Hada hannyoyi daban daban ka kore tsuntsaye daga gonar shinkafar ka

Lura ga mai watasa shiri

Save and edit this resource as a Word document.

Manoma sun sane da cewa idan basu iya sun kore tsuntsaye daga gonar su  a karshen shuki ba, za su iya fuskantar babban matsala.Kai da kai akan aika mata da yara gona su kare ta daga tsuctsaye.Wannan nada tata matsalar gaske  domin hakan na kara nauyin aiki ga mata kuma yana hana yara zuwa makaranta.

Wannan shirin radiyo na samar da hannyoyin tsoratar da tsuntsaye da manoman shikafa  suka jarraba kuma suka yi amfani da su.Muna shawartan ka da ka bishi da shirye-shirye game da tsoratar da tsuntsaye  da manomar unguwan ka masu saularen ka suka bulo da su.Domin karin bayani game da misiltun tsuntsaye a gonar shinkafa, ka dubi rubutn 89.9 a cikin shirin nan, “kiyaye albarkatun shinkafar ka daga tsuntsaye”

Firan nan shirin ce da ta danganci  labarin da Robert Anyang daga AfricaRice, Tanzania da Léonce Sessou daga Centre Songhai, Benin.

Rubutunsa

‘Yan wasa

Mai wata shiri a radiyo

Mallamin gona: Dr. Panicle

Taken wakan shirin

Mai watsa shiri a radiyo:
Waddan nan manoma dake saularen ka a yau suna sane da cewa da zaran ‘ya’yan shinkafa suka soma girma. Lokaci ke nan da za’a dau hannyoyi da daman na kore manyunwatan tsuntsaye.A yau zamu tattauna wasu hannyoyi nan tare da malamin gona Dr. Panicle.

Barka da, Dr. Panicle.muna godiya da amincewa da gyayyatan mu.

Dr. Panicle:
Ina maraba da kai.

Mai watsa shiri a radiyo:
A wani lokacin shukowan shinkafa manomi zai soma tsoratar da tsuntsaye?.

Dr. Panicle:
Daga lokacin da hure ya bayana, manoman shinkafa kamata yayi su soma tsoratar da tsuntsaye.

Mai watsa shiri a radiyo:
Wasu hannyoyi zaka bayar da shwara akan su?

Dr. Panicle:
Ina bayar da shawarar hannyoyi daban daban da na ga manoma na amfani dasu a fili.Waddan nan an jarraba kuma ingantatun hannyoyi ne, kamar: amfani da zaren kaseti , hannyoyin layin tsoratarwa da tsarin mutun-mutuni da raga.

Mai watsa shiri a radiyo:
A cikin dukannin hannyoyi nan, wane ne yafi?

Dr. Panicle:
Dukannin su na aiki da kyau.

Mai watsa shiri a radiyo:
Du da hakan ma Manoma na Kokawa da Tsuntsaye Duk da layin tsoratarwa ko Shinfida zaren Tape cikin filin

Dr. Panicle:
sabili; da suna amfani da hannya daya kadai kuma suna cigaba da amafani da shi tsawon lokaci,Don haka,a cikin hanzari, tsuntsaye na gano hannyoyin kuma baya aiki sosai.

Mai watsa shiri a radiyo:
A cikin wanan lamarin, yaya zamu yi?

Dr. Panicle:
A tunane na abinda yafi shine kowani kwanuka kadan a kara sabuwar fasaha ga hannya ko hannyoyin a cikin filin.Ga shawarar ds zan ba manoma: Da farko, a kafa itatuwa kewayen filin sai a rataya zaren kaset akan itatuwan.Yi amfani da wannan hannya ga farkon kwanuka kadan

Mai watsa shiri a radiyo:
Bayan waddan nan‘yan kwanukan?

Dr. Panicle:
Sai a yi amfanii da slayin tsoratarwan kusa da juna. Hakan na nufin kana amfani da hannyoyi biyu lokaci daya ke nan.Zaran kaseti da layin tsratarwa.Bayan sati daya amfani da biyun hannyoyin. Bulo da hannyar mutun-mutuni.

