Rikici da mata da cutar Kanjamo (HIV/AIDS)

Lura ga mai watasa shiri

Rikici da mata ta shafi fyade da tilasta jima’i, nuna karfi ko wulakanci domin jima’i, harma da mumunar ta’ada, kamar kaciyar mata da tilasta auren wuri..Irin waddan nan rikicin na kara yawan haduran mata na kamuwa da cutar kanjamo ta tilsata jima’i kai tsaye ko saka musu tsoro, wanda ke rage kwazon mata wurin nemar yarjejeniyan yanayi da ake jima’i da amfani da robar jima’i.Rikicin na shafar lafiyar jiki, hankali da cigaban zaman takewa.

Mata da yawa na bayar da rehotun halin rikicin da suka shiga dangani da kamuwa da cutar kanjamo ko kuma yarda da gwajin cutar kanjamo.Wannan rikicn zai iya dagula kwazon mata wurin nemar jinnya da kullawa ko kuma ta tsaya wa jinnya da maganin anti-retroviral(ARV) Wasu mazan ma na taimaka wa kansu ta jinnya abokiyan zaman su da AVR..
Rikic da mata ya samun gindin zama sosai, acikin kasashe masu tasowa da waddan da suka ci gaba.A unguwanin da dama mata da suka fadawa rikici sunkai kashi 50 bisa dari.

Kamar yanda rubutun ya nuna ,akwai alaka mai karfi tsakanin rikici da mata da rashin daraja hakin su,irin su damar ilimi, dammar bayana ra’ayin su,damar malakar kadarori, da dammar samun walwallan motsawa..Rikicin da mata na samun makamashi da goyon baya wasu ka’idodi dake hana mata samun waddannan hakin mutanen.

Idan zaka rungumi wannan rubutun ga masu saularen ka na gida, zaka so ka yi fira da wakilan kungiyoyin mata na kasa akan radiyo ,watakila ka kara da shiri kira a layin waya. A cikin shekara 1999, Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 25 ga watan Nawamba ta zamo ranar kawadd da rikici da mata.Zaka so ka gudanar da shiri da dama da suka danganci hakan.

Rubutunsa

Dominic Mutua Maweu:
Barkaya kai mai saulare, Gidan radiyon Mang’elete FM nn central Kenya ke nan kuma suna na Dominic Mutua Maweu. A yau, zan gabartar muku.da shirin Imanyiliile wanda na tabbatar ya taimake ku sosai kuma kuna masu so sa! A cikin harshen Kikamba , Imanyiliile na nufin “Yi hatara, akwai hadari!”

A yau, ian son mu dubi yanda rikici da mata ke kawo yaduwan cutar kanjamo.Idan muka ce rikici da mata abin nufi shine, rikici,fyade,da taken hakin mata.Idan muka ce hakin mata,abin nufi shine hana wa mata dammar samun ilimi lokaci daya dace,da kuma dammar mata na yin bayani akan tasu ra’ayi akan duk wani abin da ta shafe su don kan su, unguwan su da kasar su.

Ya kai mai saulare,sanin kan ka ne cewa, makami mafi dacewa da yaki da wannan cutar shine soyyaya. Maza! Idan lele muna son matan mu, da suka hada da kannen mu mata da iyayen mu, baka jin cewa zamu daina fada dasu a gidajen mu, gun aiki da kuma kasuwannin mu? Baka jin mun daina musu fyade da kuma hana so hakin su?.

(Wakafi) Ina son kuji kalamu daga Rhoda Maende, wata mace daga gundumar mu, wadda mai bayar da shawarwari ne kuma shugaban kungiyan mata da aka sani da suna Makueni Women’s Regional Assembly.A cikin jawabin ta,inda take zance ga jama’ar gundumar Makueni da suka taru a garin Makindu domin bikin ranar AIDS ta duniya wato 12 ga wata Januwari din shekara 2005.

Shude sautin ayiri, sai kayi kasakasa da shi ayayin da take jawabi

Rhoda Maende:
Hamjambo, Hamjambo tena kuma yaya kuke? Suna na Rhoda Maende daga Makueni.Ina tare da wata kungiya mai suna Makueni Women’s Regional Assembly. Daya a cikin ainihin ayukan da neke yi shine in tabbatar mata sun samu hakin su, yara ma sun samu hakin su, kuma an darajar maza. Yau, ina son nayi zance akan anobar cutar kanjamo . Ina son inyi magana game da yanda yake da alaka da rikici da mata ko duk wani irin take hakin matan aure da marasa aure.Fadace fadace acikin gidajen mu da yi wa matan mu fyade na kawo yaduwar cutar.

