Tallaluka akan rigakafin cutar Korona

Kiwon lafiya

Lura ga mai watasa shiri

Abun lura ga masu gabatarwa

Samun gaskiyar alamurar game da cutar Korona na da matukar muhimanci fiye da komai.

Ku tura wadanan sakonin a yayin da kuke gabatar da shirye-shiryenku da wasu lokutan domin kara yawan masu sauraron da suke jin su. Haka kuma, ka yada wanan sakon a shafukan sada zumunta gidan rediyonka. Idan aka hada da hton zane, wanan sakon zai iya samun sababin masu sauraro ko kara karfafa abun da tsofin masu sauraron ka suka saba ji. Zasu kuma taimaka wurin wayar da kan jama’a kan wasu karairayin da jite-jite game da cutar dake yaduwa shafukan sada zumunta.

Ga wasu misalan talaluka a shafukan sada zumunta da sukai jawabai kan karairayin da labaran bogi akan cutar Korona:

  • Africa Check yanargizo
  • Africa Check akan Facebook
  • Africa Check Nigeria akan Facebook

Har cikin watan Disamba, zaka iya shiga group din WhatsApp na Afrika Check a cikin wanan kasa-she:

Rubutunsa

Talla 1:
Kananan Illolin riga-kafi

 

MAI GABATARWA:
Yar karamar illa bayan allura riga-kafin KORONA abu ne sanane.

Kamar ko wace irin riga-kafi, riga-kafin KORONA na iya samar da karamar illa ta wucen gadi kamar ciwo a wurin da akai allura, zazzabi da kuma gajiya. Wanan alama ce, cewa rigak-kafin na aiki.

Kaje ayi maka riga-kafi! Domin ka kare kanka da alummar ka.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta sanan ka hada da link din wanan bidiyon: https://www.facebook.com/584311918440395/videos/260977218910193


 

Talla na 2:
Nau’in omicron

 

MAI GABATARWA:
KORONA ta cigaba da yaduwa, sanan nau’in omicron shine sabon babban nau’in a cikin jerin biros din.

Masanan kimiya na cigaba da nazari akan nau’in omicron domin su gano ko yafi yaduwa da kuma tsanani a cikin jerin nau’oin cutar KORONA.

Domin kare kanka da alumma, kaje kayi riga-kafi, ka sanya takunkumin rufe fuska, kana bada tazara tsakaninka da mutane, kana wanke hannu, sanan kana tari a cikin gwiwar hannu in ya kama.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta sanan ka hada da link din wanan bidiyon: https://www.facebook.com/viralfacts/videos/487756619403361


 

Talla na 3:
Nau’oin KORONA

 

MAI GABATARWA:
KORONA na yaduwa a wuraren da mutane kalilan ne suka yi riga-kafi.

Yawan yaduwar KORONA, shi ke kawo yawan nau’in cutar kamar nau’in delta da omicron.

Don haka, kaje ka karbi riga-kafi domin kare kanka da alumma.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta sanan ka hada da link din wanan bidiyon: https://www.facebook.com/viralfacts/videos/3178204335840205


Talla na 4:
Menene guguwar cuta?

 

MAI GABATARWA:
Sabuwar guguwar cutar korona tazo.

Amma menene guguwar cutar?

Guguwar cutar KORONA wani gagarumin karin masu kamuwa da cutar KORONA ne.

Hukumar Lafiya ta Duniya tace sabuwar guguwar na samuwa ne game da wasu dalilai, misali, idan mutane suka kara kamuwa da cutar, ko kuma akwai sabuwar nau’in cutar, ko kuma idan mutane suka daina daukar matakan kariya.

Hanya mafi inganci domin kare kai akan nau’in da kuma kariya ga sabuwar guguwar cutar shine kaje ayi maka riga-kafi.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta sanan ka hada da link din wanan bidiyon: https://www.facebook.com/viralfacts/videos/3151128975124101


 

Talla na 5:
Matakan riga-kafi

 

MaI GABATARWA:
KORONA gaskiya ce kuma tana da hadari.

Ga hanyoyi shida da zaka iya kare kanka da iyalinka:

Kaje ayi maka riga-kafi!

Kana bada tazara tsakanin ka da mutane!

Kana saka takunkumin fuska!

Kana wanke hannu a kai-kai!

Ka tabatar da akwai ingantaciyar iska ta hanyar bude taga!

Kayi tari ko atishawa a gwiwar hanunka!

Mu hadu mu hana yaduwar guguwar cutar KORONA.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta sanan ka hada da link din wanan bidiyon: https://www.facebook.com/viralfacts/photos/a.152469173263846/519184793258947/


 

Talla na 6:
Mata masu juna biyu da kuma rigakafin cutar KORONA

 

MAI GABATARWA:
Juna biyu wani loakci ne mai abun sha’awa.

Amma kamuwa da cutar KORONA lokacin juna biyu na kara hadarin rashin lafiya da rikitarwa.

Labari mai dadi shine mata masu juna biyu na iya karbar rigakafin KORONA.

Saboda haka idan kina tsamani, kije ayi miki riga-kafi!

