Lura ga mai watasa shiri
Abun lura ga masu gabatarwa
Korona ta cigaba da zama hadari matuka ga lafiyar mutane a duk duniya. Yanzu da aka samu rigakafi, kana da dama da zaka karfafawa masu sauraron ka suje su karbi rigakafi ta hanyar:
- Amsa tambayoyin su ta cikin girmamawa da kulawa akan rigakafin Korona.
- Samar da bayanai na gaskia da hakika akan rigakafin.
- Karfafawa masu sauraron ku gwiwa suje su karbi rigakafi ta hanyar yada maganganun wadanda suka karbi rigakafin a unguwanin ku wanda suka shirya su zama zakararun masu tallan rigakafin Korona.
- Kara tabatarwa masu sauraron ku cewa rigakafin Korona bata da matsala kuma tana da inganci.
Bayanai da sakoni akan Korona bai ka mata su tsaya akan shirye-shiryen ku na lafiya ba! Zaka iya tallan rigakafin KORONA ta cikin sauki da inganci ta hanyar watsa wadanan jerin talaluka guda 24 a cikin shirye-shiryen ku—wanda suka hada da labarai, wake-wake, kasuwanci, wasanni, da kuma shiryen-shiryen addini—da zai kai ga masu sauraro da yawa.
Ka dan dau lokaci kayi bitan wadanan talaluka ka mai dasu daidai da yadda tashar ka ke watsa kala-kalan shiryen-shiryen ta. A misali, wasu tallan anyi su ne a kasuwa, amma za’a iya yinsu a filin kwallo ko wurin wake-wake, ko a opis, ko filin gona ko kuma a wurin ibada.
Hakanan zaka iya cenja shirin dan yayi daidai da al’ummar ku ta:
- Cenja sunayen yan wasan zuwa sunayen gida da aka saba dasu,
- Yin amfani da sunan gidan rediyon ku da aka sanku dashi (rubutun ya nuna: Rediyo XXX),
- Yin amfani da kalmomin da aka fi sani a alumma ga masu sauraran ku (misali, masu sauraranku zasu iya kiran COVID-19 da wani suna kamar “KOVID” ko “Korona”, da
- Tabatar da cewa labaran da ka bayar suna tafiya hannu da hannu da shawarwarin da maaikatan lafiya na unguwani suke bayarwa.
Domin kirkira naka tallan, ka tambayi masu sauraro suna bada labarin abubuwan da suka faru a yayin da suka je yin rigakafi sanan ka nemi izinin su dan ka dau muryar su dan yadawa, sai ka hada su a cikin tallan da kakeyi. A cikin hirar, ka tambayi sunan su, shekarun su, ya akai akayi musu rigakafi, sanan yaya suke ji yanzu. Ingantattun labarai irin waɗannan na iya yin nisa sosai wajen gamsar da masu sauraron ku cewa rigakafin suna da aminci da tasiri.
Rubutunsa
Talla 1: Ka sanya takunkumin fuska sanan ka sanya yadda ya ka mata
Annobar Korona ba karamin wahalar da mutane tayi ba—ahaka kuma bata kare ba. Amma kada ku karaya! Dole mu cigaba da jajircewa mu tsaya wa juna sanan mu kare abokanmu, da yan’uwa da alumma gaba daya.
Saboda haka, ko an maka rigakafi, ka cigaba ta sanya takunkumin fuska da zata rufe maka hanci DA baki. Kafin takunkumin fuska ya taimake ka, sai ta maka cif-cif a kumatu da hanci sanan da kasan habar ka. Idan an sa ka takunkumin fuska daidai, za’a ji bata da takura.
Ka sa takunkumin fuska da yayi maka daidai a fuska, sanan kaje ka karbi rigakafi.
Gaba dayan mu, zamu ga bayan Korona.
Talla 2: Takunkumin fuska na asibiti yafi yadi da wasu ke amfani dashi—amma ko wana irin takunkumi yafi a ace an sa, da a fito ba takunkumin fuska.
Takunkumin fuska na daya daga cikin hanyoyin kariya daka yaduwar Korona. Takunkumin fuska na asibiti mai kyau da ake yarwa bayan amfani da yafi inganci wurin kariya da kuma hana yaduwar Korona akan yadi da ake sake amfani dashi.
