Kwamitin ruwa na gida na taimaka wa yan kyauye, samma ma mata da yara

Lura ga mai watasa shiri

Ruwa nada mihimanci kuma rayuwar mutun na mutukar bukata, kuma ana daukar ta a “rayuwa” Babu shaka, samu da kiyaye ruwa wasu muhimman ababa ne ga rayuwa mai kyau. Samun ruwa nada amfani, samma ma wannan lokaci da muke fuskantan sauyin yanayi.A wurare da dama,samma ma unguwannin karkara, kadan da ake samu ma basa da kyau.kuma yana da nesa da matsugunnin kyauye.Yara su su kafi shan wahala cikin wannan halin.Rashin samun ruwa mai kyau, tare da harakokin rashin tsabta, na hadasa cututtuka harma da mace mace tsakanin yara,sabili da cutar zawayi da wasu cututtuka da suka dangaci hakan.

Mata, da kasa kasa ma yara, ke da halakin dibo ruwa domin amfanin gida, safarar da ita zuwa gida, adanar ta har zuwa amfani da ita, amfani da ita wurin dahuwa, wanka, wanki da shayar da dabobi. Idan aka samu karancin ruwa, mata da yara ke wahala, suna daukar awa shida a rana suna tafiyar nemar ruwa, zai iya ya dace ruwan ma baya da kyau.Yana da muhimmanci masu watsa shiri su gano waddannan matsalolin suyi zance akan ruwa da tsabta.

Wannan rubutun daga kasar Tanzania ne yana nuna yunkurin manoma a hade inda karancin ruwa ya zamo matasala tun a cikin shekara ta 1960.Ba idon ruwa a kyauyen; Mata da yara (samma ma ‘yan mata) na tifiyar kilomita tara su dibo ruwa. Ruwan da aka tattara baya da kyau, domin gun wuri ne karamin kuma kasa kasa nan ruwan ta tattaaru ta zamo tafki.Tun da ana kuma shayar da dabobi daga tafkin, dabbobo na tattaka cikin ruwa su kazan ta ta.Cututtukan ruwa nada sauki anan kyauyen.

Bayan da suka sha wahala shekaru suna jiran gwamnatin ta samar da kyauyen ruwa, ‘yan kyauyen suka dau shawara yin aiki a hade su magance matasalar ruwan.Sun gina wata karamar tafki suka tattara ruwa. Dake gangarawa lokacin damana.Suna iya amfani da ruwan watannin uku bayan damana ta kare.Kuma hukumar kyauyen na kraban kudi daga kowani gida su biya kudin gina rijiyoyi mara zurfi sabili da su samar da kyauyen ruwa mai kyau.

Za’a iya rungumar rubutun nan ga kowani kyauye dake fama da matsalar ruwa da tsabata, kuma da inda unguwan ko kyauyen bai samu wani taimakon gwamaati ba ko daga wani kungiya mai zaman kanta ba,kuma sun dogara ne akan yunkurin su ala tilar.

Wannan rubutun ya dogara ne akan ainihin fira, da akayi da shugaban kyauyen Tanzania.Indan kana son kayi amfani da shi a tashar ka, kana da zabi kayi amfani da murya ‘dan wasan kwaikwayo ya wakilci shugaban kyauyen, kuma ka sake zanttukan rubutu ya dace da yanayin unguwan ka Idan haka ne,ka tabbatar ka sanar tun da farkon shirin cewa,muryoyin na ‘yan wasan kwaikwayo ne, ba ainihin mutane da akayi fira da su ba, sai dai an ari shirin ne ga masu saularen ka na gida, amma ya dogara ne akan ainihin fira.

Rubutunsa

Taken waka ta shigo,sai ta shude sannu sannu

Mai atsa shiri:Ya kai mai saulare, barka da saduwa da kai akan shirin mu na yau. Sanannan ne cewa ruwa daya ne a cikin magance matsalolin mu.

Kade kade ta shigo,sai ta shude sannu sannu

Mai atsa shiri:
Barka da zuwa dakin watasa shirye-shiyen mu, Mr. Francis.

Francis:
Na gode.

Mai watsa shiri:
Mr. Francis, ko zaka iya yi wa masu saularen mu bayani sh’anin ruwan kyauyen Talawanda?