A daina rikici da mata! Ama sivyo akina mama ko “ba haka bane,ya ke mama ta”? Muka ce a daina rikici da mata.

Akwai mata dake aiki a mashayar mu. Ko wani aiki aiki ne kuma mace na da damar tayi aiki a ko’ina. Sabili da tana aiki a mashaya ba shi ke nufin kowani kostoma dake zuwa nan zai iya kai mata hari ba.Idan naji kowani irin labari na kai hari ga waddan nan mata ko suna dauka su ala tilar.Na kai su kotu kuma za’a sasu gidan yari.Domin lefi ne.

Ko wata mace na bukatan a daraja ta akan abin da take yi..Tana da dammar ta kula da kanta,to mai zata ci idan bata yi aiki ba, muna cewa adaina kai musu hari kuma duk mace a daraja ta.Idan mace ta yarda tayi tafiya da kai, ba damuwa! amma adaina rikici da su!

Shude sautin mutanen na dakiki biyar, sai ka fito

Dominic Mutua Maweu:
Da fatar kunji abinda wannan shugaban ta fada.Ina son kuyi tunanen sa ta haka. Take hakin mata, samman, dammar samun ilimi, shi yafi komai muni wurin yada cutar kanjamo.sabili da ilimi kadai ne mutun zai nemi sanin cutar da illar ta. Kuma ta ;yancin magana ne mace zata iya fadar, “Ina son nayi amfani da robar jima’i,” ko da ya kasance da mijin ta take magana.

A karshe,haka ya kamata al’uma suyi idan an yi rikici da mace: Da farko,kayi kokarin shiga tsakani Idan ka gano akwai cuta.a harakar. Na biyu, saulari kayi jawabi ba tare da ka ga lefin wanda aka cuta ba. Na uku, kayi magana ga mutane game da rikici da mata; ka samar da fagen muhauwara akan rikici da mata a unguwan ka.Na hudu, ka tuna siri nada mmuhimmancin gaske, tattauna sha’anin da suka shafi duk wani rikici. Na biyar, ka hada taron jama’a na samu saduwa da ‘yan sanda da kuma gwamnati kuma ka nace wurin nemar a kyautata wa mata da aka muzguna musu .Sama da duka ,Ka taimaka wa hakin mata su rayu lafiya kuma amintantu tsakanin al’uma.

Na gode, a yau ,bara mutsaya a nan. Suna na Dominic Mutua Maweu, ni na shirya kuma na gabatar da shirin.Kamin sake saduwa da ku, sai an gan ku, ku kiyaye kan ku!

Acknowledgements

Gudunmuwa: Dominic M. Maweu, producer and presenter, HIV/AIDS Program, Radio Mang’elete, Mtito Andei, Kenya.
Nazari: Rebecca Hodes, D.Phil candidate in the History of Medicine, Oxford University,
Dora hankali: HIV/AIDS in the Media; and Mawethu Zita, Driven Force Co-coordinator and Artistic Director, Other Half Project Team Member, Ikhwezi Lokusa Wellness Centre, East London, South Africa

Information sources

Rosemarie Muganda, undated. Violence and the threat of HIV/AIDS. African Women and Child Feature Service. http://www.awcfs.org/new/features/health/hivaids/128-violence-and-the-threat-of-hivaids
Harvard School of Public Health, 2006. HIV/AIDS and Gender-Based Violence (GBV)
Literature Review. http://www.hsph.harvard.edu/pihhr/files/resources_and_publications/literature_reviews/Final_Literature_Review.pdf
UNAIDS, undated. Stop Violence Against Women – Fight AIDS.
http://data.unaids.org/Publications/IRC-pub07/jc1184-stopviolence_en.pdf Human Rights Watch, 2003. Policy Paralysis: A Call for Action on HIV/AIDS-Related Human Rights Abuses Against Women and Girls in Africa. http://www.hrw.org/reports/2003/africa1203/