Lura ga mai watasa shiri
A cewar Majalisar Dinkin Duniya ta Mata, aikin kulawa “ya kunshi ayyuka da kulla dangantaka domin cimma bukatin lafiyar jiki, da lafiyar kwakwalwa ta manya da yara, tsofaffi da kuma yan kanana, masu raunin jiki da masu karfin jiki. Ya hada da ayyukan kulawa kai tsaye da ya shafi bada kulawa ga yara, tsofafi, mutane marasa lafiya, nakasasu, hade da ayyuka wadanda ba kai tsaye ba kamar su aikin gida, dafa abinci, goge-goge, debo ruwa, siyo abinci da kuma debo itacen dafa abinci…Aikin kulawa da ba’a biya ya na nufin ayyukan da mutane sukeyi a cikin gida ko kuma a cikin unguwanni wanda ba’a biyan su kudi amma sunayi ne don amfanin alumma. Yawancin ayyukan da ba’a biya ya fi samuwa a tsakanin yan uwa. Ana samun ayyukan da ba’a biya a matakin unguwanni ga mutanen da ke wajen gida (abokai, makwabta da kum alumma unguwa).”
A ko ina a duniya, kulawa yawancin aikin mata ne da yanmata. A nahiyar Afrika, mata na bada aikin kulawa da ba’a biya sau 3.4 fiye da maza. Wanan yana ha na su damar samun ilimi da aikin yi, ya na kuma shafar zamantakewar su da lokutan hutun su. Hakan yake taba lafiyar su da kuma kara musu matakin talauci.
A wanan shirin, zaka kara ilimi akan ayyukan kulawa da ba’a biya, hade da rashin daidaiton jinsi da ke tare dashi. Maudu’in sun hada da:
- Akwai bukatar nuna godiya da daraja ayyukan kulawa da ba’a biya da mata sukeyi
- Ayyukan kulawa da ba’a biya ayyukan ne na musamman
- Akwai bukatar kowa da kowa a cikin gida suna raba ayyukan kulawa.
- Rana guda a cikin rayuwar mata masu aikin kulawa da ba’a biya
- Boyayen fa’idoji da mata suke bayar wa a cikin ayyukan kulawa da ba’a biya
- Koyawa yara muhimancin raba ayyukan gida
- Talafawa ma’aikatan kulawa da ba’a biya hakkin alumma ne gaba daya.
- Taimakawa abokiyar zama da ayyukan kulawa na gida
- Ka ce a’a ga cin zarafi na jinsi akan ma’aikatan kulawa da ba a biya
- Masu ma’aikata na iya taimakawa ma’aikatan kulawa da ba’a biya wajen daidaita aikin su da sauran al’amuran rayuwar su
- Inganta damar samun kayan aiki ga jama’a yana taimaka wa ma’aikatan kulawa wanda ba’a biya
- Yadda kafofin yada labarai da masu fada aji zasu iya canza fahimtar mutane game da aikin kulawa da ba a biya
Wanan shirin sun banbanta a tsayi, wasu dakika 45-60 ne, sanan ana iya sa su a lokuta dayawa a cikin shirye-shiryen na lafiya, ko daidaiton jinsi ko kuma wasu shirye-shirye da suka danganci haka.
Lakanin shirin ana amfani dasu ne kawai dan a gane sunan shirin. Ba anyi sune ba don a karanta da karfi a cikin shirin.
Rubutunsa
Talla #1: Nuna godiya ga mata masu aikin kulawa da ba’a biya
Amma ko kunsan ko menene shima mai muhimmanci kamar aikin ku? Aikin da iyalin ku suke a gida.
Bacin an sha fama da aiki, ya na da kyau ace ka dawo ka tarar ana maka maraba a gida. Gidan da komai yake tafiya lafiya ya na baka nutsuwa a zuciya ka mai da hankalin ka wurin aikin ka.
Don haka yau, ka godewa iyalinka ga me da duk kokarin da takeyi a gida.
Talla #2: Ayyukan kulawa da ba’a biya ayyukan ne na musamman
Talla #3: Aikin kulawa da ba’a biya alhakin kowa ne
Irin wadanan ayyukan a na kallon su a matsayi aikin mata. Amma bai kamata a daura wa mata kadai nauyin wadanan ayyukan na kulawa da ba’a biya!
Kowa da yake cikin gida—maza da mata, har da yara manya zau iya taimakawa da ayyukan kulawa. A raba nauyin daidai tsakanin kowa da kowa.
Ka tuna gidan da komai yake tafiya lafiya lau bashi da banbanci da kamfani, ko opis ko kuma layin kera abubuwa—yana bukatar kowa ya bada gudunmuwar sa.
Saboda haka, mu hada kai domin samun gia mai albarka.
Talla #4: Abubuwan da aikin ke bukata: Rana guda a cikin rayuwa masu aikin kulawa da ba’a biya
MARIYA: Wow, Zainab, dubi bukatun aikin nan. Haukan yayi yawa.
ZAINAB: Ahaba, nasan bai kai yadda kike fad aba, Mariya.
MARIYA: Hmmm, zaki gani ai. Abu na farko shine “dole ka zama akan waya 24/7, kwanaki 365a shekara.”
ZAINAB: Me? Ba hutu? Idan kana rashin lafiya fa!
MARIYA: Ana tsamani ka zo aiki ko b aka da lafiya. Sanan babu hutun zuwa haihuwa. Da alama dai a lokaci daya kake da damar hutu da ka aikin kulawa da ba’a biya, lokacin da kazo haihuwa da kuma dan lokacin da zakai na warkewa.
