Yi kira ga nemar daidaicin jinsi da saka iko a hannun mata

Lura ga mai watasa shiri

Rashin samu daidaicin  jinsi na kara matsalar gaske ga Africa da wasu nahiyoyin.Idan mata suka rashi malakar albarkatu kamar kasa,baza su iya daukar shawarar da zai habaka arzikin iyalinsu ba, Idan ba iko akan arzikin iyali. Misali na shuka kayan gona ba, zaka samu mata na bayar da gudunmuwar karfi da lokacin su don rikon  rayuwa ne kawai, kuma suna fuskanta tsananin talauci fiya da maza.Kuma al’adun gargajiya, dake iya haramta wa mata harakoki irin su shuka bishiya ,na rage hazakar su na kiyayewa da kuma cira darajar kare mahali.

Hakin kasa da kadarori, musamman, a sannu na zamowa ainihin zance dake tsakiyar duk wani taron da jami’an gwamnati ko na kunmgiyan jama’a ke shiryawa kuma mata ke kan gaba a cikin yaki da nuna banbanci ko wariya.Daidaicin jinsi haki ne ga dan adamu kuma shine cibiyar cimma cigaban manufofin miladiya.Tilar ne kamin a shafe nyunwa , talauci da cuttutuka.Daidaicin  jinsi na nufi a samu  daidaicin  a duk matsayin ilimi da duk bangarorin ayukan yi, daidaicin iko akan albarkatu, da daidaicin wakilta a sha’anin jama’a da ta siyasa.

Wannan rubutun na dubar fidda wariyan jinsi a cikin duk bangaren rayuwa , sabili da ba zamu ji dadin cigaba ba idan ba tsaro,ba zamu ji dadin tsaro ba idan ba cigaba, haka kuma ba zamu ji dadin ba idan ba’a daraja hakin dan adamu.Hannya daya da zaka rungumi wannan rubutu domin masu saularenka na gida shine kayi fira da wani acikin unguwar ko jihar ka wanda ke kira game da sha’ani samun daidaicin jinsi.

Wanan rubutun ta dogara ne akan ainihin wata fira. Zaka iya amfani da ita wurin gudanar da bincike da rubuta wata irin zance acikin unguwar ka.Ko kana da zabi kayi amfani da ita a tashar ka, kana mai amfani da muryoyin ‘yan wasan kwaikwayo su wakilci masu Magana.Idan haka ne, ka tabattar ka sanar da masu saularen ka tun da farko shirin cewa, muryoyin na ‘yan wasan kwaikwayo ne ba ainihin mutanen da akayi fira dasu ba

Rubutunsa

Bari sautin taken ta shude dakiki 10 sai ka soma shiri

Mai watsa shiri:
Barka da saduwa da ku, masu saulare, shirin yau ta kumshi sha’anin mata da hakin malakar kadarori.Wanan ba kasa kadai ta shafi ba, ta hade duniya bakiya ne.A nan kuna tare da mai watsa shirin Rachael Adipo, ke kawo muku shirin daga nan Ugunja FM, Miss Jessica Odima, na tare da ni nan ,wata mai kira ne ga kare hakin mata a can kasar Kenya.Ku cigaba da saulare.

Shude satin taken dakiki 2 sai ka soma

Mai watsa shiri:
Barka da sake saduwa da ku,.Yau zamu dora hankali ne akan sha’anin mata da malakar kadorori ta zamo wata hannyar cimma manufofin miladiya na kira da nemar daidaicin jinsi da saka iko a hannua mata. Samma ma a gundumar Siaya, Barka da zuwa,. Miss Jessica. Ko zaki bamu wani haske game da hakokin mata?

Jessica Odima:
Na gode, Zan soma da cewa, mata na da hakin samun filaye, samun tsaro da kuma hakin malakar kadarori.Mata da maza gaba dayan su sun fahimci wanann zance,a anihin zancen dake bukatan muhauwara akai.Ko da yake dokar kasar Kenya baya nuna wariya ga mata wurin gadon kadorori, al’adun gargajiya mutane ke cigaba da hana musu malakar kadarori.

Mai watsa shiri:
Ta yaya ke da ‘yan uwayen ki masu kira da kare hakin mata a can yankin Siaya ke kokarin taimaka wa mata wurin sake dokokin dake nuna wariya da ta’adodin da suka shafi gado,kai tsaye mace ta malaki kuma tayi haraka da fili, da kuma samun ta a cikin malakar filin dangi?

Jessica Odima:
A matsayi na na mai kare hakin mata a gundumar Siaya,mun taimaka wa mata suka fahimci hakin su, ta hannyar ilamantarwa, da fadakar dasu game da sha’anin doka ta shirya taruka, ta kafofin watsa labarai akan samun fili da kadarori,da gudanar da bikin ranar mata ta duniya, takwas ga watan Marisin kowace shekara,.

