Kasadar mabukata: Wani ma’aikacin lafiyar dabba unguwa na taimaka wa tafiyar da cutar Newcastle

Kiwon kaji da noman zuma

Lura ga mai watasa shiri

Save and edit this resource as a Word document.

Kaji wasu irin tsuntsaye ne masu sauki kiwo sabili da suna iya kewayawa su kiwo da walwala akan abinci da kenan.A wasu kalamun, ‘yan zangon walwala ne.Kuma, kaji na yaduwa a cikin sauki.Amma suna da hadrin kamuwa da babban cutar da babu magani. Cutar Newcastle Ko da yake baya da magani, akwai alurar riga kafi ga cutar.Amma makiyaya na kasa yi wa kajin su alurar sablili da rashin sani ko sabili da alurar nada tsada.Lokaci-lokaci, ana sayar da maganin acikin mannyan kwalabe da ze iya jinnyar ‘daruruwan kaji.wannan na da tsadar gaske ga makiyayan dake da kaji kadan Hakan yasa alurar riga kafi a unguwan ga kaji da ma’aikacin lafiya dabba unguwan keyi ra’ayi ne mai kyau,.

A cikin unguwannin da dama, ana samu karancin likitocin dabbobi. Pravetererarian, da kuma ake kiran su da suna ma’akatan lafiyar dabba unguwa ko masu aikin sa kai ga dabba , na taimakawa da aiki inda ba’a likitan dabbobi.Masu aikin sa kai ne da basa karban albashi,amma suna rayuwa ne da kudin kasdan da suke karba tamkar ladan aiki..Ana horar da su su duba kuma suyi jinnyar dabbobi da dama, su aika wasu cuttuukan zuwa ga likitocin dabbobi.Makiyaya kai da kai suna sayan magunguna su samar da sufri ga ma’akatan lafiyar dabbaobi unguwa tafiya da dawowa gonakin su.

A cikin rubutun nan, ma’akacin lafiyar dabba unguwa na fada wa ‘yan kyauye cewa, ana samun magungunan alurar cutar New castle acikin adadin kaji masu yawa ne kawai,kamar 300 ko sama.A ciin wasu kasashen Africa,za a iya sayan alura mai karamin adadi.Kuma,a cikin wasu kasashen Africa kamar . Zambia, Mozambique da Ghana, ana samun alurar da ba sai an adana a firiza ba.Kayi bincike yanayin kasar ka

Wannan rubutun karamar-wasan kwaikwayo ce dake kara haske akan bukatar yin alurar riga kafi ga cutar Newcastle da amfanin samun ma’aikacin lafiya unguwar ka.Hannya biyu da za’a iya amfani da rubutun nan sune ko a rungumi wannan wassan kwaikwayon ga masu saularen ka ko ayi amfani dashi tamkar kwarin gwiwa ka shirya gajeran wasan kwaikayo kan ka akan cutar dabbobi unguwar ka.

Rubutunsa

Mai fira:
A cikin kasashen Africa da dama, har daMalawi, mafi yawancin makiyaya nada akalla kaza daya Waddannan kajin na gida ne suna yawaon kiwatawa.A cikin wasu kalamun kaji ne dake sake.Barkewar cutar Newcastle ze iya a cikin sauki ya kashe duk kajin kyauyen. Ana iya kiyaye cutar Newcastle da alurar riga kafi. Don haka mai yasa makiyaya da dama basa sayan maganin alurar riga kafi wa kajin su?

FX:
Sautin buga karfe da karamin hamma

Wife:
Ubangida na Neddy, yaya kake gyaran keken hawan a kurare lokaci? Ina zaka je?

Neddy:
Haba! Uwargida ta…ban zan je ko ina ba a yau, Ina shirye-shiryen gobe ne. Kin san lokacin rani na gabatowa….

Wife:
(Tana ba’a) Na dauka wani sa mai ciwo ne. Tun da ka zamo ma’aikacin lafiyar dabbobin unguwa, ko yaushe kana hannya tafiya

Neddy:
Kina murna yanzu, uwargida ta?

Wife:
I, Mai asa bazan yi ba?

Neddy:
Duk abinda ake nufi da zamowa ma’aikacin lafiyar dabbobin unguwa kenan. Bama rayuwa da shi, uwargida ta?

Wife:
Na sani, Amma kamata yayi mutane su baka wasu lokutan hutu.Suna kiran ka duk lokaci.Harma tsakiyan dare! Zo nan! saniya tayi kaza, allade nada wanca matsala…Ba lokacin hutu.

Neddy:
Ashe kina kulawa dani kwarai haka?

Wife:
I ina yi, masoyina.