Amma ka tuna: Takunkumin fuska dole ka sakata dai-dai domin ta baka kariya daga kamuwa cutar da kuma yadawa wasu.
Idan baka samu irin wace ake amfani da ita a asibiti ba, to ka cigaba da sa yadi da ake maimai tawa dan ya rufe ma hanci da baki. Sanya yadi a matsayin takunkumin fuska yafi DAYAWA da ace baka sa komai ba.
Ka kare mutanen da kake kauna. Sanya takunkumin fuska.
Talla 3: Dole ne mu dau matakan kariya akan Korona.
MAI-LABARI:
Wato Annobar Korona ta dade ta na wahalar da mutane. Abun takaici kuma, har yanzu bata tafi gaba daya ba.
Ya zama dole mu cigaba da daukan matakan kare kai.
Mu cigaba da sa takunkumin fuska da zata rufe mana hanci, DA baki. Ka na barin tazara tskanin ka da mutane. Wanke hanu akai-akai. Kana tabatarwa akwai isha shiyar iska a inda kake ta hanyar bude taguna. Kayi tari da atishawa a cikin gwiwar hanun ka.
Sanan abu mafi muhimanci, kaje ayi maka rigakafi!
Mu cigaba da karfafawa junanmu gwiwa mu kare al’ummar mu.
Talla 4: Korona na iya yin dogon tasiri akan lafiyar mutum ta dindindin.
SFX:
SAUTIN DAGA ABU MAI NAUYI. SAI KA SA TARI.
UWARGIDA:
Kofi, lafiyar ka kalau? Me ke faruwa?
MAIGIDA:
(NUNFASHI DA KARFI) Eh, lafiya ta kalua, nagode masoyiya. Har yanzu ban dawo daidai ba tunda na warke daka cutar Korona … har yanzu ina jin nunfashi na dauke min, sanan irin ayyukan karfin da nakeyi da yanzu wahala suke mun.
UWARGIDA:
Amma ya haka ya faru? Gwajin da akai ma satin da ya wuce, ya nuna baka dauke da Korona, ga ka dan saurayi mai lafiya!
MAIGIDA:
Hakane, amma likita na ya fada mun Korona na iya hadasa illa akan huhu na, hanta da koda—da kuma rashin jin kamshi ko wari da dandano. Kin san har yanzu ban dandana girkin ki ba sati da yawa da suka wuce. Kuma kullum ji nake na gaji …
UWARGIDA:
Allah sarki miji na, Sanu … Allah ya baka lafiya. Mungode Allah yanzu an mana rigakafi.
MAI-LABARI:
Korona bata nuna banbanci. Hadari ce ga KOWA sanan ta na da doguwar illa akan lafiyar mutum. Yin rigakafi shine hanya mafi sauki da inganci wurin samun kariya daka tsananin rashin lafiya, kwanciyar asibiti da kuma mutuwa ta dalilin Korona.
Saboda haka kar kayi jinkiri, kaje kayi rigakafi.
Talla 5: Kana kokonton rigakafin Korona? Kaje ka samu bayanin da kake nema
MUTUM 1:
Na kasa gane dalilin da zai sa ace muje muyi rigakafin Korona. Wanan ya keta haki da yanci na!
MUTUM 2:
Dan’uwana, na san yadda kake ji. Nima nayi kokonton rigakafin Korona da. Da nake so in samu karin bayani akan yadda yake aiki, sai na saurari gidan Rediyon XXX sanan nayi musu dukkan tambayoyi na. Tun daka nan, na cenja ra’ayi na. Yanzu ina gani dole muje ayi mana rigakafi domin kare sauran mutane da alummar mu, tare da kare kawunan mu.
MUTUM 1:
Hmmm … Idan har kayi duka wadanan bincike, ina ganin kana da gaskia … Zanje inyi nazari akai …
MUTUM 2:
Yauwa! Yanzu ya batun wasan kwalon namu! (MURYAR TA TAFI KASA-KASA)
MAI-LABARI:
Mutane da yawa suna kokonto, ko jin haushi, ko tsoro akan rigakafin Korona.
Ka zama gwarzon rigakafi ta hanyar samun lokaci ka karanta bayanai akan rigakafin dan tattaunawa da iyalan ka da abokan ka akai.
Ka san gaskiyar lamarin. Kaje kayi rigakafi.
