Ba a yanka tselen mata kuma: Kyauyawa a Seganegal sun gudanar da bikin kare hakin mata na cikon shekaru 10

Lura ga mai watasa shiri

Lalata tselen mata ko FGC ya hada ne da aikaceceniya da dama na yanke gaba daya ko bangare ko kwaskwarimar wajen tselen mace ba tare da dalilan kiwo lafiya ba. Tsarin aikin zai iya kasancewa ana amfani da kayan aiki da ba a kashe dafin su ba, daga wata zuwa wata ko mara inganci.

Fasahar da ake amfani da ita acikin wannan aikin ta bi muhimman cigaba da dama. Da farko da aka soma sanin harakar wajen al’umar da suke gudanar da ta’adar, gaba daya ana kiran ta da “kaciyar mata” Wannan lakabin, babu shaka, ta kawo gigicewa tsakanin harakoki biyun nan dabam dabam na kiciyar mata da maza. Lamarin ‘yan mata da mannyan mata, FGC wata bayani ce ga rashin daidaicin jinsi da tayi kanta ta basu kasa-kasan matsayi cikin al’uma kuma nada illa a bayyananne ta jiki da ta zamantakewa.
.
Kusan karshen shekara ta 1970, zance “lalata tsellen mata” (FGM ) take ta cigaba da samun goyon baya.Kalmar”lalatawa” ba kawai tana banbanta tsakanin ta da kaciyar maza bane, haka kuma , sabili da mumunar alaka , bayanin tsananin harakar. Amfani da kalmar“ lalatawa” na kara karfi ga ra’ayin cewa wannan harakar wani take haki ne na ‘yan mata da mannyan mata. Hakan yana taimaka wa bayanar da kira ga kasa da kasa- kasa suyi watsi da ita.Tsakanin al’uma, babu shaka, kalmar zata iya zamowa matsala.Harsunan gida gaba daya na amfani da mafi saukin hukunci “Yanka” wurin bayanin harakar, iyaye a tasu fahimtar na kin shawarar cewa suna “lalata” ‘ya’yan su mata ne.A cikin wannan halin, cikin shekara ta 1999, Jami’in Majalisar Dinkin Duniya ta musammam game da harakokin gargajiya yayi kira da asa hankali da hakuri game da harakokin waddannan uguwannin kuma a jawo hankula akan hadarin “munana” wasu al’adu, adinai da al’uma.Sakamokon haka, Kalmar “yanka” ana yawaita amfani da ita domin hana ware unguwannin

Hukumar lafiya ta duniya ta kiyasata yawana ‘yan mata da mannyan mata a miliyan 100 waddan da suka fadawa wasu irin yankan tsalen su.Haka kuma aka kiyasta ‘yan mata miliyan biyu ake yanke wa tsale (FGC) a kowace shekara.Mafi yawancin su a Africa ko Asia.A mafi yawancin kasashen turai da Arewancin Amurka, FGC haramtaciya ce, ko da yake wasu lokutan ana sigaba da yi Africa da Unguwannin Asia

Wannan rubutun ya dogara ne kan ainihin fira, Zaka iya amfani da rubutun nan tamkar kwarin gwiwa ga bincike kuma ka rubuta wata da ta dace da unguwan ka ko kana da zabi kayi amfani da ita a tashar ka , kana mai amfanii da muyoyin ‘yan was an kwaikwayo su wakilci masu magana, Idan haka ne,ka tabbatar ka sanar tun da farkon shirin cewa,muryoyin na ‘yan wasan kwaikwayo ne, ba ainihin mutane da akayi fira da su ba.

Rubutunsa

Mai watsa shiri:
Ina kwana (Ina yini, barka da yamma) kuma barka da saduwa da ku akan shirin.A yau zamu yi fira da Maimuna Traoré da Marième Traoré.Mata biyun nan sun fito

Malicounda Bambara, na kasar Senegal ne,kuma suna cikin gungun matan da suka soma furucin cewa kyauyen su baza ta kara gudanar da harakar yanke tselen mata ba.Bikin cika shakaru 10 na wannan furucin Malicounda Bambara an gudanar ne a ranar 31 ga watan Juli,shekara 2007.

Malicounda Bambara wata kyauye ce dake unguwan Thiès a can yammancin Senegal.Mata talatin da biyar daga wannan kyauyen suka hadu suka shirya wannan furucin ranar 30 ga watan Juli,sheakara 1997.Hakan ta biyo bayan horo da suka samu daga wata kungiya da ake kira Tostan inda suka yanke shawaran daina take hakin yaran matan kuma suka bayanar.Horon sun hada ne da sanarwa game da hakin lafiyar ‘yan matan su,yarjejeniya akan hakin yaro,yarjjeiya akan kawad da dukannin muzguna wa mata, yarjejaniyar Africa akan jindadi yaro, sanarwa game da matsalolin da zasu iya tashi daga yanka tselen mata.(Dakata) Maimuna Traoré, , ko zaki yi bayanin kanki ki kuma fada mana a cikin kalamun ki abinda ya faru shekaru goma baya.cikin shekara ta 1997?