Mai watsa shiri a radiyo:
Don haka a yanzu manomi na amfani da hannyoyi uku ke nan: zaran kaseti
,
da layin tsoratarwa da mutu-mutuni.

Dr. Panicle:
I, bayan ka dasa mutun-mmtuin ka ,lokaci ke nan da zaka daura musu leda mai ruwan bula.Haki kanin zancen shine,daidai lokacin da kaga tsuntsayen sun saba da hannyoyin ka a filin, lokacin kenan da zaka sake dabarun ka

Mai watsa shiri a radiyo:
Har zuwa lokacin da shinkafan zai girma da kyau, Ko baya da?

Dr. Panicle:
Ya danganci iri. Wasu irin shinkafa na shukowa a cikin karramin lokaci

Mai watsa shiri a radiyo:
To yaya idan irin ya dau tsawon lokici kamin ya girma?

Dr. Panicle:
A cikin wancan lamari, manoman shinkafa kamata yayi su cigaba da kiyaye gonar su daga tsuntsaye tssawon lokaci da karin sabbi hannyoyi.Riki amfani da mutun-mutni da leda mai ruwan bula, kuma haka raga ya kama tsuntsayen, kamar ragar kamun kifi. Yi amfani da duk waddan nan hannyoyi har girbi.

Mai watsa shiri a radiyo:
Radio presenter: Sai yasa abinda kake fada shine kowani kankanin lokaci manoma su kara sabuwar hannyar tsoratar da tsuntsaye akan waddan da dama can ke cikin filin.Bayan wadacan hannyoyin, ko kana da wata shawara da zaka bayar?

Dr. Panicle:
I, yi kokari ka kiyaye jawo tsuntsaye zuwa filin ka a zance ta farko.

Mai watsa shiri a radiyo:
Ta yaya zamu yi hakan?

Dr. Panicle:
Wannan lamari ne na kulawa sosai da filin sinkafar ka.Samar da duk wani muhimmi kulawa ga shukin shinkafar ka lokacin shukowa.Ga misali,manoma Rafin Senegal sun lura suna da matsaloli kadan idan suka riki filin su ba haki.Domin tsuntsaye na son cin ‘ya’yan haki,Haki zai jawo tsuntsaye zuwa filin ka.

Mai watsa shiri a radiyo:
Ko da wani abu kuma?

Dr. Panicle:
A karshe, Ina kira ga dukannin manomar shinkafa dake cikin jihar daya da su shuka shinkafan su lokaci daya, domin filin dake da girman mai dauke da shinkafan da ta tsira lokaci daya baza ta lalace da yawa ba.

Mai watsa shiri a radiyo:
Na gode, Dr. Panicle. Yaku masu saularen mu,ku kuma mun gode! Amfani da hada fasaha daban daban na kore tsuntsaye, kamar yanda Dr. Panicle ya fada,zaka kiyaye filin shikafar ka da kyau daga laatawan tsyuntsaye.

 

Don Allah ka sadu damu nan tashar idan kana da wata hannyar kore tsuntsaye da kake son ka bamu tasaraba.Zamu watsa ra’ayoyin domin amfanin wasu manoman jihar mu..hakan ya kawo mu karsen shirin mu na yau, Mun geode da saulare!

Shude taken wakan kawo karshen shirin.

Lura

Ya kai mai watsa shiri a radiyo, ka aiko mini da jawabin da aka samu daga masu saulare game da fasahar misiltun tsuntsaye ga Felix Houinsou at AfricaRice, by email: f.houinsou@cgiar.org.

Acknowledgements

Rubutu: Felix S. Houinsou, Rural Radio Consultant /Africa Rice Center

Nazari: Paul Van Mele, Program Leader, Learning and Innovation Systems/Africa Rice Center (AfricaRice).

Information sources

Léonce Sessou, Crop Production Unit/Centre Songhai, Porto Novo, Benin
Robert Anyang, Emergency Seed Initiative Project (AfricaRice), Tanzania

The Bill and Melinda Gates Foundation (BMGF), da USAID, da taimakon kudi.