Mai watsa shiri:
Naji cewa,a gundumar Siaya, duk wani taron jama’a ba zata yi armashi ba ba tare da masu kare hakin mata sun halarta ko sarkin yayi bayani bukatan samun mata harma da yara a cikin sha’anin kadorori ba.

Jessica Odima:
Haka ne, duka waddan nan sun cira himar mata na yakin nemar hakin su da kuma karawa da hadamarmun dangi masu saka mata acikin wahala na kore su daga gidajen auren su, su kwace musu kadarori.

Shude wakan taken dakiki 2 sai ka soma

Mai watsa shiri:
A yanzu, Miss Jessica,ko zaki ba masu saulare wasu labaran mata da kika ji a unguwar ku?

Jessica Odima:
I, kwarai Ko. Sai muji labarin Agnes Apiyo daga gundumar Siaya.

Agnes Apiyo:
Gaba daya da kamala ta’adar Luo,wadda ke bukatar a fidda hakoran kasa shida, Wani makwabci, dake nemar matan da ta dace wa dan danuwar sa ya nufato ni. Ba da jimawa, na sadu da kyakkyawan mutu wanda ya zamo miji na kuma uban ‘ya’ya na biyar maza uku da mata biyu.. Nayi rayuwan jin dadi da miji na shekaru goma sha takwas sai da wa’adi ta kai. Miji na Daniel Omollo ya mutu daga cutar zazzabin sauro.Sai gaba daya dunyia ta marmashe, har da murna ta na ‘yar gabar goshin surukunnai na.Kowa na muzguna mini, Daga kanin miji na zuwa iyayen sa, kowa na bukatan rabon sa daga kadarorin.

Jessica Odima:
Ba Agnes kadai bace, A lokacin taron fadakarwa da wata kungiya mai zaman kanta ta gida da ake kira Ugunja Community Resource Centre tare da hadin kan wata kungiya ta kasa mai suna Kenya Land Alliance. An fadi labarai masu daure kai game da mata da mazan su suka mutu kuma aka tilasta musu barin gida bayan da mazab suka mutu..

Mai watsa shiri:
wato wannan taron fadakarwa ya bude wa mutane idanuwar su?

Jessica Odima:
I, a yanzu mata na bukatan su malaki rayuwar kansu.Yanzu, suna son su fada cawa, “Waddannan harakokin tamu ce kuma tsarin cigaban rayuwar mu nan gaba muna da su” Ba, “Waddannan harakokin tamu ce kuma cigaban rayuwar mu nan gaba an shirya mana.bane”

Mai watsa shiri:
Na gode, Miss Jessica.Yanzu mun gano cewa,,samun ababa daban daban tsakanin mata wata kafa ce na samun arziki, karfi .ilimi da kwarin gwiwa.

(Wakafi) mun koyi ababa da dama a yau: hakokin mata daban daban, yanda za’a shafe harakokin nuna wariya, da yanda masu kare hakin mata na gundamar Siaya ke fadakarwa.Munji cewa, waddan da ma aka nuna musu wariya zasu iya samun sakankancewa. (Wakafi) Mai saulare,wanna ya kawo mu karshen shirin mu na yau.A yau mu dora hankali ne akan mata da malakar kadarori a wata hanya cimma manufofin miladiya na daidaicin jinsi da saka iko a hannu mata.Da fatar kun koyi wani a bu. Sai mun sake saduwa, a huta lafiya.

sautin taken na dakiki 10 sai ka shude

Acknowledgements

Gudumuwa: Rachael Adipo, Ugunja Community Resource Centre, Kenya.

Nazari: Carole Houlihan, International Development Consultant, Canada.

Kofi Annan. Africa’s Green Revolution (A call to action).UN press release, July 6, 2004. http://www.un.org/News/Press/docs/2004/sgsm9405.doc.htm

UN Millennium Development Goals. United Nations Environment Program. United Nations Development Goals.

Phillip Onyango. Land and Property Rights. Ugunja Community Resource Centre, 2005.

Information sources

Ba wani shawara akan nau’i nau’i na samu malaka fili ko kadarori.Wasu lokutan yin rejistan kadarori yafi dace da wasu  kuma ta al’ada tafi ga wasu.Samar da tsaro mai inganci da daidaicin wurin samun fili da kadarori ga mata na bukatan a gudanar da harakoki ba gwamnati kadai ba, daga duk bangarorin al’uma, da suka hada da.masu zaman kansu, shugabanin unguwanin da na gida, da kuma kungiyoyi abokai da kungiyan kasa kasa. Mata na bukatan daidaicin murya a cikin daukar shawara da ta shafi rayuwar su daga tsakanin dangi har zuwa kokoluwan matsayin acikin gwamnati.Wannan muhimmi ne cikin saka iko a hannun mata..Lokaci da dama maza sun mamaye daukar shawara a kokoluwan matsayi.Matakan kiyayewa da gyara na yin zagon kasa ga hakin mata na malakar filaye da kadarori, sabili da tsarin yanzu, sai an shirya ka’idodin tatalin arziki.