Zabi mafi kyawon kwayar shinkafar ka ta jiko da tsinta

Lura ga mai watasa shiri

Sabiili da girbin shinkafa yayi kyau, Kwayan shinkafa mai lafiya na da muhimmanci. Ɗanye hatsi ko hatsi da kwari suka bata sune mafi karancin nauyi a cikin ma’auni fiya da lafiyayen hatsi.Don haka , za’a iya fidda su idan aka jika su a ruwa kamin a shuka. Hatsi dake da digo baki ko ruwan-kasa su kuma basa da lafiya.Amma waddan nan hatsin ba lalle bane su rashi nauyi ba don haka baza’a iya fidda su ta hannyar jiko ba. A cikin wannan lamarin,manoma na tsinta da hannu ne.Za’a iya yin haka da zaren an yi girbi,kamin a adana kwayar,ko kuma kowani lokaci kamin sabon lokacin shuki.Hannya biyun nan na taimaka wa Habaka kwaya.

A cikin wannan firam akan radiyo, Mr. Chabi Adéyèmi , wani mataimakin jami’in bincike a cibiyar Africa Rice Center dake Cotonou a Benin, na ba masu saulare umarni bi da bi game da fasahar yanda za’a aikata jiko da tsinta da hannu.

Wannan rubutun ta dogara ne akan ainihin fira.Zaka iya amfani da ita ta zamo kwarin gwiwa ga bincike da rubuta wata zance makamancin ta a unguwan ka.Ko zaka iya amfani da ita a tashar ka, kana mai amfani da muryan ‘yan wasa su wakilci masu magana. Idan haka ne, don Allah kayi kokari ka fada wa masu saularen ka tun da farkon shirin cewa muryoyin na ‘yan wasa, ne ba ainihin mutanen da akayi fira da su ba.

Rubutunsa

Mai watsa labarai:
Yaku Abokai,Ina kwana kuma barka da saduwa daku akan shirin radiyo game da harakar gona.Shirin yau zata dogara ne akan fasahar jika shinkafa da tsinta.

A nan dakin shirye-shiryen mu muna tare da Mr. Chabi Adéyèmi , wanda mataimakin bincike ne a Africa Rice Center dake Benin an kuma san ta da AfricaRice.Yana nan ne yayi zance akan muhimman fasaha biyu da zasu tauimaka wa habaka darajan kwayar shinkafar ka.

Mai watsa labarai:
Mr. Chabi, manoma wasu lokutan na ganowa wurin shuki cewa kwari sun lalata kwayar shinafar su ko ‘dannye ce.Ta yaya manoma zasu iya habaka kwayar su su iya samun girbi mafi kyau?

Chabi:
To da farko, manoma zasu iya samun kwarin gwiwa daga irin ayukan da manomar Bangladesh ke yi su samu kwaya mafi kyau. Daya a cikin hanyoyin ana ace da ita jikon kwayar hatsi.

Mai watsa labarai:
Ko zaka iya yi wa masu saularen mu bayani?

Chabi:
Kwarai ko, abinda yasa nake nan yau kenan!

Mai watsa labarai:
Muna saularen ka.

Chabi:
Haka ne, zan soma. Bayan anyi bakace, kwayar hatsin da basu cika ba da masu ramuka a cikin suna hadewa da cikakun hatsi masu lafiya.Abinda zaka yi shine ka raba waddan nan hasti banzan ta jika su a ruwa.

Mai watsa labarai:
Hakan yasa ake ambatar wannan fasahar da jiko!

Chabi:
Allal hakika, Yin amfani da wannan hannyar kamata yayi ka bi taku da dama.Da farko, ka zuba ruwa mai haske a cikin matari.Na fi son amfani da bokati.Sai ka kara gishiri ko sinadirin urea aciin ruwan sabili da ya sake yanayin ruwan.

Mai watsa labarai:
Ta yaya zaka gane lokacin da zaka daina kara gishuiri ko sinadirin urea?

Chabi:
Kayi ta kara gishiri ko sinadirin urea ko ma laka sai har sabom kwai da aka saka zai iya yawo kan ruwan. Matan Bangladish sun gano wannan hannyar cewa idan kwai zai iya yawo kan ruwan,yanayin ruwan yayi daidai ken an ga hannyar jika hasti., Mai bi, kara hatsin ka a cikin ruwan ka dama komai da hannu,Bayan wani dan lokaci,Duk hastin da ta lalace da marasa nauyi zasu yi samaman ruwan.