Talla 6: Kamuwa da cutar bayan rigakafi
MACE:
Hello, ka kira gidan Rediyon XXX. Muna sauraranka!
NAMIJI:
Hello! Ina da tambaya akan rigakafin Korona. Me yasa zanje ayi mun allurar rigakafi? Tunda naji ance har wadan da aka yiwa rigakafin ma suna kamuwa da cutar Korona.
MACE:
Eh, zai iya faruwa ayi rashin lafiya sakamakon kamuwa da Korona har ma a yada ta bayan rigakafi. Amma yin rigakafi, yana rage hadarin faruwar haka sosai.
Rigakafi na bada kariya akan rashin lafiya mai zafi, kwanciyar asibiti, har ma mutuwa. Dan haka ne yake da muhimanci kayi rigakafi—domin lafiyarka.
NAMIJI:
Kina nufin idan na kamu da Korona bayan anyi mun rigakafi, zanfi samun sauki akan in ba’a yi mun ba?
MAI-LABARI:
Ita nau’in omicron tana da da saurin yaduwa da kamuwa. Shi yasa mutane da yawa ke kamuwa da Korona bayan anyi musu rigakafi. Amma rigakafi na da inganci wurin kariya daka tsananin rashin lafiya, kwanciyar asibiti da kuma mutuwa.
Don haka kada ka jira. Kaje kayi rigakafi.
Talla 7: Kaje kayi rigakafi dan kariya ga masu babban hadarin kamuwa da ita.
BINTOU:
Fatou! Me yasa bana ganin ki a kasuwa kwana biyu?
FATOU:
Hallo, Bintou. Ai bana fita sosai yanzu. Bazan iya yin rigakafin Korona ba, saboda haka nake daukan matakai sosai don in cigaba da zama cikin koshin lafiya.
BINTOU:
Toh! Me yasa baza ki iya yin rigakafi ba?
FATOU:
Ina so inyi kawata. Amma da yake ina yin maganin cutar kansa, bazan iya ba. Rigakafin na da kyau da inganci na sani, amma kariya da ke garkuwar jiki na yayi rauni bazai iya daukan rigakafin ba saboda maganin da nake sha.
BINTOU:
Wanan labari ba dadin ji, Fatou, Sanu kinji. Ki fada mun, ko akwai abun da kike so nayi miki?
:
Eh—ina bukatar ku na karfafawa yan uwa da abokan arziki gwiwa suje su karbi rigakafi. Ko ni bazan iya karba ba, zai taimaka sosai in duk wanda suke
kusa dani sunyi. Idan kowa yayi rigakafi, to zanfi samun nutsuwa in koma zuwa kasuwa.
MAI-LABARI:
Mutanen da suke da raunin garkuwa jiki, sun fi shiga hadarin kamuwa da rashin lafiya ko kuma mutuwa saboda cutar Korona. Kuma saboda baza su iya karbar rigakafi ba, sunfi shiga hadari.
Ba da kariya ga alummar ka, wanda ya hada da masu babban hadarin kamuwa da ita. Jai ka kayi rigakafi.
Talla 8:Eh, mata masu juna biyu zasu iya karbar rigakafin Korona ba tare da matsala ba.
MACE 1:
Ina maki fatan alheri da daukan juna biyu, yar uwata! Nasan kina ta murna za’a samu karuwa a gidanku.
MACE 2:
Muna ta murna sosai. Kuma ina jin dadi yanzu da akai mun rigakafi Korona!
MACE 1:
(MAMAKI YA KAMA TA) Rigakafi?? Amma ya akai kikai rigakafin Korona bacin kina da juna biyu?
MACE 2:
Au baki ji ba? Masana kimiya sun tabatar cewa rigakafin bashi da wata matsala ga masu juna biyu da jariran da suke dauke dasu. Amma kamuwa da Korona ba karamin hadari bane gare ni da jariri na. Rigakafi zai taimake mu sosai!
MACE 1:
Wanan labari ne mai dadin ji … ya kina ganin jaririn zai yi kama da ke ko kuma maigida? (DARIYA KASA-KASA)
MAI-LABARI:
Mata, zaku iya yin rigakafin Korona ba matsala ko kuna da juna biyu. Masana kimiya da suka cigaba da bincike akan Korona sun tabatar mata masu juna biyu zasu iya karbar rigakafi.
