Lura ga mai watasa shiri
A lokacin girbi, muna ganin manoma da dayawa suna shannya hatsi su akan fili ko baki hannya.Amma shannya shi a kasa zai iya sa ya jike ya kuma lalace da wuri.Wannan rubutun na nuna yanda zaka yi shannyi ba a kasa ba.Manoma matan kasar Bangladesh.sun yi amfani da wannan tsarin kuma sun yi.
Rubutunsa
Wakan take da na gano tashanDa farko, ku shakata da wannan faifai na (sunar mawaki)
Dakatar da wakaIna tsamani da gaskiya na idan nace mafi yawancin manomar dake salaren wannan shiri na shannya abinda suka girbe waje a fili ko gefen hannya.Amma idan damana ta soma ya kamata mutun ya kwashe komai domin tsoron zasu jike, ko ba haka bane? Bugu da kari, kana aiki duk rana kana shannya hatsin ka kanamai kare su daga yara da kaji kada su shiga ciki.
Amma babban matsala itace shannya hatsin ka a kasa zai sa su lalace da wuri bayan ka baje.haka ne sabili da hatsin na jan danshi daga kasa.Bugu da kari,yashi, itacuwa da dauda na hadewa da hatsin, sai ya rage masa daraja. Zai yu kuma nau’i anau’i zasu hautsune gaba daya.Amma, menene musannyar shannyi a kasa?Menene zabin ka?
Ku sake shakatawa da wake, zan dawo muku da jawabin tambayoyin nan.
Dakatar da wakaDaya acikin wadan nan hannyoyin ya zo mana ne daga kasar Bangladesh ,Matan Bangladesh na amfani da tabarmi, tarpauli mafi kyau ma, akan teburi wurin shannya hatsin su.Iska na samun kadawa a cikin sauki akan teburin, abin nufi hatsin na bushewa da wuri, Shannyi akan teburi, matan nan na tabbartar da hatsin basa dauda.Da zara ruwan sama ta soma sauka sai su dauke teburin suyi cikin gida da su sabili da kada su jike. .
Matan nan ada can sun fuskanci matsaloli sosai wurin shannya hatsin su lokacin damana.Amma tun da suka koyi cewa hasti zai iya bushewa a inuwa,kuma iska ke taimakawa bushewa,basu sake fuskantan waddan nan matsalolin ba.
Wannan wani abin da zaku iya gwaji ne- amfani da teburi wurin shannyi hatsin ku.Baza ka kashe kudi da yawa kayi ba.Duk abinda kake bukata sune wasu kusoshi da wasu katako ko icen gora.Wannan baya da wani tsada-komai zasu iya fitowa gonar ka, sai dai watakila, kusoshi.Idan kayi teburin da icen gora yafi, sabili da baya da nauyin dauka.Idan ruwan sama na barazana, yana da sauki daukewa
Teburin na wasu amfanu, Zaka kuma iya amfani das hi ka busar da kifi, alkama, saffron, tamkwa da wasu ababa.Idan yana kwari sosai kuma baya da tsayi kwarai,za’a iyaamfani a gadon barci, ko kuma gun adana.
Shude wakan karkashin murya mai wasta labaraiYa kai manomin shinkafa, idan kana bukatan faifan vidiyon shirin tsabtace hatsi, shannyi da kiyayewa, zaka iya saduwa da (mai watsa shiri ya bayar da sunar mutumin gida dake raba faifan vidiyon shinkafan)
Acknowledgements
Gudnmowa: Felix S. Houinsou, Rural Radio Consultant/Africa Rice Center (WARDA)
Nazari: Paul Van Mele, Program Leader, Learning & Innovation Systems/Africa Rice Center (WARDA)
Information sources
Masu watsa labarai zasu iya zuwa: http://www.warda.org/warda/guide-video.asp su ga dandalin jerin faifan shinkafa. Ko kuma su ga jerin da suke hade da rubutun nan.
Godiya zuwa ga:
International Fund for Agricultural Development (IFAD) da taimaka wa nazari akan manoman shinkafa mata ,da kuma fasarta faifan vidiyon a cikin harshen gidan.
Bill & Melinda Gates Foundation da IFAD na taimaka wa hada rubuun nan.