Jindadin dabbobi: Dabba da aka kula dashi sosai dabba mai albarka ke nan

Lura ga mai watasa shiri

Save and edit this resource as a Word document.

Dukannin dabbobi nada da ainihin bukatu ,kamar abinci d a ruwa da gida mai kyau.Amma dabbobi kuma nada bukatun a kula da su da kyau.Wannan ya hada da rayuwa a cikin mahali walalle, ruyuwa da wasu dabbobi, da kiyaye wasu yanayi dake gajiyar da dabba.

Idan dabbobi suka samu kulawan gaske, wannan nada da babban amfani ga mai su. Dabbobin gida da suka samu kulawa da kyau na samar da nono da yawa.,suna girma da fadi, su samu ‘ya’ya masu cikeken lafiya.Namar su nada darajar gaaske.

Wannan rubutun na bulowa da wasu muhimmin shawara game da jindadin dabba, kuma yana amfani da saukin labarin wani mutun da dan sa da saniyar su wurin bayani waddan nan shawarwarin..

Damuwa game da muhimmacin jidadain dabba na kara fadada da wuri-wuri a matsayyin kasashe.Hukumar lafiyar dabbobi ta duniya tana aiki ta kafa matsayi ta duniya game da jindadin dabba. Za’a iya samu karin labarai daga dadalin gizo http://www.oie.int/eng/bien_etre/en_introduction.htm

Wannan rubutun firan mutun biyu ne masu wasta shiri.Mai watsa shiri zai yi zancen jindadin dabba.sai ya bayar da wata shiri a labarai.Akwai hannyoyi da dama da za’ayi amfani da rubutun nan. Zaka iya a sawake ka rungumi wannan rubutun wa tashar ka ta sake zantukan labarin. Zaka iya watsa rubutun da ka runguma sai ku kewaye teburin tattauna jindadi dabba.. Waddan da zasu tattauna su hada da makiyayan cikin gida, Kwararru a haraka dabba daga malaman gona, masu kiwon kaji da sauran su.Zaka iya zabar fadada labarin ta shirya dan wasan kwaikwayo, da ta dogara akan zancen jindadi dabba da akayi zance sa a cikin.

Rubutunsa

Mai shiri 1:
Ina kwana kuma barka da zuwa ( ambaci sunar shirin ko sunar tashar) Suna na.

Mai shiri 2:
Ni kuma nine. Barka da saduwa da ku a shirin jindadin dabba.

Mai shiri 1:
Muna dogara akan dabbobin gida-suma suna dogaro akan mu.Sai yasa, tabattar da rayuwa mai kyau ga dabbobin mu nada hankali a ciki kuma yana da kyau ga mai shi.

Mai shiri 2:
Gaskiya ne.Bara muyi zance jindadin dabba.Menene dabbobi ke bukata su girma da kyau, ta samar da nono ko ta haihuwar yara masu cikeken lafiya? Mai ke shafar kyaun rayuwar su? Ko zai yiwu cewa wasu lokutan muna yin ababan sa zai hadasa gajiya fiya da yanda dabbobin za su iya jurewa

Mai shiri 1:
Tamnbayoyi masu kyau. Muna amfani da babbobi wurin aikin sufiri,su ja abin noma ko tarrago, domin nono, nama da ababa da dama. Don haka, jindadin dabbobi nada da mihimmanci ga masu shi. Idan akayi rikon lalaci, dabba baza tayi albarka ba,darajar ta sai yayi kasa sai yasa makiyayi asarar kudade da yawa.

Mai shiri 2:
Don haka kulawa da dabba da kyau nada riba.Idan aka walakantar da dabbobi, aka fita iskar su ko aka barsu a yanayi mara kyau, zai kawo asara ga makiyayin. Amma muna jin labarai yana faruwa duk lokaci. Mai yasa?

Mai shiri 1:
Bara mu saulari labnarin wani makiyayi dake da dabbobi kadan,watakila zamu gano wani abu.

