Yazo kamar wuta: Kula da cutar burtuntuna ta dankalin turawa a Nijeriya

Noma

Lura ga mai watasa shiri

Bayanin kula ga Mai Gabatarwa

Dankali shine abinci na hudu da aka fi so a duniya. Bashi da sinadirin sodiyom, kolestrol, maiko, kuma yana da babban mataki na bitamin C, sinadirin potashiyom, ayon, bitamin B6, da kuma fiba. Ana iya sarafa dankali zuwa abinci kala-kala, kamar abun ciye-ciye kamar soyayan dankali da kuma kirips.

A kasar Nijeriya, mafi yawan noman dankali ana yin sa ne a yankin Jos ta Jahar Plateau, yayinda yanayin kasar wurin ke samar da sanyi da ake noman dankali.

Dankali na samar da fa’idodi da dama ga manoma da masu amafani dashi. Suna da sinadiran gina jiki sosai, suna samar da kudin shiga, nomansu ba wahala, basa bukatar katon fili, suna da saurin dahuwa ba kamar sauran amfanin gona ba, basa bukatar sarrafawa bayan girbi.

Wanan shirin yana bada labarin manoma masu karamin karfi dake Jos, a kasar Nijeriya wanda suka wahala a hannun cutar burtuntuna ta dankalin turawa, daka bakin su. Za mu karu daka labarinsu da kuma kokarin da sukeyi domin kariya da kuma yakar cutar. Dadin dadawa, kwararin masana guda biyu yan garin, sun bamu gaskiyar lamarin cutar: yanda zaka gane ta, da hanyoyin kare ta ko yakar ta ta amfani da sinadirai ko a zahiri.

Wanan shirin anyi shine akan ainihin tattaunawa da akayi da mutane. Zai iya zama abun dogaro wurin binciken ka ko rubutun wani shirin a wani bangaren a unguwar ku. Ko kuma kayi amfani dashi a gidan rediyon ka, ta amfani da masu hawa kan murya su wakilci masu Magana. Idan haka ne, ka tabbata ka gayawa masu sauraro tun daka farkon shirin cewa, ba ainihin mutanen da aka tattauna dasu bane, kawai kayi amfani da masu hawa kan muryoyi ne.

Zaka iya mayar dashi madubin dubawa, ka futa ka samo mutane daban-daban da suke cikin harkar dankalin ka tattauna dasu.

Idan ka kirkiri shirin ka akan dankalin turawa, ka tattauna da manoma, masu saye da sayarwa, masana harkar abinci, malaman gona, da kuma sauran masu ruwa da tsaki a unguwar ku. Zaka iya tambayar su:

  • Ana shuka dankalin turawa a unguwa ku? Idan A’a, toh me yasa?
  • Menene manyan kwaruka da kuma cututuka da suke kawo kalubale ga noman dankali a unguwar ku? Wana hanya ce mafi inganci da kuma arha da manoma zasu yi amfani da ita domin su shawo kan kalubalen?
  • Wadanan ayuka ne ake dasu domin tallafawa manoma suyi maganin kwari da cututuka?

An kiyasce lokacin wanan shirin, hade da take, gabatarwa, da kuma sallama ya zama minti 20-25.

Rubutunsa

MAI GABATARWA:
Barkan mu dai, masu sauraro, muna muku maraba a cikin wanan shirin. Sunana _____.

Yau, zamuyi Magana ne akan cutar buntuntuna ta dankalin turawa a Nijeriya. Munyi tattaki har zuwa garin Jos, a arewacin kasar nan. Zamuyi hira da manoma da masana mazauna garin, domin jin tabakain su a game da cutar da kuma yadda sukai kokari suka yake ta suka sha kanta.

Duk da dai ansan yan Nijeriya da san doya, dankalin turawa yana da farin jinni sosai kuma ana cin sa sosai a Nijeriya. Hasali ma, shine abinci na uku mafi farin jinni a jerin abincin da ake tonowa bayan doya da rogo.

