasa shiri

Yawan mayagun dabbabi da tsirai na ragewa. Misali,ana tunanen  akwai giwayen Africa miliyan uku zuwa biyar a cikin sheara ta 1930 zuwa 1940.Adadin na kasa da rabin miliyan ayau.Ada , haramtaciyar cinikin hancin giwa (Ivory) nada barazanan gaske,amma tun da aka dora  hani akan cinikin Ivory a shekara ta 1989, babban matsalar itace rasa matsuguni a dalilin fadada tsare tsare da harakar gona.Ga wasu dangin halita, farautan namun daji nada gaugawan barazana.

 

Wasu unguwannin na samun lalacewar sosai na albarkatun gona harma da rasa rayukan mutane a dalilin rikicin miyagun halitu.Wannan lamari aihin saboda yawan adadin mutane a mazaunin miyagun dabbobi ne.Amma kamata yayi ‘yan kyauye su nemi abinci kuma su samu kudin shiga.Ta yaya miyagun dabbobi  da adadin mutane zasu yi rayuwan jin dadin juna?

 

A cikin lamruka da dama, gwamnati da kugiyoyi masu zaman kansu na aikin tare da al’uma su samun hannyoyi hulda masu dorewa da kiyaye ainihin mahalin su. A wasu lamrukan kuma, al’uman da kansu suka nemi hannyar kiyeye maalin su, suna ciyar da kansu kuma suna samun kudin shiga.

 

Wannan rubutun na bayanin wani aiki acikin kudu maso yammancin Cameroon.Wata babban kugiya mai zaman kanta na ksaa kasa- wato, World Wide Fund for Nature (WWF atakaice) tana taimaka wa unguwannin gandun daji su samu ayukan dake samar musu da kudin shiga daga miyagun iri ba tare da an lalata gandun gaji ba.Idan kayi binciken abin dake aukuwa a unguwanka, zaka iya gano irin ayukan da WWF ke gudanarwa da wasu kugiyoyi.

 

Wannan rubutun ya dogara ne kan ainihin fira, Zaka iya amfani da rubutun kayi bincike ka rubuta wani akan irin zancen a unguwan ka.Ko kana da zabi kayiamfani da shi a tashar kana mai amfani da murya ‘yan wasan kwaikwayo su wakilci masu magana, Idan haka ne,ka tabbatar ka sanar tun da farkon shirin cewa,muryoyin na ‘yan wasan kwaikwayo ne, ba ainihin mutane da akayi fira da su ba.

Rubutunsa

Mai watsa shiri:
Ina kwana, mai saulare.Kana da sanin cewa zaka iya taimaka wa kare ababan halita? To, shirin yau zai taimake ka ka fahimci yanda yake.Shrin na zance akan sanin aiki wasu ‘yan kyauye uku dake jihar gandun daji a cikin jihar kudancin Cameroon,da yanda wata kungiya da ake kira World Wild Fund for Nature ko WWF atakaice ta taimaka musu.

Mai watsa shiri:
Duk inda ake rayuwa, mutane na dogaro ne akan mahali mafi kusa dasu su noma abinci su kuma nemi kudi.A unugwanin gandun daji, mutane na yanka itacuwa suyi amfani dasu a katako ko kuma suyi wasu harakoki na daban da su, ko kuma a sawake su dibi zuma.Suna hallaka dabbobi domin cimaka da sayarwa.Albarkatun gandun daji sun shahara.Ko domin tsiro da dabba da ake magani dasu, mutane na yawan lalata dabbobi da tsiran dake gandun daji domin nemar kudi ko biyan bukatun kullun.

Lalata gandun daji yayi mumunar tasiri, akan biyun, lalata mahali mafi kusa da duniya baki daya. Misali,lalata gandun daji na taimaka wa yanayi ta tashi sama abinda ke kawo sauyin yanayi. Lalata gandun daji na halaka nau’i nau’i dabbobi da tsirai.