Don haka kar ki jira! Kare kanki da jaririn ki. Kije kiyi rigakafi.
Talla 9: Rigakafin Korona baya kawo rashin haihuwa ko rashin karfin gaba.
MAI-LABARI:
Zai iya yi yuwa kunji jita-jitai cewa rigakafin Korona na sa rashin haihuwa ko rashin karfin gaba! Wanan ba gaskiya bane. Ba wata shaida da take nuna cewa rigakafin Korona na sa rashin haihuwa ko rashin karfin gaba.
Kar ka yadda da jita-jita. Kaje kayi rigakafi.
Talla 10: Rigakafin Korona baya kawo rashin karfin gaba.
Namiji 1:
Aboki na, naji ance baka yi rigakafin Korona ba. Ko me yasa?
NAMIJI 2:
Bazan iya yin rigakafi ba—har yanzu ina so in sake haihuwa!
NAMIJI 1:
Ah wanan jita-jita ce ta banza. Kuma ba gaskia bace. Rigakafin Korona baya hana haihuwa! Rigakafin na da kyau kuma yana da inganci. Zai kare ka daka kamuwa da rashin lafiya, kwanciyar asibiti ko kuma mutuwa daka cutar Korona.
NAMIJI 2:
Haka dai kace. Amma ta ya zaka tabatar?
NAMIJI 1:
Ina sauraran gidan Rediyon XXX. Sun tattauna da maaikatan lafiya na jama’a, likitoci, da kuma mutanen da aka yiwa rigakafi. Dukan su sun fadi abu daya. Rigakafin Korona baya sa mata ko maza rashin haihuwa.
Don haka, dan Allah kaje kayi rigakafi. Zai taimakawa rayuwar ka da mutanen unguwanin ku.
NAMIJI 2:
(DOGON TUNANI) Lallai … Akwai kanshin gaskiya ace duka mutanen sun fadi abu daya. Kuma dai na aminta da gidan Rediyo XXX … Amma duk da haka ina da wasu yan tambayoyi. Zan kira gidan rediyon yau da dadare.
MAI-LABARI:
Rigakafin Korona ba ya sa rashin haihuwa.
Kar ka yadda da jita-jitan karya. Kaje kayi rigakafi.
Talla 11: Rigakafin Korona ba yasa mata rashin haihuwa.
SFX:
KARA KASUWA. SAI YAYI KASA-KASA.
NAMIJI 1:
Ahmed, Naji ance matarka ta karbi rigakafin Korona. Me yasa akai mata? Na dauka kana san kara haihuwa.
NAMIJI 2:
Eh, Abdoul, anyi mata rigakafi kuma naji dadi sosai. Rigakafin Korona ba zai sa ta zama bata haihuwa ba. Zai bata kariya daka rashin lafiya mai tsanani da kuma mutuwa.
NAMIJI 2:
Saboda, mutane biliyoyi anyi musu rigakafin Korona kuma lafiya lau suke, dan haka ina da yakinin cewa babu wani matsala.
MAI-LABARI:
Rigakafin Korona ba ya sa maza ko mata rashin haihuwa.
Kar ka yadda da jita-jitan karya. Kaje kayi rigakafi.
Talla 12: Mata masu shayarwa zasu iya karbar rigakafin Korona.
SFX:
Yaro na kuka a baya-bayA.
ASSATA:
Toh, Mariama, masha Allah kyakyawan yarinya haka! Ina miki san barka.
MARIAMA:
Nagode, Assata, Allah ya albarkace mu sosai. Kuma wancen satin da ya wuce, akai mun rigakafin Korona saboda in zama cikin koshin lafiya a yayin da jaririya ta take girma.
ASSATA:
(MAMAKI) Rigakafi?? Ta yaya akai haka? Kin tabbata kina shayar da yarinyar kuwa?? Ba za kiso ki bata rigakafin nan ta hanyar shayarwa ba!!
MARIAMA:
Kawata, ina shayar da kyakyawar ya ta mana. Rigakafin Korona basu da matsala ko kadan ga mata masu shayarwa da jariran su, kuma rigakafin zai iya bawa jaririn kariya shi kansa daga Korona.
ASSATA:
Toh, na samu kwanciyar hankali! Nayi murna kina kula da kanki da kuma jaririyar ki.
MARIAMA:
Ni uwa ce yanzu—bazan yi ganganci da rayuwa ta ba.