A yau, kusa da kadada dubu dari uku na gona ke samar da ton sama da miliyan daya na dankali a kowace shekara a Nijeriya. Wanan albarkar gona za’a iya habbaka shi, amma manoma na fuskantar kalubale da yawa. Kalubale da suka hada da yanayi mara kyau, kwari, da kuma cututuka, tare da kalubale na zamantakewa kamar rashin ilimi, rashin kudi, sifiri mara kyau, da kuma karancin wurin ajiya, da kuma wuyar samun iri mai juriya (Abun lura na Edita: ana kiransa da irin dankali).

Daya da ka cikin abubuwan da ke kawo karancin amfanin gona itace cutar burtuntuna. Kusan kowane manomi da yake shuka dankali yana da labari da zai bayar na wanan cutar ko ta shafe masa gona ko ta shafe masa rabun gona sa.
Yau, zamu tattauna da manoma da kuma masana a wuraren Jos, a Jahar Plateau a kasar Nijeriya, garin da yafi ko ina shuka dankali a kasar.

Amma farko, zamuyi hira da Dr. Daniel Lenka, wanda zai bamu takaitacen bayani akan noman dankali a Nijeriya. Dr. Lenka malami ne a Jami’ar Jos, sashen noma na Jami’ar, yayi kuma aiki da Cibiyar bincike na amfanin gona sashen dankali. Barka da zuwa Dakta.

DR. LENKA:
Barkan mu dai.
MAI GABATARWA:
Ko zaka iya bamu takaitacen bayani akan noman dankali a Nijeriya?
DR. LENKA:
Eh kwarai, mutanen Jamus ne suka shigo da danakali Nijeriya shekaru 90 da suka wuce a 1930. Dankalin turawa yana cikin jeirn amfanin gona da suke girma a wurare da suke da tudu. A Nijeriya akwai wurare biyar ko shida da suka fi dacewa da noman dankali.
MAI GABATARWA:
Toh, kana bukatar wurin da yake da tudu saboda yanayin wurin yafi dalma-dalma?
DR. LENKA:
Eh hakane, a wurare masu tudu, yanayin wurin na da sanyi. Dankali yana san yanayi da bai wuce digiri 5-15 na maunin Selshiyos dan ya girma yayi kato. Idan zaka iya tsayar da yanayin na kamar wata biyu, zaka iya noman dankali. Yanayin da yafi dacewa shine digiri 10 maunin selshiyos.
MAI GABATARWA:
Amma wanan yanayin kamar yayi kasa sosai. Shin akwai wurare irin wanan a kasa mai zafi kamar Nijeriya?
DR. LENKA:
Eh, kamar yadda na fada a sama, akwai wurare biyar ko shida a Nijeriya da suka fi dacewa da noman dankali a Nijeriya. Amma kaso 95% na noman dankali ana yin sa ne a Jos Plateau. Shi Jos Plateau yana da karfin noman ton 20-30 na ko wace kadada daka shuka ton biyu na irin dankali. Amma saboda kwari, cututuka da wasu abubuwa, a yanzu haka muna noma kasa da ton 10 a ko wace kadada a Nijeriya.
MAI GABATARWA:
Mun gode Dakta. Ka bamu takaitacen labari, to amma menene gaskia lamarin da ke kasa a yanzu?
DR. LENKA:
Eh, albarka tana raguwa saboda kwari da cututuka. Akwai cututuka biros da bakteriya, amma wada tafi ko wace kawo kalubale itace cutar burtuntuna, cutar funfuna ce da take wa dankali illa.

Saboda cutar funfuna ce, idan yanayin wurin na da kyau, cutar tana yaduwa da sauri. Tana kama ganye da sandan shuka, ta sanya su su koma bakake. Idan babu ganye, shukar baza ta iya yin abinci dakanta ba sai ta mutu.