Francis:
Ruwa ta shafi kowannen mu, domin ruwa itace rayuwa.Yara, maza mata da dabbobi-mu duka ta shafe mu ta wata hannya ko wata.Zan iya bayar da wasu misalai.Yara da basa wanka na wasu kwanaka, zasu iya samun matsalar fatan jiki, dangi na samun abincin su a makare sabili da iyaye na bata lokaci da yawa wurin dibo ruwa.Mata sun fi shan wahala, sabili da suke dauke da alakin aikin gida.

Mai watsa shiri:
Mai yasa kace mata sun fi shan wahala?

Francis:
Mata ne waddan da ke tafiya kimanin kilomita tara su dibo ruwa da matari mai daukar lita 40 na ruwa.Lokacin da matan ke dauka wurin dibo ruwan ke hana musu loakcin kulawa da Iyalin su da wasu ababan.

Mai atsa shiri:
Francis, ta yaya matslar ruwa ke shafar manoma?

Francis:
Karancin ruwa na hana shayar da shuki lokacin rani, ko idan an samu tsawon lokacin rani. Albarkatu irin su, timatir da koren tankwa na samar da firasin mai kyau lokacin rani, amma bama iya shuka su, sabili da a aikace bama samun ruwan shayarwa.Dabbobi irin su, shanu,awaki, tumaki basa samun ruwan da suke bukata.Maimakon hakan, ana basu ruwa so biyu a ne sati kadai.

Mai watsa shiri:
Wani matakan magancewa ko madadi kyauyen ke da su?

Francis:
Kyauyen na tsakanin gangaren tudai, kuma akwai tafkuna biyu a kasan da ke cikowa da ruwan lokacin damana.suna kusa da unguwan jama’a.Bana da tabbacin girman sa ,domin bamu auna su ba.Amma zan iya kiyasta daya da fadin mita 200 kuma zurfin sa mita 5 zuwa 10.Muna amfani da ruwan da muke tattarawa cikin tafkuna idan damana ta yanke a cikin watan Mayu har zuwa karshen rani a cikin watan Agusto. Bayan hakan,’yan kyauyen sai su nemi ruwa wasu gun

Mai watsa shiri:
Ta yaya ake dibar ruwa daga tafkunan?

Francis:
Da bokati

Mai watsa shiri:
Ko ana yarda dabbobi su sha daga dukanin tafkunan?

Francis:
I, yana kuma gurabata ruwan.

Mai atsa shiri:
Wani abu kuka yi a matsayin ku na kwamitin ruwa ku shayo kan matsalar ruwan kyauyen ku?

Francis:
Kwamitin ruwa na aikin harhada duk harakokin ruwan kyauyen,Da farko,muna hada kan ‘yan kyauyen a haka karamin rijiya,mai zurfin mita 20 da fadin mita 5.Bama iya yin da yawa sabili da rashin kayan aiki.Abin madalla shine, rijiyan na samar da ruwa, ko da yake bata da yawa.Amma rijyan bata bushewa har damana ta soma.

Mai watsa shiri:
A ina rijiyan take? Kowa zai iya amfani da rowan kuwa?

Francis:
Rijiyan na kusa da makarantar firamiren kyauyen ne, kuma kowa ke bukatan ruwan zai iya amfani da rijiyan.

Mai watsa shiri:
Ta yaya ‘yan kyauyen ke dibo ruwa daga rijiyan?

Francis:
Ruwan rijiyan na aiihin amfanin gida ne, Mata na amfani da kananan kwano ko bokati da zai dauki ruwa lita 5, kuma ana daurewa da igiya mai karfi.

Mai watsa shiri:
An kange rijiyan ko an masa rufi ta wani hannya?

Francis:
A’a kullun akwai tsoron cewa ruwan zai yi dauda, ko yara zasu fada ciki

Mai watsa shiri:
Ko kwamitin ruwan nada shirin bunkasa lamarin?

Francis:
I, mun dau shawarar kara hakar rijiyan sai mu rufe da murfin kankare saboda mu samu ruwa da yawa kuma mai kyau, ko da lakocin rani ne.Idan zai yiwu, zamu so mu samu na’urar jan ruwa.

Mai watsa shiri:
Wa nene zai dau nauyin waddan nan cigaba?