Kungiyoyi da daman na aikin kare gandun daji. Daya ce World Wide Fund for Nature ko WWF atakaice,wata kungiya ce mai zaman kanta da aka kafa ta tun a cikin shekara ta 1961.Munufar kungiyar itace ta hana lalata ainihin mahali da su gina nan gabar da mutane zasu yi rayuwar zaman lafiya da halita ta hannayar kiyaye nau’in ababan halata,kira akan rage gurbatawa da banzatarwa, da tabbatar da amfani da arzikin kasa masu karko da sabantawa.

WWF tana aiki a Cameroon tun shekara 1989 tana kulawa da shiriye-shirye hudu, da suka hada da shirin WWF Coastal Forests Programmme a can kudu maso yamma da jihar Littoral dukannin su a Cameroon.Firan da zaka ji anyi sune a gun shirin cikin yankin Kupe Muanenguba, dake jihar kudu maso yammancin Cameroon.A cikin wuraren ababan halita daban daban muhimmai a kudu maso yamma inda WWF ke aiki, Unguwan Kupe Muanenguba itace ta musamman

Sautin gandun daji- tsuntsatye da ta wasu

Mai watsa shiri:
Kupe unguwa ce kan tudu masu tsinin da tsayin su yakai mita 2,000 samma da kwanciyar teku. Mafi girman gun gandun daji ne, kuma gandun dajin ta tana cikin gandu daji mafi tsufa a Africa
.
Bugu da kari, shuka tsiron da nan jihar kawai suke tsira, kuma akwai miyagun dabbobi da nau’i nau’in tsirai:mannyan birai irin su mahudi , kebabu nau’i irin hawainayar, kuma da samma da nau’in tsuinye 300.

Duk da fuskantan matsalar cigaba da lalacin mahali acikin jihar, WWF na haraka tun a cikin shekara 1990. Harakokin WWF na sajewa da karfafa aikin da wasu kungiyoyi kamar Birdlife International da Ma’aikatan kula da gandun daji da dabbobi, da suka shirya a shekara ta 1990-2000 gangami kiran mutane da kada su halaka miyagun dabbobi ko yanka bishiya ba tare da izsini ba a cikin gandu daji.

WWF tana aiki ne da al’umar dake rayuwa a cikin jihar. Tana ilimantawa da basu horo su samu kudi ba tare da sun lalata gandun daji ba, taimaka musu da kudi,kayan aiki, da kuma horo su iya gudanar da harakokin da zai taimaka musu nemar masu sayan kayan su.Ta hakan,WWF tana taimaka wa rage talaucin unguwannin da taimaka musu gudanar da aiki misaltun gandun daji da zasu nare.

Ga labaran Ngol’epie, Pa Atabe, da Mbonteh, mutane uku daga yankin Kupe Muanenguba, waddan da, da taimakon WWF, na bayar da tasu gudunmuwar misaltun gandun daji da zasu nare.

Waka

Mai watsa shiri:
Da farko zamu saulari Ngol’epie, dake Nyasoso,wata karamar kyauye kusa da gandun dajin Kupe.

Mai watsa shiri:
Barka, Mr. Ngol’epie, yaya kake?

Ngol’epie:
Barka, ina lafiya

Mai watsa shiri:
Ko zaka iya fada wa masu saularen mu abinda ya sa da kuma yanda ka yanke shawarar juyawa daga Mafarauci zuwa manomi?

Ngol’epie:
Kwarai ko, ni mazaunin Nyasoso ne tare da iyali na.A matsayi na na mafarauci, Ina shiga gandun daji a kullun in kashe dabba in sayar, in kuma sassake jikin bishiya inyi maganin gargajiya dashi.

Na kuma yi aiki a matsayin mai shiga gaba ga kungiyoyi masu zaman kansu dake aiki a nan gandun daji.Amma hulda na da WWF, na koyi cewa harakar farauta na na lalata gandun daji

Wata rana, a yayin da nake nemar bishiyar magani a cikin daji, sai naga bera ta fito wani babban rami.Na rike ta.Da taimakon karnuka na, su suka fadada ramin, sai na kama berayen da dama acikin bagi na.Tare da mata ta,.sai na yanke shawarar kiwon waddan nan berayen. Da farko,sai na musu dakin katako,amma sai rashin sa’a ya sa berayen suka cannye.Amma godiya ga shawara da taimako dagaWWF,Zan yi sabuwar gida kuma in cigaba da kiwon berayen.Ina ciyar dasu da busasun kifi,ayaba,doya, gyeda da ciyawan fili irin su sissongo (Lura ga editor: kuma an san sa da suna raken daji ko ciyawar giwa) da kuma gannyen dankalin turawa,

Domin bani kwarin gwiwa, WWF ta saya mini tarago ta taimake ni daukar abincin berayen Kuma WWF na cigaba da bani shawara dake taimaka mini daina dora nauyi akan dabbobin daji da gandun dajin baki daya.