Suka yi dariya su biyun.

Wife:
Amma Neddy, naji kana zancen wani abu game da lokacin rani na gabatowa. Menene alakar dake tsakinin lokacin rani da zuwa gari gobe?

Neddy:
Kisani cewa lokacin rani busahen lokaci ne. Amma ko kin kuma sani cewa lokacin rani muke rasa kaji da dnma da suka yi yawa lokacin damana ga cutar Newcastle?

Wife:
I, na sani.

Neddy:
Yanzu nan lokaci kenan da zamu yi wa kajin mu alurar riga kafi- Kamin Newcastle ta sayo kai.Kusan watanmnin uku ke nan da muka yi wa kajin mu na kyauye nan da kewayi alurar riga kafi.

Wife:
ka nen, kana son ka sayi wa kajin mu magungunan riga kafi ne?

Neddy:
A’a! ba ga kajin mu kadai ba, amma….

Wife:
(Ta shiga Maganar da hushi) Amma mai? Kana son ka fuskancinn abin kunnya kamar baya? Ka manta yanda mutane suka ce kana yiwa kaji alurar riga kafi kawai saboda kudi ne?

Neddy:
Ina tunawa da kyau uwargida ta, amma kin sani

Wife:
(Tana mai karban maganar) Ka sani? Kada kaci gaba da gardama. Gobe idan ka je gari ka sayi maganin alurar ga kajin mu 10. Shi kenan!

Neddy:
A‘a. Kin san ba kananan kwalabe ga kaji 10. Shago daya ke sayar da magani alurar kaji 1000 a MK850 wani shagon kuma na sayar da maganin alurar kaji 300 a MK600. Don haka….

Wife:
(Tana mai karban maganar) don haka sayi na kaji 300, kayi amfani dashi ga kajin mu 10 sai kayi jifa da ragowar.

Neddy:
Za muyi asarar kudi. Ma’ana zamu yi alura a MK60 ga kowani daya maimakon MK10, da zan iya caji inyi riba.

Wife:
She yasa gasiya ne fadar da mutane keyi – cewa kana ksuwancin ne?

Neddy:
Uwar gida ta, ki tuna abinda ya bani sha’awar aikin sa kai in koyi yanda ake alura. Ba saboda a kawo karshen matsalar lafiya dabbobi kyauyen nan bane? Ina jin mafarkin mu shine mu ceto kyauyen mu daga cutar dabbobi da kuma matsalar da za’a iya kiyayewa?

Wife:
I, na tuna kuma dalili haka ne na bari kake yin shi yanda ka shirya.

Neddy:
Uwara gida ta kenan ke zance

Suka yi daioya su biyun

Sakiyar fage. Buga waka, sai ka rike ta kasa-kasa.

Mai fira:
Neddy ina sane kwarai cewa sayan babban kwalban maganin alura ga kaji kadan asarar kudi ce.Ko ka taba jarraba makwabcin ka cikin yi wa kajin ka alurar riga kafi? Yana da wahala! Ina zancen famar sa jama’ar baki daya cikin kiyaye cutar Newcastle?

Fagen waka sai ka shude ts tayi kasa-kasa

Mai fira:
Neddy ya san cewa tun da yayi wa kajin alurar riga kafi watannin uku da suka wuce ba labarin cutar Newcaslte, bama a kyauyuka da basu yi wa kajin su alurar riga kafi ba. Ko ‘yan kyauyen zasu yarda ya yi wa kajin su alurar wannan lokacin kuwa? An yi kiran mutanen zuwa fadar sarki kuma suna masu jiran suji abinda ya sa akayi kiran su.

FX:
Ayirin a farfajiyar fadar sarki

Shugaban kyauye:
Jama’a kuyi shuru, kuyi shuru don Allah.

Mwale:
(Ya sha ya bugu kuma yana waka da rawa a sannu yana gabato fadar mic a kashe) Ayo! Ayo! Ayo! Bayar da gilashin beer a cike!

FX:
mutane na dariya

Wife:
(Tana gunaguni) Dan‘uwa na Mwale na bani kunnya. Koyaushe a buge.so nawa yana kunnyata matar sa?

Mrs. Kwenda:
I koyaushe ‘dan uwra ki ya bugu.Amma a wani bangare kuma,dan’uwarki Nwale ma’aikaci ne kwarai, idan zai rage shan barasa zai yi galaba.

Wife:
Kana da gaskiya.

Shugaban kyauye:
Mallam Mwale! Mallam. Mwale!

Mwale:
Sarki!