A sabon karnin nan, cutar burtuntuna ta dankali an same ta ne a shekara ta 2014 a karamar hukumar Bokkos, yankin Jahar Plateau. Bokkos ita take samar da kaso 40% na noma dankali a Nijeriya amma haka cutar ta yiwa manoma illa. Kusa da kadada 500 ta gona ne suka kamu a cikin sati guda, haka ta yadu a Jahar gaba daya babu inda ya tsira. Asara kudin da akai ba karama bace-ba wai kawai a wurin shuka ba, harda rasa rayuwa dan adam. Manoma da yawa suka dau ransu da kansu bacin sun ziyarci gonar su suka ga sun rasa komai a kiftawar ido.

MAI GABATARWA:
Wanan abun takaici ne.
DR. LENKA:
Eh, sosai ma kuwa. Gwamnati ta kawo dauki, amma cutar ta yadu da sauri da gwamnati ba ta iya tsayar da yaduwa ba. Yawancin dankalin basuyi girman da za’a siyar dasu ba.
MAI GABATARWA:
Mun gode Dr. Lenkan. Zamu dawo gurun Dr. Lenkan nan da dan lokaci kadan a cikin shirin namu. Amma yanzu, bari muyi hira da manoma da suka hadu da cutar burtuntuna. A farko, muna tare da Bob Ezekiel, manomi ne da ya dade yana noman tun bayan gama makarantar sakandiri. Barka da zuwa wanan shirin Ezekiel.
BOB EZEKIEL:
Na gode. Nayi murna da zuwa na wanan shirin.
MAI GABATARWA:
Ko zaka iya gaya mana yadda ka shigo noman dankali?
BOB EZEKIEL:
Gado Mukai. Iyaye na manoma ne, kuma ina da ra’ayi. Ina gama makaranta, sai na bisu.
MAI GABATARWA:
To yaya tafiyar take?
BOB EZEKIEL:
Lafiya lau da yan kalubale kadan. Muna iya ciyar da kanmu mu kuma siyarda kadan mu samu kudi. Na siyar da dakali na kamar dubu 50,000 (wurin $150 ta amurka) a girbin da ya wuce.
MAI GABATARWA:
Menene kalubalen ka?
BOB EZEKIEL:
Akwai kalubale da yawa. Ni dai, kalubale na daya shine samun iri. Idan ka samu iri mai kyau tun farko, zaka fara irga ribar ka. Amma, wasu irin da na samu basu da kyau sosai wanan ya taimaka wurin samun albarkar gona kadan. Kudi ma matsala ne, saboda yana iya taba abubuwa da yawa: lokacin shuka, kyan irin da zaka samu. Wanan yana taba amfanin gonar ka. Kamar takin zamani, zaka sa ne a wasu lokuta na musamman, idan baka da kudi da zaka zuba a lokacin da ya dace, baza ka iya samun albarkar gona da kake sa rai ba.

Kwari da cututka suma manya abubuwa ne. A wata shekara, beraye suka cinye mun rabun gona ta. Haka kuma wasu a wani karin kwari suka farma wa gona ta. Amma babbar matsala itace burtuntuna, wace take zuwa idan anyi ruwan sama sosai.