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta sanan ka hada da link din wanan bidiyon: https://www.facebook.com/viralfacts/videos/581588119581778


 

Talla na 7:
Samu tabatacen bayanai

MAI GABATARWA:
Jita-jita da rashin fahimta akan KORONA na ko ina, amma duk da haka, mutane miliyoyi ne suka karbi rigakafi ba tare da wata matsala ba.

Rigakafin KORONA baya kawo rashin haihuwa ga mata ko maza.

Kuna saurara tashar XXX domin samun ingantatun labarai game da KORONA —a gidan rediyon ko kuma a shafin su na yanar gizo.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta sanan ka hada da link din wanan bidiyon: https://www.facebook.com/viralfacts/videos/486795659773821


 

Talla na 8:
Tantance zance

 

MAI GABATARWA:
Akwai karairayi a shafukan yanar gizo da yawa.

Amma batun gaskiya shine, rigakafin KORONA BAYA sakawa mutane kwayar cutar biros kuma baya sakawa ka cutar da wasu.

Mutane miliyoyi sun karbi rigakafi kuma sun samu garkuwa akan cutar, hade da dukan nau’oin ta.

Dan haka, domin samun ingantacen labarai game da cutar KORONA, ka saurari gidan Rediyon XXX.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta sanan ka hada da link din wanan bidiyon: https://www.facebook.com/viralfacts/videos/586204605924854


 

Talla na 9:
Tarayya Garkuwa

 

MAI GABATARWA:
Idan kaso na mutane da yawa a unguwa ku suka yi rigakafin cutar KORONA, kuna zuwa wani matsayi da masana kimiya ke kira “tarayya garkuwa.”

Wanan yana nufin yiyuwar kamuwa da cutar KORONA kadan ce.

Don haka, kaje kayi rigakafi, ka kare kanka da alumma.

Duba karin bayani a shafin Facebook na gidan Rediyo XXX.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta sanan ka hada da link din wanan bidiyon: https://www.facebook.com/viralfacts/videos/161828956045309


 

Talla na 10:
Kula da rigakafi da kuma cutar COVID

 

MAI GABATARWA:
Rigakafin KORONA na da aminci kuma na da tasiri.

Suna da inganci sosai wurin kariya daka tsananin rashin lafiya ko matua ta dalilin KORONA.

Bayan anma rigakafi, zaka iya kamuwa da KORONA, amma yiyiwar kamuwa da cutar kadan ce. Sanan ko ka kamu da ita, alamomin cutar zasu zo ma da sauki.

Don haka, kaje kayi rigakafi, ka kare kanka da alumma.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta sanan ka hada da link din wanan bidiyon: https://www.facebook.com/viralfacts/videos/569616074462576


 

Talla na 11:
Rigakafi da gudan jinin

 

MAI GABATARWA:
Wasu mutane na cewa kada kayi rigakafi saboda yin rigakafin KORONA na kawo taruwan gudan jinni.

Amma, samun taruwan gudan jinni dalilin yin rigakafi ab ne da yiyuwar sa take kalilan.

Hasali ma, kafi yiyuwar samun taruwan gudan jini idan ka kamu da cutar KORONA.

Don haka, kaje kayi rigakafi, domin ka kare kanka da alumma.

Duba karin bayani a shafin Facebook na gidan Rediyo XXX.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta sanan ka hada da link din wanan bidiyon: https://www.facebook.com/viralfacts/videos/296820051781587


 

Talla na 12:
Shaidu

 

MAI GABATARWA:
Gloria Mosha daka kasar Tanzania na da shakku karbar rigakafi KORONA bayan jin jita-jita a yanar gizo kala-kala. vaccine after hearing many rumours online.

Amma, sai ta ga mutane da yawa na kusa da ita na karbar rigakafi kuma babu wata matsala da ta same su.

Taje an mata rigakafi.

Ka samo gaskia. Kaje ayi maka rigakafi.

Duba karin bayani a shafin Facebook na gidan Rediyo XXX.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta sanan ka hada da link din wanan bidiyon: https://www.facebook.com/viralfacts/videos/278704130474218


 

Talla na 13:
Hadin kai

 

MAI GABATARWA:
Hanya mafi kyau ta gudun kamuwa da cutar KORONA shine a kare kowa daka cutar.

Idan duka iyayen mu mata, da yayin mu, iyayen mu maza, suka karbi rigakafi sanan suka dau duk wasu matakan kare kai, zamu ci nasara akan KORONA gaba daya!

Don haka, kaje kayi rigakafi, ka kare kanka da alumma.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta.


Talla na 14:
Karin rigakafi ta uku

 

MAI GABATARWA:
Karin rigakafi ta uku nan a kara kariya a wurin wadanda suka karbi duka biyun rigakafin a baya.

Akwai su a wasu kasa she, amma ba ko ina.

Idan ka karbi duka rigakafin ka ta KORONA, ka tambaya ko akwai karin ta uku a inda kake.

Kaje kayi rigakafi, ka kare kanka da alumma.

Domin maida wanan tallan zuwa shafin sada zumunta, ka saka rubutun a shafinka ka na sada zumunta.


 

Acknowledgements

An ƙirƙiri wannan albarkatun a cikin aikin AMPLIFY, tare da haɗin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).