Maimuna Traoré:
Suna na Maimuna Traoré.ni ne mai kula da aikin din Community Management Committee kuma ina dauke da halakin matan Malicounda Bambara.Ba mun shirya wannan furucin bane muyi watsi da gargajiyar mu bane, face, mun shiga shirin ilimantarwan Tostan inda muka koyi ababa da dama game da matsalar yanke tseln mata.

A laokacin da matan Malicounda su kayi nufin watsi da wannan harakar, ina can kasar Mali,Dana dawo,Sai naji cewa matan sun halarci taron daukar horo akan hakin mutu da lafiya.Sun koyi matsalar da zata iya tasowa idan ana gudanar da yanke tselen mata ko kaciyar mata.Matan suka shirya wasan kwaikwayo akan zance domin su fadakar da al’uma.

Dana dawo matan, suka tambaye ne ra’ayi na game da lamarin.Na fada musu ina goyon bayan yunkurin su domin sune iyayen yau,kuma wannan lamarin ta shafi lafiyar‘ya’yan su.Don haka, idan suka yi shawara da mazajen su suyi watsi da wananan harakar sabili da matsalolin dake tare da yanke tselen mata, kawai namu ne mu goyi baya mu kuma daraja ra’ayin

Mai watsa shiri:
Ko an sha wahala wurin aiwatar da furucin nan?

Maimuna Traoré:
A matsayi na na mahalarciyar shirin ilimantarwan, mun yi zance da al’umar Malicounda Bambara gaba daya.Bayan muhauwara da musannyam, ra’ayin ayi wasti da harakar mun yi shine a hade.

Horon Tostan ya bamu damar sada tsakanin matsalolin da mata da ‘yan mata suka shiga na yanka tselen su da harakar yanka tselen mata.Shirin ta bamu dammar aiki a hade da famar sake ababa.

A lokaci da yanka tselen mata ke da amfani ga amincewar zamantakewa da aure. Don haka ra’ayin wasti da harakar mace daya baza ta iya yi ita kadai ba sabili da tsoron kiyaya daga alumar.Babu shaka , bayan furucin, mun fuskanci matsaloli domin wasu manema labarai da suka wasta labarin sun murgude ra’ayin mu.Sakamakon haka ,dukannin al’umar Bambara na adawa da mu.Yana da sauki a yanzu kayi zancen game da wasti da hakarakar FGC,amma an sha wahala kamin a kai ga hakan

Mai watsa shiri:
zaki iya bayani ko wani abu ya sake tare da rayuwar matan tun lokacin da aka daina aiwatar da FGC?

Maimuna Traoré:
Takamaimiyar sakiyar da muka samu itace an daina FGC na dindindin.Hujja game da nasarar furucin mu shine dubunnai al’uma sun karu da mu kuma mutane na da kwazon magana a fili game da harakar da a shekaru goma da suka wuce ta zamo haramtaciya.Daina FGC ya kawo karshen banbanci tsakanin al’umar mu. FGC wata bukata ce ga amincewar zamantakewa.Wata alama ce na zamowa. Bambara,anyi hakan har Bambara baya aure sai Bambara.A yau, muna iya ganin ainihin sakiyar zamantakewa.Yanzu muna ganin aurayya tsakanin Bambarawa da Sererewa da Walfawa a kyauyen mu.

Wasu sakiyan a unguwannin mu suna alaka da shigar mu shirin ilimantarwan Tostan.kamin shiga shirin nan.yana da wuya mata su shiga taron maza.Mata basa da alaki; zasu aiwatar da ra’ayin maza ne kawai,A yau, mata dake matukar jin kunnya na tsakiya da gabar al’uma.Nice mai kula da Malicounda Bambara Community Management Committee,mai mambobi 17, da maza a ciki.Shirin Totta din nan ya ba matan kwamitin dammar tabka muhauwara da maza akan daidan fage.

Mai watsa shiri:
Na gode, Mallama Maimuna.A yanzu zamu waiwayi. Marième Traoré Ko zaki iya bamu taki ganin game da daya-dayan tambayar?