MAI GABATARWA:
Ko zaka bamu labarin gamuwar ka da cutar burtuntuna?
BOB EZEKIEL:
Na lura akwai digon baki a jikin koren ganyaye na. Kafin in ankara, ganyen sun bushe sun mutu. Anyi ruwan sama sosai a lokacin.
MAI GABATARWA:
Ko ka samu ka shawo kanta?
BOB EZEKIEL:
A lokacin ban samu ba. Amma, an fada mun cewa inyi amfani da wani sinadiri sati uku kafin shuka. Ance ina zubawa shuka ta duk sati har sai sun kai girbi. Zan ga amfanin sa wanan girbin.
MAI GABATARWA:
Mun gode, Mista Ezekiel. Nagaba, zamuyi hira da wani manomi, Joseph Dangyang, wanda yayi shekara 10 yana noma. Barka da zuwa wanan shirin Mista Dangyang. Ko zaka iya fada mana yadda ka fara noman dankali?
JOSEPH DANGYANG:
Nagode. Eh, an haife ni cikin manoma na kuma dau sha’awar noma tun ina da karancin shekaru. Nayi noma abubuwa da yawa, amma dankali shine wanda nafi jin dadin nomawa.
MAI GABATARWA:
Ko akwai kalubale wurin noman dankali?
JOSEPH DANGYANG:
Wani lokaci, muna samun kalubalen iri. Wasu suna da cututuka-a ido lafiya lau, amma idan ka shuka su, zasu kai wani girma sai su mutu. Wanan yana nuna ma irin na da matsala. Amma girbi na mafi muni shine wanda cutar burtuntuna ta janyo. Cutace sananiya da mu manoma muke fama da ita.
MAI GABATARWA:
Ko zaka iya bayyana mana yadda cutar take?
JOSEPH DANGYANG:
A kari na farko, ganyayen suna samun digon baki, sai suyi yaushi su mutu. Wanan yana kawo cikas wurin girman shukar.
MAI GABATARWA:
Wana mataki ka dauka wurin shawo kan wanan cutar?
JOSEPH DANGYANG:
Sanda na gano cutar, sai na lura cewa tazo ne lokacin da ake ruwan sama mai yawa, garin kuma yayi sanyi. Toh sai nayi shuka da wuri kafin a fara ruwan farko, saboda na guji ruwan. Cutar burtuntuna na zuwa ne wurin watan Yuli ko Agosta, idan ka fara da wuri, zakayi girbin dankalin ka kafin lokacin cutar ta fara.
MAI GABATARWA:
Yaya ka lura da cenjin yanayin garin tunda ka fara noma a rayuwa ka?
JOSEPH DANGYANG:
Shekara ta 10 ina noma, kuma yanayi ya cenja. Ina ganin kwari a gona ta sosai. Yawanci da beraye ne wanda nake yakar su da maganin beraye. Ina ganin sauyin yanayi ke sawa cutar burtuntuna ke nasara.
MAI GABATARWA:
Mun gode, Mista Dangyang. Bara mu kira masanin mu yayi mana Karin bayani akan alamomin cutar burtuntuna. Gbenga Oni kwararen mai bincike ne da yayi shekaru sama da goma akan noman dankali da kuma yaki da cutar burtuntuna. Yayi aiki a cibiyoyi da yawa da kuma cibiyar binciken kayan gona da kuma hukumar cigaba ta Jamus, GIZ. Barka da zuwa shirin mu, Mista Oni.
GBENGA ONI:
Nagode.
MAI GABATARWA:
Munji illar cutar burtuntuna akan noman dankali a Nijeriya. Me zaka ce akai?
GBENGA ONI:
Eh, cutar burtuntuna taza ma kamar cin wuta; wanan itace hanyar da za’a iya kwatanta ta. Wuta da tazo a bazata. A matsayi na na mai bincike da kungiyoyin cigaba na duniya, mun dau matakai daban-daban dan taimakawa manoma su inganta amfanin gonar su-shuka iri mai kyau, ko kuma inganta cinikaiya daka gona zuwa kasuwa. Duk zamuyi wadanan abubuwa, amma cutar burtuntuna zata zo kamar cin wuta. Ka auna wata rana ka tashi kawai kaga kamar wuta taci kan amfanin gonar ka, ta kona ganyaye.
MAI GABATARWA:
Kuma ka rasa komai.
GBENGA ONI:
Ba wai haka ba. A wurare da ake da cigaba, idan aka kusa girbi, sai ka yanke ganyayakin da suka tabu ka cire bangaren da ya tabu, kada cutar ya kai ga kasar wurin. Wanan yana sa shukar ya zauna a kasa Karin wani lokaci har fatar tayi tauri tayi karfi. Amma, a nan Nijeriya, idan manoma suka ga cutar burtuntuna, sai suyi girbi da wuri. Idan har kai girbi da wuri, zai iya kawo illar ga naman dankalin. Sai ya zama bashi da kama, da sauran su. Wanan yana da tasiri in anje kasuwa domin dankali masu kama wana iri basa kawo kudi mai kyau.
MAI GABATARWA:
Mun tattauna da manoma a baya da suka sha wahalar cutar burtuntuna kuma kamar gano cutar da wuri zai iya taimakawa a ceto amfanin gonar. Ta ya zaka gane cutar burtuntuna ta kusa? Menene alamunta?
GBENGA ONI:
Ganyan na lankushewa, ya koma baki, ya kuma kone a dare daya. Gonar ka zata iya koma daka koriya shar a dare daya zuwa kamar wani ya sa mata wuta.
MAI GABATARWA:
Mun gode, Mista Oni. Muna yiwa Dr. Lenka maraba. Dakta, menene abubuwan da ke kawo cutar burtuntuna? Me yake sa wasu gonar suke saurin kamuwa da cutar?
DR. LENKA:
Cutar burtuntuna na zuwa ne daka jikin dankalin. Idan jikin dankalin ya kamu, akwai kuma wuri mai kyau da funfuna—kamar danshi na kwanaki da yawa-digo-digon mai kama da auduga zai cigaba.

