Manomar Niger na cin moriyan barin bishiyoyi su tsira akan filayen su

Lura ga mai watasa shiri

Save and edit this resource as a Word document.

A cikin shekara 1970 da 1980, an yi rubutu da dama akan rikicin makamashi a kasashe dake yanki sahel da kuma unguwannin busassu da tsakatsakiya. Akwai kamar babban rata tsakanin bukatun jama’a na makamashin-kusan duka a kebe itatuwa ke samarwa-da yawan itatuwa da kare domin biyan bukatun. A wannan lokaci Sahel ta fusakancin fari shekaru bisa shkaru.Filayen gonaki na mikewa gaba da gaba zuwa yanki mara amfani,da aka halaka. ciyayn su.

Kamar ciyayin dake kusa da biranen cikin Sahel zasu halaka gabadaya sabili da yanda bukatun jama’a na makamashin itatuwa ke yaduwa cikin hanzari.

Kwanannan, ana tunane ciyayi cikin Sahel na ragewa domin yawa-yawan amfani,.Amma kamar yanda wannan ke gudana a filin wasu bangarorin Sahel,akwai wurare da dama dake samun karin itatuwan ciyaye.Misali a Niger,karin itatuwan ciyayi na awukuwa ne a jihohin Tahoua, Maradi da Zinder.A Touha, harakokin dake shirya ayukan sa hanakali akan ceto da sake tsugunar da kasa kekasasshiya ke dasa bishiyoyi, kuma manoma sun soma kiyaye bishiyoyi da kare da suka sake tofowa da Ikon allah.

Masu kiwon dabbobi na kare ciyayi, kamar irin bishiyoyi, Acacia raddiana. A Maradi Kungiyoyi masu zaman kansu na tainmaka wa manoma su kare kuma misiltu bishiyoyi da kare da suka sake tofowa a cikin gonakin su.An soma wannan harakar ne tsakiyan shekara1980. Kwana-kwanannan, a jihar Maradi gundumar Aguié ta taimaka wa kafa kungiyoyin kyauye na kariya da misiltu da amfani da bishiyoiyin gonakinsu.A Zinder, an samu gagarumin misiltun manoma ta musamman game da sake tofowa daga Allah.

Wannan rubutun na tauna zance shirin Farmer Managed Natural Regeneration wato shirin manoma na misilta sake tofowar bishiyoyi. (FMNR atakaice) Ana nufi da FMNR wata aiki da ta kumshi kariya da misilta sake tsirowar bishiyoyi da kare a filaye.Shirin FMNR nada amfani ga manoma yana dawo musu da itatuwan ciyayi.Manoma a kullun na tuanen dawowa da bishiyoyi da kare tare da darajar tattalin arziki.

Yana mamaki ka gano cewa ba’a dora hankali sosai akan manomi-misilta da kiyaye bishiyoyi da suka sake tofowa da ikon Allah Kadan acikin masu yanke shawara na gida da kasa-kasa suka san da shi, kuma zance sa kadan ake bugawa a mujallu.Amma nazari daya kawai yace FMNR tayi tasirin gaske akan fillayen noma miliyan 5 a Niger.Idan wannan daidai ne, ta kadaita a Sahel watakila ma a Nihiyar Africa gaba daya

Wannan rubutun ta dogara ne akan ainihin fira.Zaka iya amfani da ita ta zamo kwarin gwiwa ga bincike da rubuta wata zance makamancin ta a unguwan ka.Ko zaka iya amfani da ita a tashar ka, kana mai amfani da muryan ‘yan wasa su wakilci masu magana. Idan haka ne, don Allah kayi kokari ka fada wa masu saularen ka tun da farkon shirin cewa muryoyin na ‘yan wasa ne,, ba ainihin mutanen da akayi fira da su ba.

