Lura ga mai watasa shiri
Akwai damuwar gaske tsakanin kananan manoma game da komabayar darajar kasar noma a yankin hamadar Africa .Samun ragowar darajar kasar noma na aukuwa ne daga karfafa shuki, sabili da yawan kananan manoma na kokari akan kasar noma kasa da fadin aka daya.Haka kuma, sabili da amfani da takin gargajiya da ta zamani.Cigaba da mona akan kasa na cannye sinadiran ta, wadda ke kaiwa ga komabayan albarkatun kasa ya kuma lalata darajar kasar sai kaga an samu ragowar albarkatun gona.
Yawan tsarin gona na hade shuki a cikin yankin hamadar Africa na riba kaya akan gona domin tsare darajar kasa.Da yawan sharan gona na kumshe da sinadirai da dama na yin taki.Ababan da ake taki dasu sun hada ne da shara , sharan abinci,sharan masana’antun tabo daga magudana, sharan gona da kuma shara daga gidaje.. Ga wasu sharan yana da muhimmanci ka raba ta rubawa da ta magani irin glashi, roba da karafuna.Domin bangaren ruba shara na da sassabawa, ba zai taimaki shuki sosai ba idan aka sa shi kai tsaye ba tare da an ribannya shi ba.Rubawa na sake shara su zamo sinadirai da ababan amfani ga tsiro a cikin sauki.
Ruba taki nada amfanin tatalin arziki ga manomi.Misali, yin sa baya da tsada, za’a iya yin sa da kayan gida, yana habaka sinadiran kasa, nada kawannya ga mahali, baya bukatan hazaka ko fasaha da yawa, baya da tsadar saya, kuma yana bunkasa abinci.Har wa yau,,kamar yanda yake acikin rubutun nan.Yin takin gargajiya sabili da sayarwa na iya samar da kudi ga kananan manoma, samma ma idan suna aiki a hade.
Wanan rubutun ta dogara ne akan ainihin wata fira. Zaka iya amfani da ita wurin gudanar da bincike da rubuta wata irin zancen acikin unguwar ka.Ko kana da zabi kayi amfani da ita a tashar ka, kana mai amfani da muryoyin ‘yan wasan kwaikwayo su wakilci masu Magana.Idan haka ne, ka tabattar ka sanar da masu saularen ka tun da farkon shirin cewa, muryoyin na ‘yan wasan kwaikwayo ne ba ainihin mutanen da akayi fira dasu
Rubutunsa
Mai watsa shiri:
Da fatar ku wayi gari lafiya, masu saulare na. Shirin yau zata a kai tsaye dubi kananan manoma. Zance ne akan cin moriyan tatalin arziki na amfani da yin takin garajiya.Shirin mu ta dogara ne akan shawarwari da kwarewar wani manomin kasar Kenya dake tare da wata kungiyan taimako da ake kira Appropriate Rural Development Agriculture Program or ARDAP. Ita ARDAP din nan wata kungiya ce dake yammancin Kenya dake kira ga kiyaye abinci da ababa n amfani da yawa. Yau, zaku ji a bayyane fira tsakanin wani manomi mai suna Romano Afwande da malamin gona mai suna Boniface Omondi. Manomin zai yi bayani aiki da takin gargajiya a aikace, a yayin dashi malamin gona zai bamu wasu bayani zancen a fasahance. Ku bari mu saulara.
Bulo da taken wakan, sai ka shude ta
Romano Afwande:
Barka da safiya( rana, yamma) Nine Romano Afwande, dan karamn manomi dake aikin takin gargajiya a yammancin Kenya.
Boniface Omondi :
Ni kuma nine Boniface Omondi ,malamin gona daga wani kungiya da ake kira ARDAP . Muna gudanar da aikin takin gargajiya tare da wasau kananan monaman yammancin Kenya.Mu biyun, muna nan ne muyi zance daku a yau game da amfanin takin gargajiya, sammam ma akan sarafawa da sayar da shi.