Maimuna Traoré:
Furucin Malicounda Bambara na da girma kuma farko kenan a Senegal.Tun lokacin, matan mu a kowani lokaci ana nuni gare su da gwarzaye a cikin yunkurin daina FGC. Mun gano FGC a take hakin lafiya ne.Sabili da shirin Tostan, mun kuma zamo masu dogaro da kanmu.Misali, muhiman ababa kamar buga lambobin waya, da sai mun nemi taimakon wani.Haka kuma ga karatu da rubutu.

An samu wasu sakiya da dama a unmguwan mu.’Yan mata basa fadawa hadarin matsalar lafiya kamar zub da jini da yawa domin ba’a aikata FGC kuma.An samu sakiyar matsayin zamantakewa kuma . Ko da wasu na aikta FGC ma, suna hakan ne acikin sirri domin suna tsoron hukuncin al’uma.Kamar yanda Maimuna ta fada,rayuwar mu gaba daya ta sake.Mu a matsayin mu na mutane ya sake.An san mu a fadin Senegal da duniya bakin daya a farkon mata da suka yi tsayin daka wurin a daina FGC.

Mai watsa shiri:
Menene tunanan ki ga ainihin zance cewa unguwani 2300 sun karu da ku a ciikin wanan harakar daina aikata FGC a Senegal?

Maimuna Traoré:
Muna murna da buga kiriji da sanin wasu sun karu cikin mu. Wannan ze kara karfafa sadakar da kan mu na daina FGC da aikata wasu ta’adu masu hadari. Haka muke buga kirji da waddan da suka shiga gaban wannan babban takun daina FGC a Senegal da wasu kasashen Africa.

Mai watsa shiri:
Maimuna, yaya kike ji da unguwannin 2300 suka shigo cikin ku

Maimuna Traoré:
Wata kafa ce da muke alfahari da ita.Ina son in gayyaci sauran kungiyoyi da basu shiga cikin mu ba a Senegal dasu hada kai da mu cikin harakar daina FGC sabili da bazaka iya dora firasi akan lafiya ba, sammam ma lafiyar mata.Shiga shirin ilimantarwan Tostan , mun koyi ababa da dama game da lafiya da tsabta da hakin ilimi,hakin sanarwa, da hakin kariya daga duk wani fitina.Wannan ta bamu dammar yin adawa da kowani irin aikatau mai illa ga lafiya,samma maFGC da auren wuri.

Yau, mun waye kwarai da al’adun da gargajiyan mu .Mun kasance Bambara fiya da da! Shirin Totan ta bari muna sa hankali sosai akan ta’adun mu sabili da tana sake sada mu da al’adun kwarai mu yi wasti da masu illa.Gaskiya ne cewa mun sake. Muna da kulawa kwarai, mun yi tsayiin daka sosai , buga kirji,sani sosai da hadin kai kwarai.

Mai watsa shiri:
Ina son nayi godiya ga bakin mu biyun nan da suka yi fira dani yau(Dakata) Masu saulare, wannan ya kawo mu karshen shirin mu.Idan kana bukatan sanin ababa da dama game da kaciyar mata, ga wasu kungiyoyin gida dake aiki akan lamarin.(Mai watsa shiri kira sunayen da lambar saduwa da kungiyoyin gidan da ta kasa) Na sallame ku a yau.

Acknowledgements

Gudunmuwa: Issa Saka, Trainer/External Relations Officer, Tostan International.
Nazari : Neil Ford, Regional Chief, Programme Communication, UNICEF, Dakar, Sénégal.

Information sources

An rugume wannan rubutun ne daga firan Tostan tare da Maimuna Traoré da Marième Traoré (cikin Faransaci) da akayi ranar 16 Juli , 2007, yana kan layi a http://www.stopfgmc.org/client/sheet.aspx?root=171&sheet=2031&lang=en-US
Daina FGM/C dandalin gizo http://www.stopfgmc.org/ na dauke da labaran FGM/C da shirin daina shi, da suka hada da labaran kungiyoyi masu zaman kansu dake aiki akan lamrukan game da lalata tsellan mata / kaciyar mata a http://www.stopfgmc.org/client/final_category.aspx?root=134&lang=en-US
Game da sabbi labarai akan FGM/C , kuma dubi http://www.stopfgmc.org/client/category.aspx?root=157&lang=en-US
Kuma dubi: United Nations, undated. Women’s Rights. http://www.un.org/rights/dpi1772e.htm
UNICEF, 2005. Changing a Harmful Social Convention: Female Genital Mutilation/Cutting. http://www.unicef-irc.org/publications/pdf/fgm_eng.pdf (Kafar labari na cikin Lura ga mai watsa labara ).
Zaka iya saduwa da Tostan International a BP 29371, Dakar Yoff, Sénégal.Dandalin gizo: http://www.tostan.org