Bayan shekara da kiwo, berayen sun girma kuma ina muirnar cewa zan iya sayar dasu in kuma yi riba mai kyau.

Sabili da hakan, na gamsu da cewa dabbobi zasu samar mini da rayuwa, Nayi amfani da kudin farko na sayi aladu.

Mai watsa shiri:
Mr. Ngol’epie, wani abu kayi da wasu zasu iya cin moriyan ilimin ka?

Ngol’epie:
Dangani da shawarar WWF, na kafa kungiyan mutun bakwai da a hade muke misilta dabbobin.An san kungiyan a cikin yaren Bakossi, da suna “Dion de Dienge.” Harakar kasuwancin na da riba har muna gina babban daki da aluminum.Yanzu na faimci zan iya zama

kusa da gandun daji in samu kudi ba tare da na kashe dabbobi a cikin gandun daji ba.

Mai watsa shiri:
Na gode Mr. Ngol’epie.

Waka

Mai watsa shiri:
Bayan munji aikin Mr. Ngol’epie, zamu saulari labarin Pa Atabe. Ma’aikacin gwmanati mai ritaya dake Tombel, wata kyauye kamin gandun dajin Kupe.Yana cikin aikin zuma. Zuman daji na da wani dandano ta mussamman kuma tana da tsada kwarai idan ana sayar da ita acikiin birane.Idan za’a dibi zumar daji, mutane na yanka biishiyoyi dake rike da gidajen zuma,sai su lalata.

Bari mu saulari aikin Pa Atabe’s Barka, Pa Atabe.

Pa Atabe:
Barka kade, kuma barka ga duk masu saularen ka.

Mai watsa shiri:
Ko zaka iya fada mana aikin ka na yin zuma da kuma aikin ka da WWF?

Pa Atabe:
Na gode! Tare da taimako daga WWF, na halarci taron daukar horo game da yin zuma a UK da Cameroon.A nan Tombel, zan bayar da horo ga wasu kuma gaba daya zamu mu kafa wata kungiyan soma aiki wato CIG ataikace. Za’a yi kiran wannan kungiyan da Tombel-Bangem Bee Farmers Association ko TOBA.atakaice.Tare da taimakonWWF,zamu koyi yanda ake gidan kudan zuma da katako, kuma zamu samu tufafin kariya, teburi, kwalabe,magani, abin tata da gun reno

Domin jawo kudan zuma acikin watan Juli, Agusto da Satumba, ‘yan TOBA na kona maganin kudan zuma a kofar gidajen su. Kamshin kunar maganin na jawo kudan zuma.Muna kuma shuka bishiyar caliandra kusa da gidajen su, sabili da caliandra wata bishiya ce da kudan zuma ke bukata Idan bishiyar caliandra ta jawo su,a sannu sai kuda zuma su saura suyi ginin gidajen su.Watannin gaba- cikin watan Maris,Afrelu da Mayu-sai a girbe zuman, duk wani mamba sai ya kawo abinda ya diba a hedikwatar CIG.Ana sayarwa ne a gu daya kuma masu amfani da shi na gida da yawa da na gefen garin zasu zo.

Mai watsa shiri:
Wani irin amfani zaka iya samu daga yin zuma?

Pa Atabe
: Akwai amfani da dama. TOBA na samar da zuma kimanin lita 2,000 na zuma a kowace shekara,abinda ke samar da dalan Amurka 9,000 a kudin shiga mara tsoka.Kudin dake shigo wa TOBA ta karu kuma mun samar da aikin yi ga matasa.Nauyi akan gandun daji na yankaka bishiya domin dibar zuma an shafe ta.

Mai watsa shiri:
A karshe, labarin mu na uku shine na Mbonteh, dake Tombel.