Digon, zasu iya tarayya akan kayan gona, bangaren da ya kamu da cutar a jikin shukar, da kuma kasar wurin. Saboda kamar auduga suke, suna yawo a iska da sauki su kama sauran shukokin.

Wani sa’in kuma yadda akai shuka ne yake kirkira hanyoyin da cutar ke tasiri. A misali, manoman mu, na shuka dankali sau biyu a shekara, wanan yana nufin tushen zasu fi saurin kamuwa da cututuka. Muna kuma cinkusa wuri a lokacin shuka.

MAI GABATARWA:
Me cunkosa yake nufi anan wurin?
DR. LENKA:
Idan an shuka irin kusa da juna, wanda ya ka janyo gumi ya kirkiri yanayi da ya dace da cutar burtuntuna ta yadu. Wani tsarin shuka da yake janyo cutar burtuntuna shine hadakan shuka, idan kayi hadakan kusa da juna. Wanan yana kara gumi da zai janyo cutar ta nuna.

Wani dalili shine chanjin dumama yanayi na duniya. Watakila chanjin yanayin yasa funfuna ta samu karfin gwiwa.

MAI GABATARWA:
Mun gode, Dr. Lenka. Yanzu bara mu tattauna da wasu manoman. Nandal Binkur ya cigaba da noma da y agada a wurin iyayen sa, ya fi shekara goma yana noma. Barka da zuwa wanan shirin, Mista Binkur.
NANDUL BINKUR:
Nagode.
MAI GABATARWA:
Ya akai ka fara noman dankali?
NANDUL BINKUR:
Na dade ina sha’awa saboda iyaye na manoma ne.
MAI GABATARWA:
Me ka lura da noman dankali?
NANDUL BINKUR:
Ga dadi ga daci. Idan kasamu albarka, yafi komai dadi, idan kuma baiyi ba, akwai bacin rai. Ina son noman dankali domini dan ka shuka daya, ba guda daya kawai zaka girbe ba. Saboda haka idan kana irga ribar daka ci daka irin dankali daya, zaka ji dadi a rai saboda kasan bakayi wahala a banza ba. (DARIYA)
Ina murna sosai—Na samu albarka noma da tafi kowace wanan shekarar a wurin samun kudi, so akwai dadi, wanan ne girbin da nayi da kaina na samu riba kuma.
MAI GABATARWA:
Abu yayi kyau sosai. Kayi Magana cewa akwai dadi akwai daci. Ka taba samun kalubale a noman dankali?
NANDUL BINKUR:
Eh, abun da muka fuskanta da da yanzu da banbanci. Yawancin abun duk abun da ka shuka yana kamuwa da cututuka. Wanan ya kawo cikas wurin girbi.