Mai shiri 2:
Wani makiyayi nada dabbobi kadan akan karamin fillin sa.Akwai raguna da awaki kadan,da saniya daya da yake tatsar nono.Wasu lokutan dan sa na taimakawa da dabbobin.Babu shaka,mutumin ya lura cewa a ranakun da dan ke taimakawa, sai saniyar ta shiga damuwa.Bata cin abinci kuma ba murna kuma tana da wuyan al’amari.Wata rana sai tana dingishi.

Mai shiri 1:
A tunanen ka mai ke faruwa? Ko kana da wata ra’ayi

Mai shiri 2:
Kamin mu koma ga labarin mu, bari muyi zance da dama game da kulawa da dabbobi.Ta yaya zamu yi bayanin lalacin kulawa da dabbobi? Watakila, ba banbanci kwarai da abinda ke faruwa da mutane idan muna karkashin yanayin tsananin gajiya.

Mai shiri 1
: Haka ne. Idan muka tsorata ko muka damua ko wasu sun muzguna mana, muna nuna hallayya daban daban.Idan bamu ci ko sha da kyau ba, lafiyar mu na tabarbarewa.Idan muka ji rauni, watakuila baza mu iya aiki ba kamar yanda muka saba,ko zamu samu wata illa.

Mai shiri 2:
Haka ke samun dabbobi. Idan dabba bata iya jure wa wahala acikin mahalin ta, kawai baza tayi kyau ba. Zata girma sannu sannu kuma ba zata girman daidai da wasu dabbobi ba,samar da nono kadan, ta rame ko tayi ciwo.

Mai shiri 1:
Wasu dabbobin sunfi wasu jiyewa. Wanan ba ana nufin yawan jiyewa ta gajiyan jiki ko jin rauni bane, amma ga wasu matsaloli a wasu bangarori kamar lafiya, haihuwa ko lafiyar kwakwalwar dabba.

Mai shiri 2:
Amma a kullun akwai alamu ga kulawa da dabbobi. Yi tunane akanm waddanan alamun:

  • Dabba bata ci da sha da yawa
  • Dabba da kamannun rashin lafiya , watakila idon yayi kamar gilashi, gashi na fita, hanci na zuban ruwa
  • Dabba bata haihuwa ko tana rasa ‘ya’yan ta gun haihuwa
  • Dabba na wasu halayya kamar cije-cijen gida, ko lasar jikin ta kai da kai
  • Dabba baya girma da kyau sabili da shekarun sa an animal is not growing well for its age
  • Dabba ya rame ko baya harakawa baya ma’amala da wasu
  • Dabbaa tayi hushi da mutane ko wasu dabbobi

Mai shiri 1:
Waddan nan zasu iya zamowa wasu alamun cewa, ana muzguna wa dabba ko bai saba da mahalin ba.Akwai misalan irin waddan nan alamun da dama.Zai iya yiwuwa ka taba ganin wasu ko dukannin alamun, watakila cikin dabbobin makwabcin ka, ko naka na kan ka.Amma wasu alamun nada dan sauki, yana bukatan a lura da kyau.Dayan ka’idae itace maimakon ka dora hankali kan inda zaka so saniyaa ta tafi , watakila zai taimaka ka fahimci abinda yasa bata son zuwa gun

Mai shiri 1:
Kada ka manta cewa dabbabiobin gida na rayuwa a mahalin mutane ne. Ko da basa iindadin da kyau sabili da ana muzguna musu, sabili da mahali mara kyau da suke rayuwa a ciki, ko sabili da ba’a biyan bukatuuin su da kyau, har wayau shi mai shin zai magance matsalar.Kulawa da dabbobin da kyau zai amfane ka da dangin ka a karshe

Mai shiri 2:
Don haka, kulwa da dabba da kyau nada muhimmanci ga dabba don kan sa. Lalacin kulawa na da tata illar.