Rubutunsa

Mai watsa labarai:
Barka da saduwa da ku, masu saularen mu. A yau zamu tauna zance wani aikin gona da ake kira manomi misilta sake tofowar bishiyoyi ko FMNR, da manoma da dama ke yi a kudancin Niger. A cikin harakar FGMNR,manoma na kare kuma suna aikin misilta sake tsirowan wasu nau’in bishiyoyi a cikin filayen su.Wannan na dawowa da ciyayi a busasun wurare kuma yana habaka albarkaun gona kudin manomi.irin da suke karewa kusan kullu masu daraja ne ga tatalin arziki – a wani kalamun kuma,waddan da ke ‘ya’ya ko ake iya amfani dasu asa wuta ko ga wasu ayuka masu amfani.Ana kiran wannan aiki da FMNR a banbatta tsakanin shuka bishiya da misilta bishIyin da sukE tsaye da iko Allah.Waannan shirin na zance ne game da dalilai da yasa manomar jihar Maradin kudancin Niger suka soma kare tofowar bishiyoyi da kare da ikn Allah akan filayen su.Kuma yana zance yanda suke misilta waddannan bishiyoyin da karen,da tasirin FMNR akan rayuwar su na yau da kullun.

FMNR a cikin jihar Maradin kudancin Niger ya soma da aikin wata kungiya mai zaman kanta da ke gudanar da aikin da ake kira a turance Serving-In-Mission ko SIM acikin shekara ta 1980 ta Maradi Development Project.Game da hakan, Wani aiki da IFAD ta dau nauyi a cikin gundumar Aguié sun dukkufa akan FMNR. A cikin 1999, kashi 88 bisa dari na nazarin da akayi akan ayukan kyauye da kyauyukan da aikin bai kai gare na aikata FMNR akalla acikin filayen su.Sakamakon ne kusan ana samun Karin bishiyoyi miliyan daya da kashi daya bisa hudu a unuguwannin aikin a kowace shekara.

Na yi fira da Mr. Ali Micko, wanda ke cikin aikin a gundumar Aguié na jihjar Maradi

Barka, Mr. Micko suna na Lawali Mamane Nassourou daga kungiya mai zaman kanta Le Micro Vert. Firan mu a yau zai dogara ne akan FMNR. Ko zaka soma da bayanin kanka?

Ali:
Suna na Ali Micko, ni manomi kuma shugaban gungun ‘yan kyauye a Dan Saga.

Mai watsa labarai:
Yaushe kuka soma gano sake tofowar ciyayi akan filayen ku?

Ali:
Ciyayin sun soma zuwa kasa a cikin shekara1960s, ya kai iyaka acikin shekara ta 1970. Ainihin abinda ya hadasa karin lalacin shine halakar dukannin bishiyoyi da kuma watsi da harakar barin fili ba nomawa.

Mai watsa labarai:
Mai yakawo kuka sake aikin nomar ku?

Ali:
Lamarin ta zamo kalubale ga dukannin manoma
,
Filaye sun zamo ba’a iya mnoma akan su, yashi ta rufe shukin mu, itatuwan sa wuta ko na harakokin da dama na da wahala. Mun sake aikin gonar mu muna barin kananan bishiyoyi akan filayn mu. CARE International ce ta gudana da wani aikin goyan bayan ga wannan shawarar tamu.

Mai watsa labarai:
Ta yaya kuka sake aikin nomar ku?

Ali:
An kai wani lokaci , da kowa ya gano muhimmancin barin kananan bishiyoyi ko iri a cikin fili. Manoma suka soma rungumar waddannan bukasheshan harakar tare da goyan bayan aikin.Haka kuma muke kulawa da kananan tofowa da kanana bishiyoyi da suka sake shukowa akan jijiyoyin tsofin bishiyoyi.Bayan hakan,mun kirkiro gun reno ga nau’in bishiyoyin gida kamar Hyphaene thebaica, Acacia albida, da Parkia biglobosa (Lura ga Editore: dubi sunayen gida a karshn rubutun nan). Mun kuma soma amfani da sharan iatatuwa-matattun gannye, tsirai da reshoshi da suka fado kasa- a maimakon taki

Mai watsa labarai:
Yaushe ka gano cewa yunkuri nan na tasirin gaske ga ciyayi dake filin ka

Ali:
Mun soma yunkurawa shekaru 25 baya,amma an rungume fadada shi shekaru 18 da suka wuce.

Mai watsa labarai:
Menene tasirin ta ga albarkatun gonar ka?

Ali:
A lokacin da aka halaka daji gaba daya, amfanin girbin hatsi akan kowani hectare 90- 120 na kilogram kawai ko kimani gungun 13-17. Amma a yanzu, tare da karin ciyayi, muna iya samun kilogram 315 zuwa kilogram 455 a kowani hectre.Idan muka yi amfani da taki albartun zai kai kilogram 700 akowani hectre.