Mai watsa shiri:
Barka, Mr. Mbonteh. Yaya dai a yau?

Mr. Mbonteh:
Barka kade, lafiya lau, na gode.

Mai watsa shiri:
Kai ke dauke da hakin kungiyan dake bayar da gudunmowar kare gadun daji da kiwon katantanwa (dodon kodi) Ana daraja namar katanatanwa kwarai kuma ana bukata a mannyar cibiyoyi.Fada mana taka sani.

Mr. Mbonteh:
Mutanen Bakossi dake rayuwa kusa da unguwannin gandun daji na dibar katantanwa daga dajin. Sai su sayar. Amma suna lalata wasu nau’in a cikin gandun daji.Misali, idan annako ta gita hannyar su,sai su harbe ta. Ko da yake ‘yan Bokassi na shiga daji domin dibar katantanwa, zasu faruci duk wani karamin dabba da zasu gani.

Dangani da gangami da WWF ta shirya acikin shekara ta 2001 tare da tsohon ma’aikacin Mt. Kupe Forest project da ni da wasu ‘yan kyauye muka dau sha’awar kiwon katantanwa a gida.

WWF ta taimake mu muka tsara kanmu gungu gungu mu kiwaci katantanwa. haka aka kafa gungun da ake kire Community Action for Development ko CADEV atakaice,WWF ta bamu horo gudanar da harakoki da rubuta bukatun aiki.

Kiwon katantanwa saukin aiki ne .Yana daukar watannin hudu daga lokacin saka kwai zuwa girma.Masu kiwo na sake keii so uku wannan lokacin Ya kamata a kula da kejin da kyau domin daidaitar da yanyin danshi danshi da iska.Abincin katantanwa ana yi ne daga gwanda, cocoyam, koren gannye da ayaba.

A cikin Sarrafe Sarrafe nan,WWF ta taimaki gungun da kayan aiki, shawara, horo a kasar Cameroon da wasu wuraren.Na samu damar halarta tarukan bita a Nigeria, Chile da Africa ta kudu.WWF tana taimaka wa CADEV su safarar da katantanwa zuwa shagunan kiri harma ta tattauna da kasuwanni waje wanda ke daraja namar katantanwa.Ana samun oda daga Nigeria da Italiya kai da kai.

Hadin gwiwa da WWF a zancen muhammanci ta habaka kudin dake shigowa hannun mabobin gungun.Harakokin kasuwancin CADEV na a kowace wata samar da riba kimani dalan Amurka 210 ga kungiyan gaba daya Na zamo gwani,Ina iya horar da wasu gungun.Dangi da daman na kiwon katantanwa kuma suna habaka kudin su da matsayin rayuwar su.Sabili da ba’a farautan katantanwa a cikin gandun daji sai dai ana samun su a gonaki, nauyi akan gandun daji ta rage.

Waka

Mai watsa shiri:
Ya ku masu saulare, a krashe, dora hankali akan taimaka wa al’uma su misilta karkon ababan halita a cikin jihar kudu maso yammancin Cameroon.WWF tayi kokari taimaka wa kungiyoin jama’a 33 dake cikin harakokin basu kudi kamar kiwon Kudan zuma, katantanwa (dodon kodi) kiwon alladu, beraye kanana da mannya.Waddan kungiyoyi sun gudanar da ayukan su da nuna kawanci ga mahali a sannu suna habaka matsayin rayuwar su.

Acknowledgements

Gudumuwa: Serge Kuate, PROTEGE QV, Cameroon, a Farm Radio International broadcasting partner.

Nazari: Janet Molisa, Communication Officer, WWF Coastal Forests Programme, Cameroon and Peter Ngea, Communications Manager, WWF Central Africa Regional Programme Office (CARPO), Yaounde, Cameroon.

 

Godiya ga Ngwene Theophilus, Socio-economic Officer, WWF Coastal Forests Programme, Cameroon; Dr. Atanga Ekobo, Programme Coordinator, WWF Coastal Forests Programme Cameroon; da Sylvie Siyam, Shungaban PROTEGE QV.

Information sources

An yi firarrakin ranar 11 ga watan febuware, 2009.