Mai shiri 1:
Idan dabbobi suka gaji ana yanka sune, darajar namar ya lalace, yana hadasa rashin samun nama mai albarka, darajar sa a wurin dahuwa baya da kyau.Lokaci –lokaci, ba’a iya adanar namar kuma.Wani asarar shine rashin kulawa da dabba da kyau gajiyayyun dabbobi nada matsala da yawa na juna biyu da gun haihuwa, da haifar jinjijirai kadan masu lafiya

Akwai wasu muhimman binciken kimiya dake nuna cewa mutanen dake muzguna wa dabbobi nada alamar muzguna wa mutane.A karshe, wahalar da dabbobi na take ka’idodin adini da kuma abinda manya mutane tsakanin al’uma ke sa idon gani.

Mai shiri 2:
haka kuma, menene abinda dabbobi ke bukata su yi kyau? Hannya daya da za’a iya yin bayanin ainihin bukatun itace ta binda zaka kiyaye, ko abinda zai ba dabba walwala daga.

Mai shiri 1:
Walwala biyar nan sune:

  • Walwala daga kishi, nyuwa,da rashin abincin mai sinadirai- tabattar da haramar samun ruwa mai kyau da abinci dake samar da cikeken lafiya da kuzari.
  • Walawala daga rashin jin dadi- ta samar da mahali da ta dace, har da dakuna da gun hutu mai kyau
  • Walwala daga ciwo, rauni , cuta- bayar da kiyayewa ko kulawa da lifiya kai da kai da jinnya.
  • Walwalar bayanar da rayuwa yanda yake- ta samar da fili mai yalwa, kayan aiki masu kyau, hada dabbobi da irin su..
  • Walawala daga tsoro da gajiya- tabattar da yanayin kiyaye tabuwar kwakwalwa.

Mai shiri 2:
Waddan nan ne ainihin bukatun. Idan ba’a kulawa dasu,ba zamu iya sa ido dabbobi su girma da kyau kamar ynda zasu iya yi ba. Kuma baya da kyau ga mai shi.

Mai shiri 1:
Yanzu bara mu koma ga labarin mu na mutumin nan da saniyar sa.Wata rana, bai tafi gari ba.Sai ya dau shawarar dubar abinda dan sa keyi.Komai yayi daidai.Sai lokacin ciyarwa ya kai , sai ya ga dan sa yasa hatsi da gannye da aka yanyanka kadan a lungun rufar kuma ga duhu.Saniyar bata shiga nan take ba, sai dan sa ya dau karfe ya daka mata kan kafar ta yana tilasta mata shiga lungun mai duhun.

Mai shiri 2:
A hikimance, sai mai saniyar ya tsoma baki. A cikin hanzari yayi wa dan sa bayanin cewa saniyar bata shiga gu mai duhu inda bata gani da kyau Zai zamo zabi mai kyau ka jannye abincin ka samar da haske sosai, ko kaba dabbar lokaci taci abincin da kanta.

Mai shiri 1:
Sai kuma ya zamo cewa, acikin lungun mai duhun, akwai wani tsini daya bola kai akan bangon da yayi wa saniyar rauni a kafar ta.Tare da dan suka gyara bangon suka matsa da gun abinci.Bayan hakan saniyar tayi kyau

Mai shiri 2:
Tuna : Kulawa da dabba sosai bai kamata yazamo lamarin kudi ba.Hakikanin zance, ana kiyaye kudi idan aka kiyaye asara mai tsadan gaske.A karshe , dabba da aka kula da ita sosai zata yi kyau,ta girma da wuri,ta samar da ababan amfani,sauki tafiyar da ita, tana da sha’awar gaske ka kasance mai ita.

Mai shiri 1:
Gaskiya ne.Dabba dake cikin yanayin jindadi nada darajar gaske gare ka.Jindadin dabba hakin kowa ne.

Mai shiri 2:
Nine (sunar ka gaba daya),nake salama da ku a yanzu.

Mai shiri 1:
Ni kuma nine (sunar gaba daya) Ku kasance lafiya.

Acknowledgements

Gudunmowa: David Trus, Professional Agrologist, Ontario Institute of Agrologists. David also coordinates animal welfare issues for the Department of Agriculture & Agri-Food Canada.