Shugaban kyauye:
In mai cewa ayi shuru, don Allah

Mwale:
(Da taushin lafazi) Yayi, sarki, yayi, zan zauna kusa da suriki na Neddy.Amma da farko ka fada mana abinda yasa ka kira mu…Muna son muje gida.Muna da wasu…. Muhimman ababa da zamu yi… muna sha ne.

Wasu mutane suka yi dariya. Wasu na gunaguni na goyan baya wasu kuma na hamayya da Mwale.

Shugaban kyauye:
Mwale! Shuru. Ka tuna zaka biya diya idan kayi rashin kunnya a farfajiya na.

Mwale:
Na tuba, sarki, na tuba sarki.

Shugaban kyauye:
(Yayi hucin samun walwala sai ya sake zance) Taron nan wani mai aikacin sa kai namu na gida ya kira,dan mu, mutumin da ya ba yawancin mu damar samun mamaka irin shanu ta barbaran alura da hannayen sa masu dabo-dabo. Ku bari muyi wa Mr. Neddy.

Mutane:
(kuwace-kuwace da bushe-bushe) Neddy! Neddy!

Neddy:
(Magana a yayin da mutane ke cigaba da kuwace- kuwace) Na gode, sarki, da wannan baiwan.

Mwale:
Jeka kai tsaye ga zance kada ka jinkirtar da mu kuma.

Mrs. Kwenda:
(Da murya mai tsanani) shuru! Shuru! (Tsit gabaya) Ku bari mu saulari abinda ma’aikacin lafiyar dabbobi na unguwa ya kawo mana. (Shuru).

Neddy:
(Yana mai gyaran murya) kamar yanda kuka sani, watannin uku sun shude tun da muka yi wa kajin mu alurar riga kafi, kuma lokacin rani mai hadarin gaske na gabatowa inda cutar New castle zata iya sake kama kajin mu.

Su duka:
I

Neddy:
Lokaci ke nan da zamu sake yi wa kajin mu alurar riga kafi.

Mr. Kwenda:
Yaushe kake nufin yi wa kajin mu alurar riga kafi?

Neddy:
Mmm…Yau asabar. Domin mu baka lokacin karban kudi, yaushe kake jin mu aikata hakan, Mr. Kwenda?

Mr. Kwenda:
Safiyar talata, sabuwar sati.

Neddy:
Kowa ya yarda? Talatan sabuwar sati!

Su duka:
I

Neddy:
Kada ku bari kajin ku su fita ranar talata sai in a musu alurar riga kafi.

Su duka:
I

Mwale:
Wannan lokacin nawa ne akan kowani kaza?

Neddy:
Sabili da jama’a da dama na da kaji acikin kyauyen nan, na rage kudin daga k10 zuwa K5 akan kowani kaza don in bautace ku, mutane na.Wannan ragowar kashi 50 bisa dari kenan.

FX:
(Kowa yaji dadi kuma ya kuwata) Neddy! Neddy!

Mwale:
(Rashin amincewa) Wannan yayi yawa kwarai, wannan yayi yawa kwarai

Neddy:
Kwacha 5 yayi araha .Nawa kake kashe wa akan giya? Ainihin abinda ake karba akan kowani kaza a cikin unguwani makwabta shine K10.

Mrs. Kwenda:
Mai yasa kake caji daban? Mai yasa kudan kadan akan kaji da yawa?

Neddy:
Na gode, Mrs Kwanda, da wannan tambayar.Tuna lokacin da na fada miki cewa ina sayan maganin da kudi na don haka ina karban dan wani abu ne in biya bashin magani da aiki na? Idan kaji kadan kenan sai in kara kudin saboda na maida kudi na.

Mwale:
Karya kake yi. Yaya baza ka adana maganin kayi alurar a wani kyauye ba?

Neddy:
A’a! da zaran an buda kwalban,kamata yayi nayi amfani da abinda ke ciki kamin awa biyu ko hudu ko zai shude ya zamo mara amfani.

Mwale:
Kada ka zo gida na.

Neddy:
A koyaushe ina nanata maka wannan: zaka iya sayan kwalban maganin alurar riga kafi mai tsada ga kajin 300 idan kana da wannan kudin. Kamar Mwale – Ina jin zai sayi na kansa.

Mrs. Kwenda:
Mun fahimce ka.Ranar talata, ka rabuda waddan da basa son alurar riga kafi.Muna da kaji kadan.Mai yasa za’ a yi amfani da kudi da yawa akan kaji biyu maimakon K10 ga waddan kaji

Neddy:
she yasa ranar talata, kowa.

Su duka:
I

Mwale:
Suriki na Neddy, Nace ban son ka zo gida na., zan bi ka da karnuka idan ka zo.