MAI-LABARI:
Mata, zaku iya karbar rigakfin Korona ko kuna shayarwa. Masana kimiyya da sukai nazirin rigakafin Korona sun tabbatar da mata masu shayarwa zasu iya kuma ya dace suje suyi rigakafi.
Don haka kar ku jira. Kuje ku kare kanku DA na Jaririn ku. Aje ayi rigakafi.
Talla 13: Maza! Ana tallafawa mata a lokacin annobar Korona dinan.
Maza! Lokacin anobar Korona, mata da yawa sun sha wahala suna aiki tukuru kamar ba gobe. Yara suna zaune a gida ba makaranta, yan’uwa na kwance ba lafiya, an karawa mata nauyi da yawa akan lokacin su—duk akan sauran ayukan su na gona, wurin aiki, da aikin gida!
Kar ka bari matan da suke cikin rayuwar ka su sha wahala.
Maza ku tallafawa kanen ku mata, yayan ku mata, matayen ku, da iyayenku mata a lokacin da suke bukata ta hanyar kula da yara ko kuma taimako a wurin wasu ayukan gida.
Akwai wata hanya mai muhimanci da zaka iya tallafawa mata, sanan ka kare lafiyarsu. Kaje kayi rigakafin Korona.
Talla 14: Akwai bukatar taimako ga matan da ke fuskantar kalubale da kuma ake cin zarafin su a dalilin jinsin su a lokacin anobar Korona.
MAI-LABARI:
Korona ta wahalar da kowa—musaman ma mata.
A lokacin barkewar Korona, mata da yawa basa iya barin gida, kuma mazajen su suna cin zarafin su. Idan ke ko wata da kika sani na fama da kunci, ko rashin lafiya, ko neman shawara lauya, ko kuma taimakon damuwar kwakwalwa ka ku kira [SAI KUSA LAMBAR WAYA KO KUMA LAMBAR GAGAWA TA TAIMAKON CIN ZARAFIN CIKIN GIDA A UNGUWA KU].
Ki tuna: ba ke kadai bace kike fama da irin wanan.
Talla 15: Hanawa da kuma kai karar cin zarafi mutum saboda jinsin sa a lokacin anobar Korona.
MAI-LABARI:
Iyaye maza, yanuwa maza, yanuwa mata, da iyaye mata—dukan mu muna da muhimiyar rawa da za mu taka dan bada kariya da kai karar in munga ana cin zarafin mata. Har a lokacin barkewar Korona.
Idan ke ko wata da kika sani na fama da kunci, ko rashin lafiyar, ko neman shawara lauya, ko kuma taimakon damuwar kwakwal wa ka kira [SAI KUSA LAMBAR WAYA KO KUMA LAMBAR GAGAWA TA TAIMAKON CIN ZARAFIN CIKIN GIDA A UNGUWA KU].
Ka ce a’a da cin zarafin mata.
Talla 16: Iyaye! Kuyi magana da yaran ku akan rigakafin Korona.
MAIGIDA:
Masoyi yata, ya kamata mu tatauna akan rigakafin Korona. Yaran mu manya sun isa ayi musu rigakafi, ya kamata mu san me za muyi.
UWARGIDA:
Eh, haka ne gaskia … Ina jin kai na garau bayan anyi mun rigakafi. Kuma likitan ya gaya mana rigakafi na bada kariya sosai akan rashin lafiya, kwanciyar asibiti da kuma mutuwa.
MAIGIDA:
Haka ne … Mu zauna da yaran yau da dadare muyi magana a matsayin iyali daya. Ina ganin lokaci yayi da zamuyi wa yaran mu rigakafi.
MAI-LABARI:
Iyaye! Ku hada kai domin yanke hukunci akan lafiyar iyalanku. Kuyi magana da yaranku akan rigakafin Korona, dan daukar shawara da ta dace don kariya ga iyali da alumma.
Kar ka jira. Lokaci yayi kaje kayi rigakafi.
Talla 17: Rigakafi bata tsofafi bace kawai!
MACE 1:
Ina yiwa kowa da kowa barka dazuwa taron mu na hadin gwiwa a daren yau. Nayi farin cikin haduwa da ku a zahiri, ina kuma jin kai na garau bayan da na karbi dukan adadin allurar rigakafi Korona.