Francis:
Gwamnatin kasar mu na kira ga tainakon kai da kai ne domin cigaba.Akan hakan sai kwamitin ta nemi a cikin gidaje 640 da kowace gida ta bayar da gudunmuwar kudin shili Tanzania 10,000 (Lura ga Edita, dollan Amurka $8 ko Euro 6) sabili da mu karbi shilli miliyan shida (kimanin dollarAmurka $4800 ko Euro 3600). Da zaran mun samu kudin,zamu nemi hukumar gundumar ta bayar da gudunmur fasaha har ma da taimakon kudi.

Maiwatsa shiri:
Akwai rijiya daya tak da kyauyen ke dogara akai lokacin rani.Ko kuna da shirin samun da yawa?

Francis:
Mun fahimci cewa bamu da isashen ruwa.Muna tunanen gina rijiyoyi da dama a kewayen kyauyen.Muna son mu samu rijiya a cikin kowani dayan yankin kyauyen.Muna da shirin fadada rijiyan da muke da shi.

Mai watsa shiri:
Ta yaya kuke adanar kudin?

Francis:
Domin samar da tsakankancewa tsakanin al’uma, kamata yayi a kiyaye kudin sosai a kuma yi amfani da shi akan bukatu da aka tanada.Duk wadan da suka bayar da kudi ana basu risiti.Mun buda akantu a banki domin kiyaye kudaden

Mai watsa shiri:
Mai kuke yi bayan watannin uku , idan rijiyan ta bushe?

Francis:
Muna da kudin da yake mun samu daga gwamnati a cikin akantun banki.Zamu yi amfani dasu mu sayi fanfuna mu jawo ruwa daga tafkunan zuwa kananan tankuna kusa da kowani titin kyauyen.Hukumar da ke kula da sha’anin ruwa ce zata dasa fanfuna,kuma ruwa zata kwarara da karfi.Wannan aikin zai dau kimani wata biyar.Kamin hakan,zamu gina rijiyoyi da yawa.

Mai watsa shiri:
Mai yasa baza ku gina tafkunan suyi zurfin da zasu tara ruwa da yawa ba?

Francis:
Idan tafkunan suka yi zurfi da yawa, baya da kiyayewa, Mutane da dabbobi zasu iya fadawa a ciki.Idan tayi zurfi da yawa, ba zai yi sauki ga mutun ya kare kansa ko kare kanta ba. Don haka muna tsoron mace mace.

Mai watsa shiri:
Wasu kayan aiki kuke amfani da su wurin ginan rijiyan?

Francis:
Muna amfani da bulon siminti wurin ginan rijiya. Ana yin su ne da yashi da siminti.Idan muka yi amfani da waddannan kayan, ruwa na saura cikin rijiyan tsawon lokaci.

Mai watsa shiri:
Ta yaya zaku biya bashin ginan rijiyan?

Francis:
Muna shirya taron kyauye muyi musu bayanin shirin mu, irin amfanin shi, da yanda kyauyen zasu taimaka.Muna fatan zasu yi shiri sabili da ra’ayin gina rijiyoyin daga gare su ne.

Mai watsa shiri:
Yaushe kuke sa ran ganin soma gudanar da shirin?

Francis:
Lokacin girbi, da yake mun san ‘yan kyauye zasu samu kudi wannan lokacin. Zai dace da watan Juni zuwa watan Oktobar sabuwar shekara. Za’a iya kamala aikin a cikin watannin biyar.

Kade kade ta shigo,sai ta shude sannu sannu

Mai watsa shiri:
Ya kai mai saulare,Da fatan ka saulari Costa Francis magakujeran kwamitin ruwan kyauyen Talawanda da basira, kuma da fatan ka koyi wata hannyar samar da ruwa a wurare da ake da karancin ruwa.Don Allah kada ka kaurace wa shiri mu na gaba.

Buga taken, sai ka shude shi a sannu

Acknowledgements

Gudumuwa: Emmanuel and Lillian Manyuka, Radio Maria, Tanzania, a Farm Radio International radio partner.
Nazari: Alan Etherington, independent consultant in water, sanitation and hygiene promotion, and ex-WaterAid staff.

Information sources

Fira da shugabannin kwamitin ruwan kyauyes

Godiya ta usamman ga Harbinger Foundation for supporting this script package on water and sanitation