Backgrounder
Menene ayyukan kulawa da ba’a biya, me ya sa yake da muhimanci?
Ayyukan kulawa da ba’a biya ya kunshi taimako da kulawa da mutane ke bayarwa ba tare da an biya su kudi ba. Wanan sun hada da, alal misali, bada kulawa, ayyukan gida, bada karfin gwiwa da rarashi, da kuma debo itache da ruwa. A matakin farko, ya kunshi ayyukan da suka shafi gida da iyali, amma ya wuce taimakon gidan mutum daya kawai, ya hada da taimakon abokai, makwabta, da mutanen unguwa. Ayyukn kulawa sau da yawa ya na fadawa kan gidaje da alumma, musamman manyan mata da yaran mata.
Me yasa za’a damu sai an dauki ayyukan kulawa da muhimanci?
Ayyukan kulawa da ba’a biya ba wai taimako da amfanar wadanda suke samun kulawa ba ne kawai, har ma da alumma gaba daya. Kowa zai iya wadanan ayyukan, misali, za’a iya daukan mai aiki, ana biyan sa. Suna bukatar karfin jiki da tunani dan yin su, sanan akwai tsada in kayi la’akari da lokaci da kake batawa. Ayyukan kulawa sau da yawa na kawo, bata lokaci, ya na kuma kawo tangarda wurin yin aikin da ake biyan mutum, da yin jagoranci, da kuma karin ilimi. Amincewa da aikin kulawa da ba’a biya a matsayin abu mai mahimmanci ga tattalin arziki ga al’ummomi zai ba da damar yin la’akari da shi a matsayin muhimmin abu da zai taimakawa tattalin arziki da zamantakewa.
Ta yaya aikin kulawa da ba’a biya zai ba da gudunmuwa wurin zamantakewa da kuma cigaban tatalin arizikin alumma?
Aikin kulawa da ba’a biya na taka muhimmiyar rawa wurin taimakon mutane, da gidaje, da alumma, yana ba da gudunmuwa wurin cigaban jama’a gaba daya. Yana ba da damar cigaban tatalin arziki ta hanyar samar da jama’a masu koshashiyar lafiya, habaka hadin kan alumma, da kuma tallafawa mutane su shiga jerin ma’aikata.
Su waye ke da hannu a cikin aikin kulawa da ba’a biya?
A duk duniya da kuma nahiyar Africa, aikin kulawa da ba’a biya ya rataya a wuyan mata. A nahiyar Afrika, anyi kiyashi cewa, mata na bada aikin kulawa da ba’a biya sau 3.4 fiye da maza. Aikin kulawa da mata sukeyi ba’a biyan su yawanci mutane basa gani kuma ana raina shi, ya na kuma dakile mu su damamakin da ya kamata su samu suyi wasu alamuran rayuwa da zai na sa ma musu kudi da sauran abubuwa.
Wadana matsaloli aikin kulawa da ba’a biya yake fama da su musamman a yankin nahiyar Afrika?
Aikin kulawa da ba’a biya abun damuwa ne sosai a yankin nahiyar Afrika da sauran wurare saboda rashin adalci wurin daidaiton jinsi. Wadanda suke da hakin aikin kulawa, wanda yawancin su manyan mata ne da yan mata, suna fuskantar kalubale kamar karancin lokaci, karancin samun damar tallafi, ga kuma rashin girmama aikin na su. Wanan na iya haifar da damuwa, gajiya, kebewa wuri daya, da raunin tatalin arziki.
Da yawan mata da basu da kudi suna tsuntar kansu cikin ayyuka masu cinye musu lokaci, da kuma aikace-aikacen gida masu wahalar gaske. Ayuukan kulawa da ba’a biya na alaka da samuwar damuwa, damuwar kwakwalwa, karancin intagataciyar rayuwa, talauci na lokaci, karancin zirga-zirga, rashin lafiya da jin dadi. A cewar wasu bincike da akayi, masu matsakaitan shekaru, wanda suke zaman aikin gida kawai, sun fi nakashashiyar fahimta sau biyar fiye da sauran mata da suke wani aiki, anan ana nufin “nakasashiyar fahimta” shine “shan wahalar wurin tuna abubuwa, koyan sabon abubuwa, mai da hankali, ko kuma yanke hukunci kan alamuran da suka shafi rayuwa.”
Aikin kulawa ba ba’a biya yana kara jadada rashin daidaiton jinsi ta hanyar dakile mata su samu ilimi, aiki, da inganta rayuwar su, galibi ya na takaita su ga karamin aiki, ko karkatace aikin da ba shi da tushe. Yayin da aikin kulawa da ba’a biya yake dakile mata shigar kasuwar neman aiki, a matakin alumma, yana da alaka da gudunmuwar su ga cigaban tatalin arziki da kuma yunkurin rage talauci.
Menene mafita ga rashin daidaton jinsi a cikin ayyukan kulawa da ba’a biya?