MACE 2:
Amma me yasa kikayi rigakafi, malama? Wadanan rigakfin Korona na tsofafi ne kawai, ke kuma gaki yarinya mai jinni a jika da koshin lafiya.
MACE 1:
Eh hakane, nagode, amma … Rigakafi ta kowa ce—tsofafi DA yara! Har mata masu juna biyu su ma.
MACE 1:
Eh, ba matsala idan mace mai juna biyu tayi rigakafin Korona. Maaikatan lafiya sun fada cewa rigakafi ita ce hanya mafi kyau ta kare kai, iyali da kuma alumma.
Yauwa yanzu sai mu cigaba da taron mu … (A CIGABA DA HIRA A BAYA)
MAI-LABARI:
Korona bata san banbanci ba. Zata iya kama kowa ba ruwan ta da shekaru.
Rigakafin Korona hanya mai kyau ce da inganci wurin bada kariya ga cutar ko me ne ne shekarun ka.
Lokaci yayi da zaka je kayi rigakafi.
Talla 18: Kar ka bari Korona ta raba ka da abokai, yanuwa da aikin ka.
MAI-LABARI:
Mutane da suka kamu da Korona mai tsanani zasu iya daukan sati shida ko fiye da haka, kafin su warke, haka kuma Korona tana illa sosai ga lafiyar mutum. Wanan yana nufin dauke maka lokacin da ya kamta ka yi da abokai, yanuwa, da wurin aikin ka.
Amma mutanen da sukayi rigakafin Korona, hadarin kamuwa da rashin lafiya, ko kwanciyar asibiti ko mutuwa kadan ne. Suna zama cikin koshin lafiya su cigaba da kula da kuma jin dadin iyalin su.
Don haka kar ka jira. Kaje kayi rigakafi.
Talla 19: Kar ka rasa rayuwarka ta dalilin Korona.
MAI-LABARI:
Kusan kimanin mutane miliyan shida ne suka rasa rayukansu a duk duniya ta dalilin Korona. Wanan ba karamin tashin hankali bane.
Amma akwai hanya mafi sauki domin kare kai. Rigakain Korona basu da matsala suna kuma da inganci. Yin rigakafi na bada kariya sosai daga rashin lafiya, kwanciyar asibiti, ko kuma mutuwa ta dalilin Korona.
Kada ka yarda ka rasa ran ka. Kaje kayi rigakafi.
Talla 20: >Kana kokonton rigakafin Korona? Kasan gaskiyar lamarin
AMMA:
Ina kwana, Sita! Nayi murnan ganinki a shagona. Gashi sai kyali kikeyi shar abun ki!
sita:
Nagode, Amma. Ina jin dadin jiki na! Na gama rigakafi na gaba daya. Har naji kamar an sauke mun nauyi a kai!
AMMA:
Toh, Sita … bana jin na amince da wadanan rigakafin.
SITA:
Na fahimci damuwarki. Amma, zaki iya neman karin ilimin abun sosai. Duka iyali na da abokai na kusa sunyi rigakafi, kuma suna cikin koshin lafiya, kamar ni.
SITA:
Eh. Mutane sama da biliyoyi sun karbi rigakafin Korona ba wata matsala. Suna da inganci wurin kariya daka rashin lafiya mai tsanani, kwanciyar asibiti da kuma mutuwa.
:
Toh, nagode sosai da kika fada mun. Amma ina da tambayoyi. Ko zaki kara mun haske akan … (YA KOMA BAYA)
MAI-LABARI:
Tattaunawa da abokai da yan uwa akan damuwar su na taimakawa wurin jadada musu ingancin rigakafin Korona.
Ka san gaskia. Kaje kayi rigakafi, ka zama gwarzon rigakafi ta hanyar tattauna wa da yan’uwa da abokan arziki akan rigakafin Korona.
Talla 21: Goyon bayan rigakafin
MAI-LABARI:
Rayuwa ni’imace daka Allah. Dukan nin mu muna da nauyin kare yan’uwan mu da alummar mu daga Korona.
Wanan (suna, take) nazo dan na fada muku rigakafin Korona bashi da matsala kuma yana da inganci. Ina baku shawara kuje kuyi rigakafi da zarar kun samu dama—saboda ku cigaba da jin dadin albarkacin rayuwa.