Mai watsa labarai:
Ina labarin hatsi masu lafiyan?

Chabi:
Hasti masu lafiya zasu saura karkashin matarin.Jiko wani aiki ne dake taimaka wa rabba kwaran hatsi masu kyau da marasa kyau..Kada ka manta ka hade gishiri da sinadiirin urea ko laka da ruwa domin sakamako mai kyau.Wannan ke kawo ‘danyen hatsi da marasa nauyi sama.

Mai watsa labarai:
Yayi kyau kwarai.,bara a gurguje in takaita fasahar ga masu saularen mu.Da farko kasa matari mai haske, ko kwano, bokati ko garwa, ka gane?

Chabi:
Kwarai, matari da zaka zabi ta dogara ne akan yawan hatsin da kake dasu.

Mai watsa labarai:
Da zaran ka samun matari, sai ka zuba ruwa a ciki.Sai ka hade wannan ruwan da gishiri da yawa ko sinadirin urea ko laka har sabon kwai ya iya yawo kan huskan ruwan.

Chabi:
I

Mai watsa labarai:
Bayan haka, sai ka juye hatsin cikin ruwa sai ka motsa sosai.Bayan dan lokaci dukan hasti marasa nauyi da waddan da kwari suka lalata su zasu taso huskan ruwan.Hatsi masu lafiya zasu saura kasan matarin. Sai, bayan dukannan, menene taku na gaba?

Chabi:
Sai ka fidda hatsin da suka lalace da waddan da basu cika ba dake yawo kan huskan ruwan Zaka iya bayar dasu ga kaji

Mai watsa labarai:
Yaya labarin lafiyayun hatsin da suka saura kasan ruwan?

Chabi:
Sai ka fidda su karkashin matari ka wanke da ruwa mai haske so biyu ko uku.Bayan haka zaka iya shuka su.

Mai watsa labarai:
Na lura cewa wasu lokutan akwai kwarar hasti mai digo baki da ruwan-kasan akan su.Da jiko za’a iya fidda waddan nan?

Chabi:
A’a, waddan nan hasti ba lelle bane su rashi nauyi ba, don haka baza su zo sama ba .Ga wannan lamarin, sai kayi amfani da tsintar hatsi da hannu.

Mai watsa labarai:
Tsintar hannu?

Chabi:
I

Mai watsa labarai:
Wannan baya daukar lokaci da yawa?

Chabi:
I, zai iya, samman ma idan kana da hatsi mai yawa.Amma idan iyali gabadaya suka taimaka,yana da sauri.Baka bukatan kayi duka a rana daya, Zaka iya yin sa a sannu, tsakanin lokacin shuki biyu.

Mai watsa labarai:
Na gode, Mr. Chabi, da lokasi a yau, da ka mana bayanin fasahar jika hatsi da tsinta.

Host:
Thank you, Mr. Chabi, for your time today, and for explaining the seed floatation and seed sorting techniques to us.

Chabi:
In maraba da kai, na ji dadi.

Mai watsa labarai:
Ya kai aboki manomin shinkafa, Kada ka manta kwara hatsi mai lafiya na nufin girbi mai kyau,Idan kana bukatan bidiyon din shiri akan haskaka kwara, busarwa da adana zaka iya saduwa da (Mai watsa shiri ya bayar da sunar mutumin gida ko kungiya da za’a sadu dawa dake rabba bidiyon shinkafa).

Acknowledgements

Gudunmowa: Felix S. Houinsou, Rural Radio Consultant/Africa Rice Center (WARDA)
Nazari: Paul Van Mele, Sugaban shiri, tsara koyo da kirkira/African Rics centre (WARDA)
Reviewed by: Paul Van Mele, Program Leader, Learning and Innovation Systems/Africa Rice Center (WARDA)

Information sources

The International Fund for Agricultural Development (IFAD) da taimakonm bincike tare da mata manomar shinkafa a filaye,da kuma juya bidyon shinkafa a cikin harsunan gida. Haka kuma zuwa ga.

The Bill & Melinda Gates Foundation da IFAD da taimaka wa wannan rubutun.