Cuta da tafi suna itace burtuntuna. Na lura idan shuka ta fara girma ganyayen sai suyi yaushi su mutu. Yana faruwa ne a tsakiyar damuna.

MAI GABATARWA:
Yaya kake shawo kan cutar?
NANDUL BINKUR:
An bani shawara inyi shuka da wuri, lokacin farkin ruwan sama. Kasa idan ruwan farko yazo, yana daukan lokaci kafin ruwan yana zuwa sosai. Idan kayi shuka a farkon ruwa, shukar ka tayi girma ta isa girbi a lokacin da cutar burtuntuna zata zo.
MAI GABATARWA:
Shin akwai wani abu daban kuma kake yi?
NANDUL BINKUR:
Eh toh, wasu suna mafani da sinadirai suyi maganin cutar, amma ba ko da yaushe yakeyi ba, saboda haka bani da tabbas akan wanan. Ni dai shuka da wuri yana mun.
MAI GABATARWA:
Shin yanayin garin ya cenja tun da ka fara noma? Shin hakan ya janyo cututuka?
NANDUL BINKUR:
Da yawa ya cenja tun da na fara noma shekaru goma da suka wuce. Yanayi ya cenja sosai kuma ina tunani yakawo kwari da cututuka. Yanzu yanayi kuma baza ka iya canka yadda zai ka sance ba. A da zaka iya cewa ga lokacin da za’a fara ruwa, amma yanzu yana daukan lokaci.
MAI GABATARWA:
Mun gode, Mista Binkur. Yanzu muna kara maraba da Gbenga Oni cikin shirin. Zai fada mana yadda yafi dacewa a shawo kan cutar burtuntuna.
GBENGA ONI:
Barkan mudai. Idan kayi tunanin yadda man fetur yake ga mutanen Niger-Delta a Nijeriya, toh haka dankali yake ga mutanen Jahar Plateau saboda saboda yadda yanayin Jahar yake. Saboda haka ka auna illar idan aka samu asara a wurin girbi. Yana da muhimanci mu samo rigakafi akan cutar nan mu kuma sanar da manoma.

Akwai hanyoyi da za’a iya shawo kan cutar—kai tsaye da kuma dabaru. Hanya ta farko shine amfanin da iri mai kyau, mara dauke da cututka. Irin da ya kamu da cuta aka ajiye dan amfani dashi lokacin shuka a gaba suna ab una farko da suke kawo cutar.

Wata hanya shine itace kasa mai kyau. Ka tabbata kayan noman ka a wanke suke haka kuma takin zamanin ka da kasar ka bas a dauke da cututuka. Kada kayi shuka kusa da juna.

Haka kuma shuka akan lokacin da ya dace. Na lura wata manoma tace tana noman tane a lokacin da ba’a ruwa. Wanan yana da kyau, amma zaiyi tsada sosai da kuma cin lokaci wurin samun ruwa.

MAI GABATARWA:
Wana lokaci ne ya dace ayi shuka?
GBENGA ONI:
Kayi shuka da wuri, tsakanin watan Maris da Mayu, saboda kayi girbi kafin a fara ruwa mai yawa a lokacin watan Satumba da Oktoba. Ka sa a rai cewa, yanayi zai iya cenjawa a kowane lokaci, ruwa zai iya zuwa daka baya, saboda haka kayi shirin ko ta kwana na ban ruwa kar takin zamanin ka ya kona ma shuka.
Akwai kuma wani irin dankali da yake saurin nuna a kasa da watanin uku. Wanan shima zai sa dankali ya isa girbi kafin ruwa mai yawa.