Talla 22: Rahsin lafiya da aka saba, da dan illar rigakafin Korona
UBA:
Lafiya lau, amma naji ance kayi rigakafin Korona. Ba ka san wadanan abubuwan zasu sa maka rashin lafiya ba?
DA:
Aw, ai wanan jita-jita ce ta karya, Baba. Na samu dan rashin lafiya da aka saba, da dan illar rigakafin kadan bayan anyi mun rigakafin. Hanuna yayi dan ciwo, sanan nanji gajiya, amma ya wuce bayan kwana daya ko biyu. Kamar ko wata irin rigakafi.
Yanzu ina ji na lafiya kalau. Rigakafin ba ya sa wa mutum rashin lafiya—yana bawa mutum lafiya. Ina fata kai da Mama zaku je ku karbi rigakafi kwanan nan.
UBA:
Naji dadi kana nan lafiya. Sanan nayi maka alkawari, ni da maman ka zamu yi nazari akan karbar rigakafi. Sai anjima da na, zan kira ka anjima … (HIRAR TA TAFI)
MAI-LABARI:
Dan karamin illar allurar kamar ciwo, gajiya, ciwo, ciwon kai, da dan karamin zazabi abu ne da ake na kwana daya ko biyu bayan rigakafin Korona. Wanan shi yake nunawa rigakafin na aiki.
Rigakafin Korona bashi da matsala yana kuma da inganci.
Ka nemi gaskia. Kaje kayi rigakafi.
Talla 23: Ka taimakawa yaran ka suje suyi rigakafi.
SFX:
KWANKWASA KOFA. BUDEWAR KOFA.
UWARGIDA:
Ya naga damuwa a fuskar ka, ya masoyi?
MAIGIDA:
Yanzu naji daka Aziz … Yace yaje yin rigakafin Korona. Nasan mutane na cewa basu da matsala, amma ni ina da shaku akai …
UWARGIDA:
Ba laifi in ka nuna damuwa akan dan ka, masoyi. Amma nasan mutane da yawa sukayi rigakafi, kuma suna nan cikin lafiya kalau. Likita ne ya fada mun zai bani kariya daka Korona. Ina ganin mu nemi karin ilimin abun ko?
MAIGIDA:
Eh toh, kema kin fadi gaskia … Kuma dai dan mu ne. Mun raine shi da kyau, kuma na yadda dashi.
MAI-LABARI:
Rigakafin Korona bashi da matsala kuma yana da inganci. Ka taimaki ya’yan ka ta hanyar tattaunawa dasu game da rigakafi.
Lokaci yayi da zakaje kayi rigakafi.
Talla 24: Rigakafin baya da matsala kuma ya na da inganci.
MAI-LABARI:
Wasu mutane suna ta damuwa wai rigakafin Korona an samar dasu da wuri sosai dan haka suna da matsala. Amma rigakafin Korona basu da matsala kuma suna da inganci.
Ga dalilai guda uku da yasa sukai saurin samuwa:
Na farko dai, masu bincike sunyi shekaru da yawa suna naziri akan cututukan korona. Korona iri daya ce da sauran kwayoyin cutan corona, dan haka masana kimiya sukai saurin gano wana irin rigakafi ne zaiyi aiki akan Korona.
Na biyu, saboda Korona ta shafi duk duniya, kungiyoyi, da gwamnotoci da yawa sun bada kudi sosai dan samar da rigakafi dan ceton rayukan mutane. Wadanan kudade sun taimakawa masu kir-kiro rigakafin suyi aikin su da wuri akan sauran rigakafi.
Na uku, rigakafin Korona an yi gwajin su sosai dan aminci, kuma har yanzu ana cigaba da gwaje-gwaje, ko yanzun nan ma ana yi. Domin, tasirin Korona na da tsanani, masana kimiya suna yin nazarin sakamakon gwajin da zara ya fito. Wanan ya taimaka wa kamfanoni su buga rigakafin da sauri.
Rigakafin Korona bashi da matsala yana kuma da inganci.
Kar ka jira. Kaje kayi rigakafi.
Acknowledgements
Contributed by: Vijay Cuddeford, Managing Editor, Farm Radio International and Hannah Tellier, Resources Coordinator, Farm Radio International
This resource is funded by the Government of Canada through Global Affairs Canada as part of the Life -saving Public Health and Vaccine Communication at Scale in sub-Saharan Africa (or VACS) project.