Romano Afwande:
A nawa fahimtan, rubba shara wani taki ne da ake yi akan gona kuma wanda ke da karancin gurbatancen kamikal (magani)
Boniface Omondi:
Gaskiya ne. Akwai takin gargajiya nau’i nau’i. Akwai na rubbawa, kuma akwai wasu irin takin gargajiya, da suka hada da na ruwa da tea manure a turance,rashin noma fili na wani lokaci da green manure
Romano Afwande:
Kuma akwai hanyoyi da dama nayin takin rubbawa. Zaka iya yi ta dabkawa ko tattarawa , ko zaka iya rubbawa acikin Kwando ko cikin bokati., zaka iya kara wasu sinadiran tsiro ayayin da kake cikin rubawan ba mai magani ba.Wannan na sa taki a karshe tayi karfi.Idan mutane suka mini tambaya game da amfanin takin gargajiya, sai in basu labarin sakiya da na sammu a gona ta. Wancan shekara na halarci gun aikin takin gargajiya.Bangaren gona ta da nayi amfani da takin gargajiya ya habaka da tsari da daraja.Wannan na nufi yashin zai iya rika ruwa na tsawon lokaci.Yana kuma nufi jijiyoyin na tsaga kasa suje nesa cikin kasa.Wannan na kara yawan albarkatun gona da kuma samun karfi. Shuki dake da jijiyo kasa sosai na iya tsayuwa lokacin rani
Boniface Omondi:
Kungiyan ARDAP nada wani shiri na saduwa da jama’a a can yammancin Kenya.A cikin shirin mu,manoma na hada kansu suyi takin gargajiya da yawa,kuma suna amfani da kayan shara ne kuma ta tsarin rubbawa akan gonaki. Sarrafa taki domin sayarwa zai iya kawo kudi.Manomi zai iya kara yawan sarrafawa, sai ya sayar da wanda baya bukata akan gonar sa ga wasu gonaki. A unguwan mu akaai wasu dangin manoma 10 da suka hadu suka kafa kungiyan yi da sayar da taki. Suna sarrafa taki tan dubu 80 a kowace shekara. Suna sayar da tan 50 suyi amfani da tan 30 akan gonakin su,.
Romano Afwande:
Sarrafa takin gargajiya, aiki ce mai kyawon gaske ga matasa. Akwai hidima a cikin kwarai, ma’ana yana bukatan namijin aiki a iya yin takin. Ga matasan kananan manoma, wani madadi ne mai kyau na samun aikin yi.
Boniface Omondi:
Ka samu riba da yawa , wasu manoman dake takin gargajiya na kuma shuka tsiro masu darajan gaske, albarkatun gona masu gajeran zamani, kamar su timatir, tankwa da kayan gannyaye.Waddan nan shukin na bukatan sinadiran masu daraja. Suna samun amfanin sosai wurin amfani da takin gargajiya akan gonakin su
Romano Afwande:
Zaka iya kara wa takin ka karfi, ta kara kayan da b a ‘a yi amfani da su ba, masu kumse da sinadirai kamar irin su farin kasa daga tudun dutse, da wasu kwayoyin halita da idanuwa basa ganin su da sharan iskar gas.
Boniface Omondi:
Ko da yake kasuwar takin gargajiyan ba’a bata kafu kamar yanda takin zamani ta kafu ba , masu takin garajiya na iyakan kokarin su. A nan yammancin Kenya, manoman dake sarrafa takin gargajiya na sayar da su ga gungun masu saya. Waddan nan masu sayan sun hada ne da masu shuka gannyaye, masu reno bishiyoyi, masu maganin gargajiya da masu shuka kayan lambu.Da yawan masu sayan , masu reno da sayar da iri ne.
Mai watsa shiri:
In son na gode wa bakin mu biyun nan na yau da suka kara mu ssosai. Naji dadin kasancewa dasu nan dakin wtsa shirye shirye. Muna fatan masu saularen mu sunyi karatu game da amfanin da kanana masu sarrafa taki zasu samu.Da wannan muka zo karshen shirin mu. Godiya ga bakin mu biyu.Muna maraba daku nan dakin watsa shirye shirye ko ba yaushe
.
Romano Afwande da Boniface Omondi (Gaba dayan ku) Na gode
Mai watsa shiri:
Ayini lafiya
Waken taken na kawo karshen shiri, sai ka kamala
Acknowledgements
Gudunmowa: Macdonald Wesonga and Justus Makhulo for ARDAP Kenya, East Africa.
Nazari: Anthony Anyia, Research Plant Physiologist, Alberta Research Council, Canada.
Information sources
Canon E.N. Savala, Musa N. Omare and Paul L. Woomer, editors, 2003. Organic Resource Management in Kenya: Perspectives and Guidelines. Forum for Organic Resource Management and Agricultural Technologies (FORMAT), P.O. Box 79, Village Market 00621, Nairobi, Kenya, East Africa, Tel. +254-20-6752866
Email: format@wananchi.com, website: www.formatkenya.org. Ana samu a http://www.formatkenya.org/ormbook/Chapters/TOC.htm