ZAINAB: Eh, amma ai haihuwa ba wai wasa bace. Wanan bukatun sun zama hauka. Amma dai ai kudin da za’a biya ka nasan da yawa, ko?
MARIYA: (DARIYA) Wana kudi? Lalle ma, ai salari dinki ziro duk wata, haka ma ziro duk shekara.
ZAINAB: (MAMAKI) Me?
MARIYA: Zaki iya nema kudin ki da ka gefe guda, amma dole ki daidaita shi da bukatun aikin kulawar ki. Sanan akwai kari ma. Dole ki iya wadanan abubuwan: iya girki, dinki, tara kudi, iya lissafi, da sanin ilimin kimiya, da iya siyo ka …
ZAINAB: (DAKATA) Wanan abun yayi yawa. Iya siyayya kuma? Wanan wane irin aiki ne? Ya sunan aikin nan ma tukunna?
MARIYA: Matar aure kenan kuma mai aikin kulawa da ba’a biya.
MAI GABATARWA: Aikin kulawa da ba’a biya na da matukar wahala yadda baka tunani. Mu ringa taimakawa masu aikin kulawa da ba’a biya, kana taimakawa kuna raba ayyuka dasu a gida, sanan ku samar da wata hanya taima-kekeniya a cikin gidajen ku, da unguwanni.
Talla #5: Boyayen abubuwa na aikin kulawa da ba’a biya
An yi kiyasi a Afrika maso yama, mata sun fi maza yin aikin kulawa da ba’a biya sau uku zuwa hudu. Wanan yana da tasiri sosai. Yana shafar lafiya jikinsu da kuma kwakwalwa su. Amma akwai wasu boyayeun abubuwan su ma.
Ya na dakile cigaban ilimin su da kuma tatalin arzikin su, da kuma sauran mu’amalar su da mutane a wurin taron suna ko biki, ko taron siyasa.
Saboda haka, ya kamata muyi adalci muna daidata aikin kulawa da ba’a biya dan mata su cimma burin rayuwar su suma kamar kowa.
Talla #6: Koyar da ayyukan kulawa wanda ba’a biya ga matasa masu tasowa.
Ka koya wa yaran ka cewa yin ayyukan kulawa wanda ba’a biya na da muhimanci wurin tafiyar da gida. Kuma hakin kowa ne, baba da yaro, maza da mata. Kayi kokari an raba ayyukan daidai tsakanin kowa da kowa ba mace ba namiji.
Aikace-aikacen gida shima wata kwarewa ce mai amfani ga kowa da kowa. Ba wani aiki da za’a ce na mata ne kawai ko na maza ne kawai. Me ya sa maza basu yi girki ba? Ko kuma mata suna wanke mota?
Ka kara koya wa yaranka tun yanzu dan su ci ribar rayuwa mai albarka a nan gaba.
Talla #7:Talafawa ma’aikatan kulawa da ba’a biya hakkin alumma ne gaba daya
Ba wai kawai mu kawo chanji a cikin gidajen mu bane muce ya isa, aah. Dole mu hada kai mu gina alumma da suke girmama ayyukan kulawa da ba’a biya da kuma su kansu masu yin aikin.
Daya da ka cikin hanyoyin da zamu bi domin cimma wnana shine taimakawa kungiyoyi da siyasa masu muradin tallafawa kare yanci ma’aikata kulawa da ba’a biya.
Don haka ku zabi masu san cigaban gidajen ku!
Talla #8: Ka taimakawa abokiyar zaman ka da ayyukan yau da kullum.
Talla #9: Ka ce a’a ga cin zarafi na jinsi akan ma’aikatan kulawa da ba a biya
Talla #10: Masu ma’aikata na iya taimakawa ma’aikatan kulawa da ba’a biya wajen daidaita aikin su da sauran al’amuran rayuwar su.
Talla #11: Samar da ingantatun hanyoyin samun kayan aiki na taimakawa ma’aikatan kulawa da ba’a biya
Talla #12: Yadda kafofin yada labarai da masu fada aji zasu iya cenza fahimta mutane game da ayyukan kulawa da ba’a biya.
Zamu iya cenja tunanin mutane cewa namiji zai iya zama mai bada kulawa kuma yayi nasara sosai akan haka.
Za kuma mu iya habbaka kukan ma’aikatan kulawa da ba’a biya sanan da sauraron abubuwan da ke damun su.
Ma’aikatan yada labarai, muyi amfani da dandalinmu wurin taikamko da inganta rayuwar ma’aikatan kulawa da ba’a biya.
Acknowledgements
Godiya:
Gudunmuwa: Ted Phido, marubuci mai zaman kansa, Lagos, Nigeria
Bita: Zahra Sheikh Ahmed, Manazarchi shirin, Women’s Economic Empowerment, UN Women East and Southern Africa Regional Office, Nairobi.
An samar da wanan ne ta shirin ‘UCARE – Unpaid Care in sub-Saharan Africa‘, wanda ke da kudirin habaka daidaiton jinsi da kuma karfafa mata ta hanayar jadada yin adalci da daidaito wurin raba ayyukan kulawa da ba’a biya da ayukan gida a tsaknin duk mazauna cikin gida a nahiyar kuda da hamadar Afrika. An aiwatar da aikin ne da ahdin gwiwar gidan Farm Radio International (FRI), UN ta Mata, da kuma cibiyar sadarwa da cigaban mata ta Afrika (FEMNET) godiay mai yawa da tallafin Global Affairs Canada.