Ya dace a hadu a magance aikin kulawa ta bangarori daban-daban, wanda suka hada da gwamnatoci, kungiyoyi masu zaman kansu, da masu aikin zaman kan su, da kuma masu iyali.
Ku kula da masu aikin kulawa da ba’a biya sanan ku kimanta su.
- Gwamnati za su iya tsara manufofi da shirye-shirye da zai na kula da kuma kimanta aikin kulawa da ba’a biya. Wanan zai iya hadawa da fita dan wayar da kan jama’a, shirya taron horar da masu ba da kulawa a cikin gida, da ba da satifiket ko difloma ga masu aikin kulawa. A gida, sauran yan uwa na iya taimakon wadanda suke aikin kulawa da ba’a biya.
Daidaita aiki da rayuwar iyali
- Gwamnatoci na iya aiwatar da manufofin da ke haɓaka damar samun ababen more rayuwa da muhimman ayyukan jama’a kamar wutar lantarki, kiwon lafiya, ruwa, kula da yara, makarantu, da sufuri. Dole ne a tabbatar da cewa kowa na iya samun kulawa cikin sauki.
A samar da kayan aikin zamani don rage nauyin aikin kulawa da ba’a biya
- Rishon zamani, ingin wanki, injin nika, da dai sauran mashinan zamani zasu rage lokaci da da ake batawa wurin yin ayyuka masu bukatar karfi kamar debo ruwa, sarrafa girbi na gida, da kuma debo itace. Wani bincike da akayi a wani kauye da ke kasar Senegal, ya gano cewa samar da hanyoyin bututun ruwa da aka yi kawai ya bawa mata dama sun fara sana’ar kiwon dabobi da kuma shuke-shuke.
Ana yada kyawawan halayen maza ta kamala— arage kallon aikin kulawa a matsayin aikin mata.
- Wakilai na gari da kuma shugabanin gargajiya na iya zama kan gaba wurin sauyan tunanin mutane kan cewa aikin kulawa aikin mata ne kawai. Wanan zai hada da wayar da kan alumma akan bambance-bambance da kallon wariya da ake wa aikin kulawa wanda ya janyo rashin daidatuwa, da karfafa gwiwar maza, manya da yara da sauran yanuwa, jama’ar unguwa, masu sana’a, yan siyasa, yan gwamnati, dattijai, malamai, da kuma kafofin yadai labarai su na fadakarwa akan kyakyawan halin namiji mai kamala.
- Maza za su fi shiga aikin kulawa idan suka san muhimancin sa da kuma tsawon lokacin da zurfin ilimi da yake bukata. Idan da yawa na kallon aikin kulawa a matsayin abu ma’ana, musamman idan wani shugaba da ake ganin girman sa na goyon bayan haka, maza za su shiga aikin kulawa.
- Da yawa ra’ayoyin da mutum ke dauka akan abu suna wanzuwa a cikin gidan da mutum ya taso. Shirye-shiryen gidan rediyo da kuma kyakyawan tsarin sadarwa na iya sauya tunanin mutane da habaka hadin gwiwa akan aikin kulawa ta hanyar tattaunawa da halayar mutane.
Habaka hadin gwiwa wurin aiwatar da aiki tsakanin alumma
- Rage yawan aikin kulawa da ba’a biya da raba ayyukan gida tsakanin yan cikin gidan, tare da kuma yan gwamnati da masu zaman kansu, zai taimaka wurin karfafa mata ta fuskar tattalin arziki saboda za su sami karin lokaci su sadaukar wa kansu, da iyalansu, da aikin da ake biyan su. Kamfen din Majalisar dinkin duniya yankin mata ta HeforShe ya bayar da hanyoyin da maza za su goyi bayan mata kan a samu a daidaton jinsi, da kuma nuna halin kamala ga maza wurin aiki tare da mata dan su kafa sanao’i, su raya iyali, sanan su kyautatawa alumma.
Haɓaka Ranar Kulawa da Tallafawa ta Duniya
- A watan Yuli, 2023, taron koli na Majalisar Dinkin Duniya ta ayana ranar 29 ga watan Oktoba a matsayin ranar kulawa da tallafawa ta duniya domin jan hankalin jama’a akan matsalolin da suke tattare da aikin kulawa da ba’a biya, ta kuma nuna bukatar magance kalubalen da yake wanzan da rashin adalcin daidaita jinsi wurin aikin kulawa da ba’a biya.
Acknowledgements
An samar da wanan ne ta shirin ‘UCARE – Unpaid Care in sub-Saharan Africa‘, wanda ke da kudirin habaka daidaiton jinsi da kuma karfafa mata ta hanayar jadada yin adalci da daidaito wurin raba ayyukan kulawa da ba’a biya da ayukan gida a tsaknin duk mazauna cikin gida a nahiyar kuda da hamadar Afrika. An aiwatar da aikin ne da ahdin gwiwar gidan Farm Radio International (FRI), UN ta Mata, da kuma cibiyar sadarwa da cigaban mata ta Afrika (FEMNET) godiay mai yawa da tallafin Global Affairs Canada.