Sanan akwai hanyar amfanin da magnin funfuna da ya dace. Akwai magungunan funfuna kadan da suke da tasiri, zaka iya Magana da malamin gona na unguwar ku kaji shawara maganin da zai baka.

MAI GABATARWA:
Kayi maganar amfani da maganin yanda ya dace. Mai kake nufi da haka?
GBENGA ONI:
Kamar rigakafin Poli ne. Dole ka bawa yaro a lokacin da ya kamata. Ba zaka bawo yaro ba yana da shekaru kayi tsamani yayi aiki, saboda kayi latti. Akan cutar burtuntuna, rigakafi yafi magani. Zaka fesa maganin funfuna kafin ruwa ya fara in ba haka ruwan zai share shi.

Daka karshe, ya kamata mu ilimantar da manoma akan wanan cutar da kuma sauran abubuwan da ke kawo wa gonar su barazana, su san hanyoyin noma da suka dace.

MAI GABATARWA:
Mungode, Mista Oni. Dr. Lenka, ko zaka kara wani abu akan abun da Mista Oni yace?
DR. LENKA:
Eh, ina so in kara akan lokutan da ya dace ayi a fesa maganin funfuna. Da zarar shuka ta fara tsiro, ka fara fesa magani. Ya danganta da irin kamfanin da kake amfani dashi, amma yawanci ana feshi ne duk bayan sati biyu har tsawon sati shida kafin girbi, ka guji feshi kusa da girbi kuma.
MAI GABATARWA:
Zaka iya amfanin da maganin funfuna a lokacin da cutar ta kai hari?
DR. LENKA:
A farkon lokacin da ka gano funfuna a yayin da ka fara ganin digo-digo akan ganye amma kafin ya koma baki, zaka iya feshi akan wuri da ya tabu, dan ka kashe funfuna da ta janyo cutar. Idan kaci nasara ta wanan hanya, zaka samu ramuka ajikin ganyaye. Amma idan ganyen ya mutu, toh babu alamun nasara.
MAI GABATARWA:
Mungode, Dr. Lenka. Mun zo karshen wanan shirin na wanan rana.

Da alamu cutar burtuntuna na yaduwa da sauki. Amma idan aka rage yanayi da yake sawa tana tasiri, ta hanyar shuka da wuri da gudun ruwan sama mai yawa, shuka iri mai kyau, amfani da iren da suke saurin nuna, amfani da hanyoyi masu tsafta, da kuma feshin maganin funfuna a lokutan da suka dace, manoma na iya cimma alabarkacin noma mai kyau.

Ina fata wanan bayanan sun taimaka muku a ganakin ku. Allah ya bada sa’a!

Acknowledgements

Gudunmuwa daka: Ted Phido, maubuci, The Write Note, Legas, Nijeriya
Tantancewa: Lucas Garba, Darekta malaman gona, Plateau State Agricultural Development Programme, Jos, Jahar Plateau.

Wanan aikin an dauki gudanar dashi ne daka gudumuwar kudi da “Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit GmbH” (GIZ) ya bayar, wanda suke gudanar da cibiyar “Green Innovation” tare da hadin gwiwar AFC Agriculture and Finance Consultants.

Information sources

Dr. Daniel Lenka, malami ne a Jami’ar Jos a sashen karatun gona, Febweru 9, 2020
Bob Davou Ezekiel, manomi, Jahar Plateau, Febweru 4, 2020
Joseph Dangyang, manomi, Jahar Plateau, Febweru 4, 2020
Gbenga Oni, kwarare mai bada shawara ne, ACCEPT (Kungiyar hadakai ta noma-da koyar da ilimin yadda za’a warware rikici), kuma tsohon manomi ne, A Cibiyar Bincike ta kayan gona da ake tonowa, Febweru 6, 2020
Nandul Edward Binkur, manomi, Jahar Plateau, Febweru 4, 2020