Shugaban kyauye:
(Yana kuwa) Zaku iya komawa gidajen ku, Amma ku tuna ranar talata da safiya.Kwacha 5 akan kowani kaza.

Su duka:
(kashe mic) I

Mwale:
Neddy, Neddy, kada kazoo gida na.Na nanata. Gida na kada kazo.

Neddy:
Kada ka bani kunnya, Mr. Mwale. Bara muyi zancen akan hannyar mu na tafiya (Ga shugaban kyauye) Na gode, sarki.Zan gan ka ranar talata da safiya.

Shugaban kyauye:
(Kashe mic) Kada ka manta da kaji, Neddy.Zan halarci wata taro amma ka zo.zaka samu komai daidai.’yan uwan ka da uwar su zasu taimaka

Neddy:
Kada ka damu, sarki, zan kula da wannan (shuru, sai ga Mwale.) she yasa kai, suriki na Mwale.Mai yasa kai, suriki na, a kulun ke bani matsala?

Mwale:
Kana cutar mu.

Neddy:
Haka kake tunane? Ka taba ganin cutar New Casle a cikin kyauyen nan tun da aka soma aiki alurar riga kafi?

Mwale:
Haka kuma ban gani a kyauyukan da nake zuwa shan giya ba, watanni takwas da suka wuce.Har ma a cikin kyauyukan da basa yarda kayi wa kajin su alurar riga kafi.

Neddy:
Wannan lokaci suma sun nemi in yi wa kajin su alurar riga kafi

Mwale:
(Dariya) Ha! Ha! Ha! Surikina, kayi kokarin cutar su kuma

Neddy:
Mwale, ka saulare ni.Wannan lokaci ne muhimmi da zamu yi wa kajin mu alurar riga kafi, domin rani na gabatowa.

Mwale:
Cuci waddan da basu san abinda zasu yi da kudin su ba. Ba ni ba.

Neddy:
(hushi da gajiya) yayi! Ka dauka kowa jahili ne amma kai keda wayo. Na yarda! Bazan zo gidan ka in yi alurar riga kafi ga kajin ka ba. Bye Neddy:

Mwale:
(Kashe mic) Suriki na kenan.Kada ka zo don Allah, Neddy.

Waka: Rike ta kasa-kasa

Mai fira:
Talatan ta kai.Neddy yayi wa duk kajin kowa alurar riga kafi face na Mr. Mwale. Wasu makwabta sun bari anyi wa kajin su alurar riga kafi, wasu kuma basu amince ba.Wata daya ta shude ba ’a samu labarin cutar NewCastle ba.wannan na nufin waddan da basu yi wa kajin su alura ba sunyi daidai kenan?

Waka: Ka shude ta yayin da ake shigar da FX

FX:
Cara da saifaya

FX:
Bugun kofa da karfi. Rike shi kasa- kasa.

Wife:
(Ta tashi mai gidan ta) Neddy! Neddy! Ta shi. Wani na buga

Neddy:
(Yana falkawa sai ya kuwata) wanene ke gun da wuri-wurinan?

Mwale:
Nine, surikin ka. Ka buda don Allah (sautin kaza mara lafiya)

Neddy:
Mai kake so da kajin ka?

Wife:
Neddy. Ka tashi kawai,.ba ka jin wa na ne? (Ga Nwale) Ka jira, yaya na, yana zuwa.

Buda kofa da rufewa

Neddy:
(Da hushi) Mai kake yi, da kajin ka mara lafiya a cikin gida na da safiya wannan lokaci?

Mwale:
Haba, suriki na- da jin sauti kawai ka san kaji na b a lafiya

Neddy:
Dubi zawo koriya da ruwan kwayi. Kanu duk sun kunbure.Wannan cutar New castle ce.

Mwale:
Suna mutuwa, Don Allah surikina, taimake ni. Basu magani.

Neddy:
Mai kace?

Mwale:
Neddy, sai kayi hakuri, kaji na duk basa da lafiya kuma suna mutuwa.

Neddy:
Ni ma sai kayi hakuri, suruki na.Amma bazan iya taimaka maka ba

Mwale:
(Da banhakuri) Mai yasa ‘dan uwa mai yasa…..?’

Neddy:
Kamanta da yanda ka sani kunnya gaban kyauyen gaba daya?

Mwale:
(Yana durkusawa yana roko) Kayi hakuri, kayi hakuri, Baba (Lura ga Editore: Mwale na kiran Neddy “baba”sabili da yana son ya bashi dukannin girmamawa yasamu abinda yake so.)’yar uwa, taimake ni, fada wa mai gidan ki nayi nadama. Ko na durkusa ne?