Mai watsa labarai:
Ta yaya shirin FMNR ta shafi kuidin?

Ali:
Harakar gona na da riba a yanzu. Bishiyoyi na samar da abinci ga dabbobi, itattuwan sayarwa, ga sa wuta da gini.Lokacin rikicin abinci daga 1999-2000, dangi da dama sun iya sun rayu, mungode da sayar da itattuwa.

Mai watsa labarai:
Menene tasirin aikin da mata suka gudanar?

Ali:
A yanzu akwai karin ciyayi,maza na saran itattuwa acikin filaye su aza zuwa gida suna amfani da tarragon da suka saya da kudi daga gona, gandun daji da kiwon dabbobi.Don haka mata na samun saukin aiki na nemar ,sara, ruwa da nika hasti. Ada, mata ne da zasu yi wannan aiki.

Mai watsa labarai:
Yaya kake misilta sabon arzikin nan?

Ali:
Tun da muka soma sabuwar taku,. Muna da kwamitin aikin sa ido mata da maza.Kwamitin na da halakin kulawa da yunkurin manoma su bayar da labari ga sarakunan kyauye idan mutane suka taki ka’idodin yanda zasu yi harakan filaye.Idan bshiyoyi suka yi tsayi, mun kafa kwamitin misiltu, wadda ta hada kan kyauyuka kadan a unguwan Dan Saga.Tare da goyon bayan IFAD da hukumar gwamnati game da mahali,kwamitin ta buda kasuwannin karkara na itattuwa,da kwamitin ke misiltu.Ana kasa kudi daga wannan kasuwar kashi kashi a saka ta matsayin jari a cikin FMNR, unguwa da hukumar gwamanati game da mahali da kwamitin.Sayan katako daga kyauyawa dake sayar da bishiyoyin filayen su ke taimaka wa kasuwar.

Mai watsa labarai:
Muna godiya, Ali, da kayi wannan firan, da kuma ka bamu labarin sanin aikin ka.

Ali:
Muna godiya da ka taho nan kuma ka nuna sha’awar ka ga yanda muke rayuwa.

Acknowledgements

Gudumowa: Sanoussi Mayana, Prèsident de l’ONG RDD Le Micro Vert, a Farm Radio International broadcasting partner.
Nazari: Chris Reij, Center for International Cooperation, VU University, Amsterdam.

Sanannun sunayen nau’in bishiyoyi da akaambata a cikin rubutun:

Acacia raddiana, da aka kuma sani da Acacia tortilis:
Larabci: talh, sayal, hares
Turanci: umbrella thorn
Fulanci: chilluki
Kanuri: kindil
Kouka: garatt
Mauritania: tamat
Swahili: munga
Toucouleu: bakan tchili,
Wolof: sandandour

Hyphaene thebaica:
Amharic: zembaba
Larabci: dom
Turanci: gingerbread tree, doum palm
Swahili: mkoma
Tigrigna: arkobkobai, kambash

Acacia albida, da aka kuma sani da Faidherbia albida:
Afrikaans: anaboom
Amharic: grar
Larabci: afrar, harac, haraz
Bambara: casala
Turanci: winter thorn, apple ring thorn tree, apple ring acacia, ana tree, white thorn
Faransanci: arbre blanc, kad
Ndebele: npumbu
Portuguese: espinheiro-de-angola, espinneiro
Sepedi: mogabo
Setswana: mokosho
Shona: mutsangu
Swahili: mgunga, mkababu
Tigrigna: aqba, garsha, momona
Venda: muhoto
Wolof: cad
Zulu: umHlalankwazi

Parkia biglobosa:
Bambara: nere
Diola: enokay
Turanci: African locust bean tree, nitta nut, monkey cutlass tree
Faransanci: arbre à farine, mimosa pourpre, néré (Senegal)
Gourmantché: budugu
Hausa: dadawa, dawa dawa
Kanuri: runo
Mandinka:nér, nété, netto
Swahili: mkunde, mnienze
Mooré: duaga or ruaga
Portuguese: farroba
Wolof: houlle

Information sources

Fira da Mr. Ali Miko, president of la grappe de Dan Saga, Department of Aguié, Jihar Maradi, Jamhoriyan Niger.