Neddy:
A’a! A’a! Kada ka durkusa. Kawai bazan iya taimaka maka ba.

Mwale:
(Kusan ya kece da kuka) A’a? Neddy, don Allah ka taimaka mini.Wannan ne kawai inda na saka jari na, taimake ni, don Allah.

Neddy:
Mai yasa baka yi wannan tunanen ba lokacin da nake yiwa kaji alurar riga kafi?

Mwale:
Ban san abinda yazo kaina ba.

Neddy:
(Yayi dariya cikin hushi) Gaskiya dai, Mr. Mwale Idan cutar New Castle na da magani, da na taimaka maka.Amma ba’a warkar wa, alurar riga kafi ne kawai

Mwale:
To yi musu alurar riga kafi kawai don Allah

Neddy:
Yayi jinkiri kwarai- bana yi wa kaji masu ciwo alurar riga kafi.Kuma bana adanar maganin alurar don bana da firiza da zan adana shi.

Mwale:
Karya kake yi.Mun san baka da firiza a gidan ka, amma yaya kake adanar maganin da kake yiwa kajin muitane alura?

Neddy:
Ka tuna akullun ina shirya wa da muane ne kamin ranar alurar?

Mwale:
I, mai yasa?

Neddy:
Ina samun maganin kwana daya kamain ranar alurar. Ina arron akwati mai daukan sannyi sai mu zuba kankara a ciki

Mwale:
Mai yasa kake adanar maganin a gu mai sannyi?

Neddy:
Idan kana adana maganin agu mai zafi zai lalace.She yasa muke zubar da duk abinda ya rage

Mwale:
Ina jin nayi karatu da wahala.Ba zan nanata wannan uskuren ba kuma.

Neddy:
Zai fi kyau idan baka nanata ba, suriki na.

Mwale:
Daga yau tafiya a ko bayaushe zan yi wa kaji na alurar riga kafi ko lokacin ko ba lokacin yi ba.

Neddy:
Surikina ken an. Kayi tutanen irin kudin da zaka yi amfani dasu ka sayi sabbin kaji.

Mwale:
Kana da gasiya.Ala tilas zan kashe kudi na sayi sabbin kaji

Neddy:
Haka ne. Yanzu da ka san muhimmancin alurar riga kafi, bani K750 da zaka kashe akan kaza daya,sai na baka kaji uku ‘yan sati shida shida wato k250 ke nan ga kowani daya daga Mikolongwe.di na. (Lura ga Editor: Wannan irin, da aka sani da suna Black Australorp, nada kyau kwarai ga kwayi da nama, na da kariya sosaigame da kamuwa da cuta fiya da wasu irin. Makiyaya na musanya sanannu irin domin cin amfani a unguwan su.)

Mwale:
‘Yayan barbaran mannyan zakarun ka ne?

Neddy:
I

Mwale:
Na geode da tayin.Bana da kudi a yanzu.Zan yi wani dan aiki a lanbu mutane. Zan bar shan giya, har sai na sayi kajin nan.

Neddy:
(Yana dariya) Ha!Ha! kawai kada ka sake kashe waddancan kajin kuma, suruki na.

Mwale:
(Kashe mic) Na sani. Ba zan sake kashe su ba, surukin kwarai na. Zo ka sake auren wata kanwa ta ta biyu ya zamo alamar halin kwaran ka. (Lura ga Editor: Wannan wargi ne,A cikin Malawi, mutane naba surukannen su ‘yar su ta biyu su aura idan ya nuna halin kwarai da rauywar cigaba.Kwanan nan,mutane na ba’a da wannan tsohuwar al’dar )

Neddy:
(Yana dariya) Ha! Ha!

Mai fira:
Kundai ji tarihin Neddy ma’aikacin lafiyar dabbobi unguwa.Tuna cewa , idan kana da kaji kadan, kai da abokan ka zaku iya raba bashin maganin alurar riga kafin kajin ku saboda cutar Newcastle.Wani abin tunawa shine adanar magani a gu mai sannyi.Idan an buda kwalban,bazaka iya amfani dashi wata rana ba. A karshe , kada ka manta cutar bata da magani.Zaka iya wa kaji alurar riga kafi ne kawai kamin su kamu da cutar.

A madadin taron bitar labarin, frodusan shirin nan , Nine Gladson Makowa sai mun sake saduwa daku sabon sati.daidai wannan lokaci.

Acknowledgements

Gudunmuwa: Gladson Makowa, The Story Workshop, Blantyre, Malawi, a Farm Radio International broadcasting partner.
Nazari: Dilip Bhandari, veterinarian, Heifer International.